Sashe 46
Tantiriya A Gidan Yari Book 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ya furta to ta matsa min Abba sai tazo gida ta dade bata zo ba har kusan 4months,Abba Yana ji yace a zamanin mu ai sai ta Shekara guda a dakin miji,Yar Inna ma sai da tayi Shekara guda da wata biyu bayan guje guje da ta sha fama a dakin miji dama kafar ta karye a lokacin an huta,Spark suka dinga dariya,Abba yace Allah in ba lalacewa ba ta Fulani a kawo Amarya Kuma kullum ta gudu sai ta kwashe watanni,Abba yace na huta siyo lemo munyi arziki Mohsin yanzu zuba mana yake a freezer Naila ebo muku harda maltina,kafin kuwa Naila ta tare da kazo na kashe kudi wajen siya Maka lemo,Kuma ka shanye ko ragewa ku dai dama Baku hada jini da Fulani ba,hasken ku ma bana Fulani bane shi yasa ba Kara babu kunya,tun lemon da Abba ya siyawa Spark yake ta faman zancensa. Naila tashi tayi ta ebo musu lemo,Abba yace dai daya kowa daya,Naila tace Abba mune fa lemo, naku ma me araha ne yanzu mineral sai manage,yace me yasa Baku taho da abinku ba,Mohsin ya kira a waya Yana dagawa yace kanwarka tazo Naila Bata kawo mana komai ba ko gishiri,Spark yayi dariya kamar me,yace Abba mun kawo suna mota yanzu zaka ga driver ya bawa Almajirai sun shugo da su,waya yayiwa driver ba a dade ba Almajirai suka dinga shugo da kayan arziki,Abba ya tashi yace yace yanzu zan koma rumfa ta. Naila tace Ina yini Umma,Kubra ta amsa tana furta Naila anyi hankali,Spark ya gaisheta sai ga Mohsin da Beauty sun shugo,Naila da gudu zata mike ta rungume Mohsin Spark ya rike mata kafa yasan hali,Umma tace Ina zaki je ne haka Mohsin din gashi ya shugo bana son shiririta ke bakya girma ne,Naila sai ta Kalli Spark ta harare shi ta zauna,tayi shuru taki magana,Mohsin yace sis ba magana Kuma? ance kar na kula ka na daina Maka magana gaba daya" ya zanyi, murmushi suka yi,Beauty ce tazo ta fada Jikin Naila da gudu ta,a zabure Beauty ta mike ta fice sai amai a gindin pampo,Mohsin yace turare taji a jikinki Naila bata son turare,tashi yayi yabi bayanta,Umma bata ce kala ba tace bari naje kitchen ta fice ta shiga kitchen. Beauty sai da ta gama amanta Mohsin yace Kinga duk abincin ya zube dama da ya aka ci,bakinta ta wanke ya wanke wajen tas suka koma ciki ta zauna can nesa,Hira suke sosai har Umma ta kawo abinci,Spark ya dan ci kadan yace tafiya zaiyi Yana da meeting,amma a jirgi zaka Koma? Umma ta tambaya yace ae Inshaallah,100k ya ajiyewa Umma ya yiwa transfer na 200k yace na Abba ne sannan yayi musu sallama Naila mikewa tayi ta tafi rakashi,a kofar gida suka tsaya yace 2days na baki,Naila kamar tayi kuka Dan Allah ka Kara min kwana ko daya ne ya zama uku,murmushi ya sakar mata yace shike nan 3days na cika kin gama,tace na gode tana murna ya tafi ya koma ciki,tana mamakin kokarin Spark yau. Tana dawowa ta zauna a gefen Mohsin tace to Yaya,kallonta yayi yana dariya yace aure me gyara mutum,Nan muka damu akan a dinga aiki ana gyara gashi kika ji a banza kin canja,Naila tace Yaya na Isa ni yanzu girkin da na koya ma ko matarka Albarka,Beauty tace akwai labari fa Naila ki