← Book details Tantiriya A Gidan Yari Book 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 45 OF 87

Sashe 45

Tantiriya A Gidan Yari Book 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ga mahaukata nan iri iri,bangaren mata daban haka na Maza ma daban,ciki suka shiga aka duba file dinta sannan Likita yace wai mata me kiran yarta? Jauro yace ae,yace Kun dauke mata yarta ta kasa mantawa sai cewa take 'yata kullum shine abinda take furtawa kawai,amma fa yanzu tafi baya samun lafiya an canja mata bangaren masu sauki sauki. Likita yasa aka rakasu Inda suke gasu nan masu dama dama mata abin tausayi ko wacce da abinda take yi,Jauro ya nunawa Iman wata farar mata duk da tayi duhu amma kawo ta asibitin ana gyara su ta sake haske,suna samun abinci akan lokaci tayi kiba kamar me lafiya,tana zaune Jikin dangar wire ta zuba tagumi tana cewa 'yata,Iman bangarenta ta koma tasa hannu ta cikin wayar tana Jan rigarta da take fes sabo da Jauro Yana Kai sutura akai akai har wasu mahaukatanma ana basu,Iman tace Umma,matar kamar Bada ita ake ba ko kulata bata yi ba tana ta faman soshe soshe ta rike jarkokin ruwa da lemo a hannunta ta kankame,Iman gashinta da yake buzaza ta jawo kadan,a fusace ta juyo ta kaiwa dangar wayar duka,Ido suka hada da Iman ta fara masifa ba a San me take cewa ba,ta juya ta zauna abinta,Iman tace Umma Ina Kwana an tashi lafiya ta kwala da karfi a kunnenta, ta sake fusata ta jefo mata robar ruwan tana bala'i, gashinta take sosawa,Haidar tausayi mahaukatan suka bashi harda hawayensa yace gwara a yo ni a Dan shege akan ciwon hauka wlh,Ina rainawa ashe ni'ima Allah yayi mana a haka,Jauro yace to wasu a haka zasu koma ga Allah. Iman magana take mata tace nice 'yarki gani sunana Iman,Juyowa tayi ta Kalli Iman ta sake kawowa wayar duka,Iman Ayaba ta mika mata ta wayar,Fisgewa tayi ta cinye har bawon,ta sake mika mata wata ta sake Fisgewa ta cinye,tura mata ta dinga yi tana ci,Haidar Yana bawa wasu shima mahaukatan,abin tausayi Iman idonta ta faka ta Dora yatsanta a kanta wai addua zata mata, ta fara karanta mata ayatul qursiyyu a kunnenta ta baya,tashi tayi tana ihu da kururuwa tazo ta daki Jikin wayar, Iman tsoro taji ta gudu daga wajen,tace Kawu mu tafi karta fito,Kawu ya ja su suka tafi,Iman harda murna yau taga babarta,da murna ta shugo gida,Annoor ta samu ya juya baya Yana waya tayi tsalle ta dane Masa baya,da bai da karfi da tuni sun fadi,tace yau naga Umma Dan boy, ta dire zata gudu,ya riko ta da sauri yace nine Dan Boy dama jiya kin ce min yaro,yi hakuri wasa fa nake,tana hannunsa ya Maida wayarsa aljihunsa ya fisgo ta jikinsa suna kallon juna, a hankali ya Dora lips dinsa Saman nata Yana gogawa a hankali,Haidar ne yayi gyaran Murya suka matsa da sauri,Haidar yace Dan Allah karka karasa zakin nata idan anyi aure ka rasa dadin ya kare Kuma,Annoor yace Ina ruwanka idan ma na rasa ai nine ba kai ba,Kai da duk an shanye naka fa sai sa Ido. Rahma da shigowarta kenan tace ana Dan ehh din ne? Karima ce tayi sallama tace Dama Wajen Annoor nazo wai Dan Allah video da na Gani na gaske ne? Annoor ya shafa Kai yace gaske ne mana first night muka yi,tace da wlh ban yarda ba,yace to ki yarda nine,Iman idonta ya kawo ruwa tace shike nan kowa ya kalleni duk Wanda ya min haka ban yafe ba,Annoor yace rufe mana baki ke ba mummuna ba mene abin damuwa, mummuna shike da kunya,ai raping dina kika yi,kin kaini hotel kin bani kwaya,kowa a gidan nan yasan yanda kike nace min, Nabeel Dake zaune yace makaryaci ka cuci yarinya ka hanata magana wlh kaji kunya,Nan kullum kake mata gori kana sata kuka Ashe Kaine. Haidar yace ai yaji kunya wlh babu gorin da Bai mata ba,Nabeela Bata c e kala ba wayarta take dannawa,Rahma tace Kun fa damu Annoor shi dai yaji dadinsa, Annoor yace a gidan uban