Sashe 85
Tantiriya A Gidan Yari Book 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
gidan Naila ku tsaya kuci kaji da yawa ko Kwa farfado,Goggo tace har a gaya mana cin nama mu,kafin kuci Naman fa? sai sati sati ranar juma'a cewar Abba. Ya dade suna Hira sannan ya tafi zai kwanta Yar Inna tace baka yi wankan ba,yau Banga dama ba bazan yi ba,ai kuwa na dafa ruwa sai kayi wanka,sabo da kina gadara baki da ciki,yanzu da cikine dake murna zaki fara kar nayi wanka,Yar Inna tace naji muje dai sai kayi wanka,Abba ya mike ya zaiyi haka ya shiga wanka ya fito wai yayi fushi an sashi dole yayi abinda baiyi niyya ba,Pillow ya dauka ya koma kasa ya kwanta,Yar Inna tace zan iya daukan ka na dawo dakai sama gwara ma ka dawo tun wuri,Abba yace da na zama banza kuwa kika iya dauka na to garin nan zan bari,fafur Abba yace bazai hau gadon ba kyankyamina akeyi sai an sani dole nayi wanka sabo da kar na lalata miki bedsheet,bazan ma hau Miki gadon ba. Washe gari su Goggo suka tafi gidan Naila,Spark yana gida abinsa suna kallo Naila tana jikinsa a kwance sai ga su Goggo sun kwada sallama,Spark yace to fa ga 'yan uwanki nan daga Jin Muryar kune,Naila tace kamar Goggo ku shugo bata da niyyar tashi a jikinsa,Goggo suka shugo"Tani tace da kyar muka gane gidan nan aradu har zamu kira waya,Spark yayi murmushi yace sannu da zuwa,Naila sai lokacin ta mike a gajiye tace sannunku ya hanya? Goggo tace Alhmdllh maji dadi ,har yanzu dai ana nan ana wannan nacin na makale makale,wai ku dan Allah bakwa Jin kunya ne? Spark dai rusunuwa yayi ya gaida su suka amsa,Naila ma haka ta mike ta shiga kitchen,Goggo tace Banga alamar ciki ba a Jikin Yar nan,Juyowa tayi ta Kalli Spark tace to Kai ya haka? Spark murmushi yayi ya daga yatsa sama ba tare da yace komai ba wai Allah ne,Tani tace kaji dashi kinibabbe ka samu yarinya son kowa kin Wanda ya rasa ai dole ka daina fita,Dan kauyen ma kaki zuwa,Spark yace a gidana fa ta koma haka ai kuwa na iya kiwo,Goggo tace wlh karya kake dama haka muka kawota kiba kadan ta Kara da haske,Spark yace Amma ta Kara ai ko Goggo ai an samu ci gaba,yarinyar nan irin kudin da take lashe min Allah ne ya sani,ku godewa Allah ta auri me shi da wani ne da yanzu ta fara yaji,ku godewa Allah ni ta aura,dariya su Goggo suka yi,ai Kai ba a kada Kai a magana kamar ba Dan Abuja ba. Arham ne yayi Sallama ya shugo yaga Goggo wacce ta doke shi,yace sannunku da zuwa,Goggo tace Kai me Ido a tsakar Kai daga Ina haka? Ina Baban naku da Mima din? Arham yace ai na dade da zama maraya ni,Goggo ta zaro ido,ya gaida su suka amsa yace Yaya Ina Aunty din? Spark yace Kai me zaka mata ka isheni na rantse da Allah,Goggo tace tana kitchen Kai,Arham ya nufi kitchen yace ni da nasan ma tana nan bazan tambayeka ba,Dan ka samu ma ana kulata,Murmushi Spark yayi yace gobe ma rana ce. Kitchen Arham ya shiga yace Aunty Naila ta juyo tace Arham ya aka yi ne? yace unguwa zanje Banda ko sisi ko ki bani ko kisa mayenki ya bani 10k kacal,Naila tace kana tunanin in nace ya baka zai baka? Ai kina kaishi bedroom wlh sai ya bani sai in Baki niyya ba,Dan 