gama dai,Mohsin yace ni wajen aiki ma zan koma,zan dawo da yamma yaci abincin a gurguje ya Kalli Beauty yace madam na wuce ni,Naila ya mikawa Hannu suka tafa yace na tafi,tace Allah ya tsare sai ka dawo. Yana tafiya Beauty ta turawa Naila abincin tace kici ni bazan ci ba bana son shi,Naila tace me zaki ci to? Taliya da Mai da yaji nake so manja Kuma,Naila tace ai sai na dafa miki ta mike ta shiga kitchen,Umma tace me zaki yi ne? Beauty zan dafawa taliya da manja da yaji,dariya Kubra tayi tace ikon Allah wai Naila kece kike haka babu kyuya, da fa tsinke baza ki dauka ba,wanki sai dai ayi miki in ana so a ganki fes,Naila tace tun yaushe yarki tayi hankali Kuma Yar Inna,Umma tace zanci ubanki sa'arki ce ni,Dan kiji Abbanku na fada ba sunan kowa bane,Naila tace Yar Innan? tana dariya sannan tace Abba yace baki da lafiya? Uhm dan ciwon Kai fa kawai nayi shine yace bazan yi aiki ba shi yayi komai ma da kike Gani girki kawai na karasa,Naila tace soyayya tana dariya,Ya ranki kiyi fata Spark din naki ya Kai kamar shekarun Abba Yana miki so haka,Naila tace zai yi ma Umma,sai kin dage kuwa kina sauke hakkokin da Allah ya gindaya miki,da Kuma siyasar zaman aure sai kin koyeta dole,komai ace baki da matsala ko aure ya Kara zaki zama on top amma mu mata wasu suna Kara girma suna sake zama boss a gidan miji suna bude rashin mutunci da rashin kunya,maimakon ana girma ana hankali mata da yawa su haukacewa suke,a haka muke zubar da mutuncinmu a gaban Mazaje,miji zai iya zagin mace ta uwa ta uba sabo da ta wulakanta kanta,karki sake kice Kun zama daya ai mene be sani ba a jikinki, ki dinga kin yin tsafta da kwalliya ko ya kika ga dama ki zauna a gida sabo da kawai ya sanki yasan komai Maza yawanci da abinda suke gani da shi suke amfani. Bana so ace kayan unguwa daban na gida daban,a gida a zauna da kodaddun kaya wulakantattu ko a sa skirt din atamfa da tshirts kullum a gida,ko a daura zani da Tshirt kullum a gida, miji bazai ga kwalliya ba sai za a fita,Maza suna son tsafta da kwalliya,suna son kulawa Kuma,kar kice ko kinyi 'ya'ya zasu dauke miki hankali kullum kina wajen yara Baki da lokacinsa,ai dai Kinga Ina kamantawa ni,na sanki da rashin karfin tsiya... Abba ne ya shugo ya leka kitchen yace Kubra an San 'ya a gaba ana koya mata Dan hali,Naila idan baki gaji Kubra ba ke Kam kin rako mata duniya,dariya suka yi Abba yace Allah kuwa nasan ma kin gajeta ko? Naila tace ae na gaje ta,Beauty ya hango yace suruka ma ta gaji surukarta,Beauty tace Abba na gajeta,yace shike nan danmu Kuma an shanye shi Ina Tausayin Mohsin,shi da Kara aure Kuma shike nan,shi yasa bana so ki dinga zuwa gidan Nan akai akai kar ki dinga course wajen Yar Inna an gama da uban Dan ma ace babu,Dariya Beauty ta dinga yi,tace Abba waye a rumfar ne yanzu ka taso da rana? Yace na gaji rana ta kwallare bazan iya ba na hada tarkacen kayan Miya na sasu a store, na fasa siyarwa kwanciya na dawo gida nayi tunda nayi sallah me zanyi anjima abokina Jauro zaizo,Beauty tace kafin Naila ta koma kuwa zamuje gidan Kawu Jauro muma mu gaisa shi,Abba yace Kun