← Book details Tantiriya A Gidan Yari Book 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 87

Sashe 13

Tantiriya A Gidan Yari Book 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

a bayansa ya kaita har cikin mota sannan ya shiga suka wuce, suna komawa gida Yar magen Naila data samo fara Yar karama a makwafta ta fito daga kitchen,Spark yace a samo mata muzuru mijinta a daura musu aure akan ta zama Yar duniya sabo da kina kallo zata dinga fita neman mazan banza waje ko ta dinga kawo mana kwarto gida,Naila ta dinga dariya tace namiji ne fa suka ce,yace tab ai kuwa zaki ga Yan mata suna zuwa harka gidan nan wlh haka suke yi,yace yunwa nake ji ya zauna a Palo,Ina zuwa ta furta ta haura sama ta fito bayan ta cire mayafinta,tace Baby Albashirnka yace goro yana danna waya t ace period yazo na fara wlh,kamar zai karya wuyansa haka ya dago da sauri ya ajiye waya yace da gaske? tace da gaske time ya canja,tagumi ya zuba yace a kunna min wakar Gwauro,Naila ta bude Data ta samo wakar Gwauro bata San ma ta waye ba wakar, waye yayi Oho wakar ba dadi kawai tayi searching Gwauro audio songs suka fito ta kunnawa Spark. Dariya yayi da kansa ya jawota jikinsa yace ashe yau bado ba rabo ba,ashe Kuma haka Allah ya tsara min, kawo min abinci duk da haka zan fita yakin Jihadi amma ba sulke zanje,Naila tace ai kuwa da ka huta ma kayi bacci,haka nace miki bacci nake ji? sai da na gama Azumina ya zo ba komai kwana nawa kika ce? 4days kika ce a baya 2-3days,mantawa nayi Yana kaiwa 4days, alright kin shirya jikinki yanzu? Naila tace ae ai da karfi ya taho wannan karon ban taba haka ba,yace to nayi gyaran hanya ba dole yayi flowing sosai ba ,kawo min abincina, Naila kawo Masa tayi a gabansa yau bai son zuwa dining,zama tayi sosai tace Baby idan ka gama cin abincin zamu yi wata magana,yace ai Kuma yanzu bazan iya ci ba gwara muyi maganar kawai,no Kaci sai muyi,a'a bazan samu kwanciyar hankali ba sai kin fada min kawai ki fada min mece maganar ,Naila yatsunsa ta ruko tana wasa da su tace dama....Ammmm...uhmm...a ..dama....cewa zanyi...da....waiiiii...ammmm....dama...cewa zanyi kayi hakuri,wata magana ce amma kayi hakuri idan na fada Maka gaskiya,Dan Allah karka ga laifi na,Spark ya tsura mata Ido dan tsoro ya kamashi yaga serious take bashi hakuri,taci gaba tace dama...kaga ...Mummy nasan kasan komai abinda ya faru Dani har na shiga prison to shine nace dama sai na dauki fansa sai na samu ta bayyana da kanta bani na kashe mata miji ba,shine fa muka sa Baseeru ya aureta ni na dinga bada kudi, muka shirya Masa karya har ya aureta,mun Dade muna target tun kafin na aure ka,to bayan na aureka sonka yayi min yawa,naji mun zama daya,ban iya cutar da Kai ko wani naka,Kuma indai aka ce yau wannan Dan uwanka ne to ko me yayi min zan iya yafe Masa na hakura,Kuma tuntuni nace da su Chika ni na zare hannuna a ciki na yafe mata sabo da Kai,bazan iya yiwa wacce ta rainar min miji haka ba,ta raineka,ta Maka komai a rayuwa har ka zama abinda ka zama Kuma nazo na aureka gashi nima Ina cin arziki har da Yan uwana da iyayena sai naga