10k ma fari kawai ya isa kina Masa fari da Ido zai bayar, Dariya Naila ta dinga yi tace nidai na shiga uku kowa cikinku sai yace in sa baki,to power ce dake ai Aunty kune masu wuta a uhm....ba irin su Anam ba. Naila tace nidai bazan ce ya baka ba zan baka kawai,yace to ai duk daya ki hado da kudin Shan lemo. Ta gama shirya abinda zata kaiwa su Goggo a tire ta fito Arham ya biyota da wani plate din,tana ajiyewa su Goggo ta haura sama tace Arham zo,Spark Yana kallon su yaje ta dauka a nata ta bashi 12k tace gashi 12k ne ma,yace na gode Allah yasa Spark ya haukace ya baki Million goma,dariya Naila tayi tace in ya haukace Kuma ai na shiga uku,yace to wlh idan ya kuskura tace zai miki kishiya sai Inda karfi na ya kare,sai dai in baya so ya sake ki ki dawo wajena ko ya kika ce,Naila tace Allah baya sa ba Kai duk adduar taka babu ta kirki suka karasa Sakkowa daga Step,ficewa Arham yayi Yana ji da gayu. Goggo kuwa suna ta ciye ciyensu" suna hira da Spark Naila ta dawo ta zauna suna hira sannan Spark ya basu waje. Goggo tace ke Naila ciki dai har yanzu? Naila tayi murmushi tace sai nan gaba zai zo ne,ko dai sai an karbo miki magani? Naila tace Hallare ma kawai ta Isa tunda tana aikinta,Goggo tace nidai na shiga uku da wannan yarinya sai nayi zaton ta shiryu sai naji ta sake sabon iskanci,Dan Allah ku bakwa Jin kunyar magana ne a gaban mu,Naila tace wai Goggo ke fa kakata ce Kuma Kakana kike aure,Tani ma kamar kaka ce to me zanji kunya,abin nan Kun sani na sani ko bakwa lallabawa data tsofaffinku,Goggo harararta tayi tace ai sai kiyi Kuma,Tani tana jinsu tace Allah ya kawo masu Albarka. Mummy tun bayan da kunama ta cijeta sai data kwana tana Shan wahala kafin ta Fadi ta samu lafiya. Yau da yamma suna zaune sai ga Misam tare da Chika sun shugo sunci wanka cikin shadda iri daya wata ruwan kwai,irin kyan da suka yi ma fada bata baki ne,Mima taji dadi ganin Misam yazo din,murmushi tayi tace kune yau,Chika ta karasa tare da durkusawa ta gaida Mima ta amsa tace Kuna nan lafiya,lfy Alhmdllh cewar Chika,Mima sai murna take taji ance matar Misam tana da ciki,su Anam basu kulata ba sai Misam kawai suka gaisar,Mima tace ita baza ku gaisar da ita ba? Ba yanda suka iya haka suka gaida Chika ta amsa,Mummy tace Misam irin wannan kiba haka,dariya yayi yace ta iya girki ne shi yasa,duk da tana dan Shan wahalar cikin nan bata kasa min girki,Mummy tace wlh nasan sai yayi zancen cikin nan ai na fada,sai dai idan ba marasa kunyar yaran gidan nan bane,Kai dalla yi mana shuru in ya fito ma gani,Misam ya murmusa Yana Jin dadi,Mima tace kunje gaisuwar matar Rafeeq kuwa? Misam ya furta sai gobe Inshaallah,Allah ya kaimu cewar Mima ya kamata muje ai Nima Ina son zuwa,Sunyi mamaki matuka,Mima tana canjawa sosai. Rafeeq kuwa suna can da safe suzo wajen makoki da dare ya dauki matarsa su wuce hotel,ranar Sadakar Uku sai ga Spark,Arham,Shaheed,Misam,Mima da Mummy sunzo,Ikhram tayi mamaki,Kuma ba wulakanci ba komai gwara ma Mummy sai da ta Dan nuna hali Amma Mima ko digo ba abunda ta nuna musu,Naila tazo da Chika har Maman Rafeeq duk tare suka