kyauta yara,da samari baligai zagada zagada a gidan idan zaku je ku zurma katon hijabai. Taliya Naila ta dafawa Beauty ta kawo mata da yaji da Maggi ga Kuma manja ta soya mata,Abba yace ko gobene Naila ki shiga makwafta duk ku gaisa ko,tace to ai dama zanje,dakinsa ya shiga Yar Inna ta shirya Masa abincinsa kamar wani Gomna flasks din na musamman komai na daban ne kayan Abba,butarsa ma babu Wanda yake taba ta, tashi dabance har cokali na Abba kalarsa daban me gida ran gida,Beauty sai gulmar Umma suke yi suna dariya,Naila tace Kinga Umma ko kunya,Ga surukarta ga yarta amma ta wuce. Beauty tace Kai muna kallon love,Abba Yana kwance a gadonsa yasha gyara ko Ina Yana kamshi yace me wanki Bai min wanki bane? Kubra tace wai bashi da lafiya ai na wanke s u tun jiya na goge tunda naga basu da yawa,Abba yace Kubra kin dauki makatin Hanawa ayi miki kishiya ta ko wanne ganni, na hakura,shiryuwar nan taki tayi yawa, nidai Kubra duk kin gama dani Kuma sai dai zawarawa suyi hakuri babu rabon Hashimu a jikinku Zawarawa. Beauty suna ta hira da Naila,tace Naila kin samu time sai kiyi gyaran jiki sosai kafin ki koma,Naila tace ban mu Sha" suka tafa" tace ai sabuwar Amarya zan koma wlh so nake idan na koma na gigita Spark yaji sabuwa,Beauty tace akwai sabon harka wlh wata matace har skin dinki komai in and out amma zaki kashe kudi,Naila tace ba komai Inda Spark yake ba daga kafa ai dole sai da gyara,a yau zamu je amma,Beauty tace ai ba sanya a yau din nan kuwa,duk abinda zaki yi kiyi da wuri kawai ba time. Daga wannan hirar suka fada hirar bikin Chika da ankon su da komai,suka kira Chika a waya. Sai yamma Mohsin ya dawo suka kebe da Naila suna ta hirarasu ta zumunci,zasu tafi ta dauki jaka da mayafi tace muje Beauty mu dauki motarki,Umma tayiwa sallama ta bisu. Spark ta kira taji yaje gida lafiya,lokacin Yana meeting ma bai picking ba text ya mata yaje lafiya meeting yake. Tun a ranar Naila ta fara gyaran Skin da Bado,Umma ma da dare ta bata wasu tsumin da take hadawa da kanta. Spark Yana komawa gida da magriba gidan ya dawo Masa wani kango ba kowa a ciki shuru matar gida bata Nan,yace mace itace darajar gida,da haka nake rayuwa ashe Kai na Sha wahala,gida ba dadi haka ko Ina shuru ya dawo kango,sama ya haura yace da yanzu an min Oyoyo harda zazzafan hug amma yau shuru,zama yayi gefen bed dinsa yayi shuru shi kadai yace Kai Naila ta zan iya kwana uku nan gaba kuwa babu ke a kusa,wanka ya shiga ya fito bayan yayi Sallar Isha kamal ya shugo gidan,Spark yace Alhmdllh na samu dan tayen hira,kasa ya sakko yace Ina matar gidan Ne? Spark yace ta tafi unguwa tana Kano fa,Kamal ya saki baci yace you Spark ka iya barinta ta tafi,kwana nawa? Yace 3days na Bata Kuma ni na kaita da kaina,Inda kasan an min asiri ni ban ma San wannan gigi ne da iyayi yasa na barta har 3days, wlh nayi dana sani Ina laifin yini Daya. Kamal yayi dariya yace kayi hakuri Dan Allah ka barta ta huta da danginta ai ya dace ma kace tayi 1week,banyi mamaki ba Dan ka Fadi haka ai Gwauro ne Kai baka San komai ba,yanzu ma da kyar na daure ban kira ta ba bari