bai dace ba,kawai na hakura na yafe mata sabo da sonka da nake yi gashi naji Hallare ta ratsa ni,shine nace bari na fada Maka ka sani ba hannuna a ciki. Spark ya gama jinta tsaf,yace sarkin ramuwa,Naila Ina so ki sani ba komai zaki ce dole sai kin rama ba,wani abin sai dai Allah ya saka miki ki daina cewa idan an miki Abu lallai sai kin rama kinji ko,sannan ba laifi kika min ba, Kuma naji dadi da kika yi hankalin haka,ko da ace Mummy ta miki asirinta ya tonu wannan Allah ne yayi ikonsa Kuma ita ta jawa kanta duk da zanji ba dadi,amma da ace kin cutar min da Mummy Naila zan Dade Ina Jin haushin ki,Dan ni nafi sonta da Mima da ita na Saba,kawai dai halayen iyayen namu ne da matsala but no body is perfect,kiyi hakuri nasan an cutar dake amma idan kika barwa Allah ko Baki ce ba gaskiya zata yi halinta watarana asiri zai tonu,ni ban san dalilin Baseeru na aurenta ba amma nasan me gadi ne tunda nasan Alhaji Kabir da dadewa itama Mummy ta sanshi,sabo da wata dattijuwa kawar Mummy yaso aurenta Allah ne baiyi ba,ya Sha zuwa wajen Mummy kamun kafa,ita Mummy Bata San gidansa ba amma ni na san gidansa na Abuja amma ban San shine Baban Beauty ba. Come ya furta Yana kallon Naila cike da so da kauna zuwa tayi ta rungume shi ta fara kukan shagwaba tana cewa wlh an cutar dani an kaini gidan yari na Sha wahala na fasa yafewa haka kawai daga taimako da bada magani shike nan sai ace nice nayi kisan Kai duk an Bata min Suna. Dariya Spark yayi yace to yanzu ya zanyi bani da hujjar kama Mummy sai dai mu barwa Allah Kuma ma ba gashi mun hadu a ciki ba,da kaddara Bata hada mu ba fa?Naila tace ai dai sai mun hadu ko ba a prison ba amma wannan sharrin da aka min bazan manta ba tana goge hawaye tana rungume da Spark,yace to zauna naci abinci na ni,tace ban gama magana ba yace Ina jinki,tace Sanda ta tana gidan a dakko min abata,wacce sanda Kuma? tun a kauye nazo da abata a gidan na barta a dakin da aka sauke ni wlh ka dakko min abata na ajiyeta a karkashin bed dina,Zan dakko miki sai me? tace sai makaranta nima a sani a university,yace bani da ra'ayinta wlh Ina da kishi bazan iya barinki ba,zan dai saki a wata part-time Thursday Friday course daya suke yi tal Islamic school ce,Naila tace ni ta boko nake so,yace to ki shiga makarantar dare gata Nan a makwafta a biya miki na addini sanda kika iya ki koma a Dora miki idan ba wannan ba bazan iya ba. Naila tace gashi Nan Chika duk suna university a gidan yari yanzu dorawa zasu yi saura kadan amma ni iya secondary duk duniya an ci gaba Banda ni,Spark ya ja abincinsa ya fara ci Yana jinta tana ta mita lallai sai tayi boko shi Kuma yace Sam,ya Santa da rashin ji idan idonta ya sake budewa sai tafi karfinsa shi yasa yace baza ta yi ba,kar taje ta hadu da watsatsun kawaye su dinga zuga Masa mata,ga Naila dama ya aka cika bare idonta ya sake budewa. Chika kuwa tana yiwa Misam waya tace gobe ko jibi zata koma gida ita,yace tazo ya mata booking wajen kwana,tace gidan Naila zata je yace ai Amarya ce kar ta takura musu Spark zai ji haushinta,dole ta yarda ta zaci hotel zai kaita sai da