zo. Ikhram dangin Miji sun mata Kara sai nan nan ake da su,Arham dariya suke wa Rafeeq ganinsa harda zubawa mutane ruwa a buta za ayi Alwala sabo da shishigi su masu Uncle,Shaheed cikin rada yace Arham Kalli shishigi kamar ubansa ne ya mutu,da haka kawai ne cewa zaiyi bai ma San Sunan buta ba,Arham yace mudai duk mazan gidanmu bayin mata suke komawa wlh,ai a Jinin sojoji yake,sojoji da yawa haka suke bayin matansu ne daga su sai matansu ai shi yasa,nidai Allah ya tsareni da wannan masifar ta son mace haka,shi yasa ma bana so naji Ina son wata da yawa,Shaheed yace Nidai sunyi dai dai haka nake so na koma chewgum,Wata budurwa ce ta wuce Yar duniya kana ganinta kaga Yar bariki,wata Abaya ta saka amma komai yabi jiki ana ganin komai kuru kuru ko bra babu. Arham yana kasa da Murya yace sadaka Shaheed ana raba mana,Shaheed ya saci kallonta Shima yace na karbi tawa nima,Spark ne ya harare su yace ance ayi addua Kuna ta wani kuskus aikin banza,hannaye suka daga suma tare da furta Ameen,wata budurwar ce tazo ta sake wucewa suka daina adduar,Shaheed yace dadina da unguwar nan dole sai kayi nishadi muna wajen makoki amma sai nishadi muke yi,Arham harda kashe Ido daya yace wannan ta iya Sadaka,gaskiya kar su Ikhram su bar unguwar Nan ko banza in muka zo ma dinga nishadi,Spark ne ya ja tsaki suka yi shuru. Suna yin Sallar La'asar Spark suka shiga ciki wajen Iyalinsa ya basu takardun gidan da suka siya musu me kyau madaidaici a wata unguwar daban me tsafta sannan aka basu jarin dubu Dari biyu biyu ko wacce, Misam ya basu mota guda ta kayan abinci,su Asabe harda kukan farin ciki da murna,Manyan Dattijai suna ta musu nasiha akan su zauna lafiya su rike maraicinsu,Kuma gida ba nasu bane na yaran ne Wanda ubansu ya mutu a haka aka yi yarjejeniya da lauya,sannan kudin ma ba a hannunsu aka basu ba suna hannun hukuma sai an kaisu gidan sun tare sannan ma a basu jarin ko wacce ta Fadi abinda zata iya yi a siya mata ta fara. Ga mutane da dama suna ta kawo tallafi,sai yamma likis suka tattara har Ikhram suka tafi Abuja aka bar su Asabe da danginsu a Kano. Mima suna komawa gida mamaki ya kama su ganin motoci lafiyayyu a gidansu,tace to wanne Baki muka yi Kuma naga sojoji,suna shiga Palo suka samu Papa a zaune ya hakimce Yana kallo,Mima tsayawa tayi kamar gawa tana kallonsa,Arham dariya ya boye ya radawa Mima mun rufe idonmu kije ki rungume abinki,Mummy tace wai wai wata sabon Gani,Papa ya kalle su yayi murmushi kawai,Mummy ta janye su Arham tace kuzo muyi Nan,Arham yace kar ayi abin kunya ba,Zaka ci ubanka wlh marar kunya muje. Mima karasawa tayi gaban Papa ta zube gwiwoyinta a kasa tare da rike Masa kafafu tace Dan Allah kayi hakuri indai a kan Halayena nane na tuba na daina,gashi ma yanzu ta'aziyya muka je ta matar Rafeeq inshaallah zan gyara Dan Allah kayi hakuri. Papa murmushi yayi yace ai na San kin gyara shi yasa ma kika ga na dawo,tashi komai ya wuce yanzu,tashi Mima tayi Shima ya mike tsaye tare da rungumeta ya furta I miss you,Miss you more tace dariya suka yi. Mima tace yau dai Allah ya taimakeka kazo a sa'a tuwo muka yi