ta zo yace ta shiga motarsa ta kwaso kayanta ta Maida motarsa yaja suka tafi sai gidan Rafeeq sabo da yasan Malama tana can,Islam ya tafi gida sai next week zai dawo Misam suna shiga,ya Samu Malama Ikhram a zaune sai kace gidan Ubanta,tana ganin Chika ta saki ihu tace harka sai da girgiza kirji,Chika tace wani ma yaji, shegiya Malama kice kina nan,Malama tace naga waje ai ni Kuma,Misam wuri ya samu ya zauna,Malama ta kalle shi tace Dan duniya yau ba magana ko Dan baka ganni a mumbari ba? Misam akwai shi da raini in yaga dama,Kai kawai ya daga mata,Malama ta Kalli Chika tace ko da shi za ayi ne? Kafin Chika ta Bada amsa Misam yace ae da ni za ayi,wlh da ace zata yarda da yau zan Bata sadakinta muyi kwanciyar mu tare,Malama tace bari na duba muku ko akwai a wani littafi na addini idan ya halatta me zai Hana,Rafeeq ne ya shugo ya dawo daga gidansu,Misam yace Malama da gaske nake a duba min ko ya halatta na mika mata yanzu muyi ciki,Malama tace Bai halatta ba,tashi Misam yayi zai tafi, Chika tace badai tambadadden hotel din Nan zaka Koma ba? wai ace mutum rayuwarsa a hotel,duk me haka ai ba mutumin kirki bane,Misam yace ki fada a gidanku next week zan Kai kudin aure,Chika tace ni ba wannan nake so ba in zaka daina kwana a hotel ka tura kudin aure wlh idan baza ka daina ba bazan aure ka ba ato mutum kullum Yana hotel. Rafeeq yace fada Masa Chika tunda ya fito karuwanci ya bar gidan iyayensa har yanzu sai dai yaje da yawo Yana Nan yawon ta zubar Yana barbada,Misam yace Rafeeq ya kamata kasan ni ba sa'anka bane wlh idan ka zuga min budurwa zaka sani mind your Business,sabo da ya fada maka gaskiya to sai ya fada,Malama ta tarewa Rafeeq. Rafeeq yace Kai gidana ba gidan ajiye mata bane na gaji ke Malama ki fara Shirin tafiya gidanku daga gobe wlh na gaji bana amfanuwa Dake tunda kika sabar min da kiss Baki Kara ba ki tattara kayanki ko gobe ko jibi zan Baki kudin mota ko na kaiki gidan iyayenki da kaina na gaji,kin tare min gado ko Kara baza ki min ba kice na dinga zuwa Ina kwanciya a gefe na gaji ki tafi gidan iyayenki,Malama hankalinta ya tashi sosai dan yanzu ita bata da wajen zuwa idan Rafeeq ya koreta Ina zata tafi,tana wannan tunanin Chika tace Kuna waya da Azima kuwa? Malama tace me kika ce Sam hankalinta baya jikinta,Misam ne yace zai tafi,Chika ta tafi raka shi tana fita ya rungumeta tace ka sake ni please kar a kamamu,ya sake kankame ta,Rafeeq ne ya bude kofa ya fito yace zan rufe gidan,da sauri Chika ta fisge kanta,Rafeeq yayi dariya a ransa dama yasan Misam zai aikata shi yasa ya fito sa Ido. Misam yace ke da gaske fa nake maganar Kai kudi,Chika tace to sai nayi tunani na gano hanyoyin zama da me neman mata,Ran Misam ya baci sosai yace me yasa bakya tauna magana kike fada min ne? Chika tace idan kayi zuciya ka daina,sai na aure ka duk kasan mata kaje ka min Illa Ina sabuwa gal Kai second hand,zuciya yayi ya juya ya shiga motarsa ya tafi ransa a bace,Chika tace ka dade baka yi fushi ba in naga dama ma sai na fasa mutum kullum a hotel wlh bazan aure ka ba in zaka canja
Chapter 13 · 0% Book details