wa naji dadin? ban San komai ba kice naji dadi,tace an barka a baya,ai ko romance da dadi bare wanga lamari,Annoor ya Kalli Rahma tace ke fa Baki da kunya Aure nake so wlh nima a dinga ehh...dani,dariya suka yi tana magana tana daga gira,Kamira tace yara kuyi aure da wuri,Annoor yace to zamu yi nine karami nine babba Kuma duk na wuce su Nabeel da Haidar,sai dai su ga ana shawara dani su kuwa ace yara ne,Dariya Haidar da Nabeel suka yi,Nabeel yace bazata zan muku wlh zaku sha mamaki. Iman juyawa tayi zata tafi Annoor yace zauna Yar fyade kinyi min ta'addanci zaki tafi,zama yayi a kujera ta zauna a hannun kujerar da yake zaune gefensa suna Hira ya juyo yace yi min kitso na,tace ai ni ban Kara Maka Kaci gaba da daure gashinka da band,hannu ta zuro ta kasan habarsa ta dora tafin hannunta a gefen fuskarsa Yana surutu tana mararinsa kadan kadan,suna magana da Nabeel ya janye hannunta a hankali, ta Maida hannun Saman goshinsa tana Jan gashin girarsa,Yana magana sai ta hade lips dinsa ta rike gam da hannu,dariya yayi yace meye haka zan mareki wlh kasa ya turota ta fado,yace bakya ji,zama tayi ta nutsu sai ya koma sa kafa Yana turata,kafafunsa yasa tare da sarkafo kanta ya matse tayi ihu yaki saki sai da ta Sha wahala,tana gaban kujerarsa a zaune ta juya baya ya sa kafarsa daya a Saman kafadarta. Karima tace kudai idan kuka zauna bakwa iya nutsuwa,sau nawa za a fada muku ba muharramai bane ku amma bakwa ji ku jira a daura,ai ko saurarar Karima basu yi ba. Abba kwana biyu bai je wajen Jauro ba,Jauro ya kira Abba yace mutumina kwana biyu? akwai labari bikin yaranka ya taso zanzo mu tsaida rana ko kuwa? Abba yace nine Waliyin Iman a kawo kudin an gani ana so,da na gaisuwar iyaye,da duk wani Abu na Al'ada a kawo min ni waliyi,Jauro yace sannu Kaine ma ka raineta ashe, to baka isa ba in zaka daura ka daura,Abba yace za kuwa aga delay ranar zaku Sha wulakancin Waliyin Amarya,mu tsaida ranar a waya mana sai kazo Dan ka Kalli Yar Inna,Jauro yayi dariya yace wallahi sai na zo yau ko kaki ko ka so,ni kazo ka dinga min shishigi a gida ni Kuma kace bazan zo gidanka ba sabo da wata Yar Inna,kana ji ma Maman Annoor ta bani zabi tace na samo mata miji na gari,Abba yace gani babban abokinka tunda fara ce, farare ai sai mu,Jauro yace da kaina zan daura,kaina na zaba mata ai tayi ganganci da tace na zabo mata wallahi da Kai zamu je ka tsara ta,Banda tone tone Kuma,Abba yace nine shugaban masu tsara Mata ai cewa zanyi tayi dace an samo na kirki,kayi addua dai kar ranar tazo min a me fadar gaskiya na tona asirinka billahillazi,Jauro yace ka rufa min asiri Dan Allah. Abba yace kace Allah na yarda idan ango yaje sai taga Kaine,Jauro yace iyakaci tayi kuka ta share hawayenta daga Nan Kuma taci kaza me 'ya'ya,Abba Yana ta dariya yace lallai kuwa me 'ya'ya. Abba Yana wayarsa a rumfa kawai sai ga mota hadaddiya tayi parking,Naila ce ta fito Spark ma ya fito,yace ba sanarwa,Naila tace ai dama nace bazan fada ba idan zanzo,Abba Baki ya rike yace Naila Allah ya yarda. Wannan kiba haka ai sai ace balarabiya ce,Naila tayi dariya,Spark yace Abba gaskiya sana'ar Nan a canja me kyau,ba Wanda ya isa ya canja min sana'a a Nan zanyi arziki,arzikina a Nan yake sana'a kusa da gida Ina gajiya na fada gida abina na kwanta, Yar Inna ta kawo min girki Ina zan iya Nisa da gida,ai ni sana'a indai ba a kofar gidana ba bazan yi ba wlh,baza a sani tattaki ba,Spark Yana sani yace to Abba Allah ya Kara girma,Abba yace girma wanne irin kake so nayi Kuma? Ko Dan bakin ciki ne Kai? so kake Yar Inna ta daina so na tace na tsufa da yawa,duk girman da nayi bai isheni ba sai Kace Allah ya karo min wani,rannan haka kace Allah ya Kara sutura a fakaice fa zagina kake yi wato bani da sutura ni takala kake so kace. Naila suna ta dariya tace Abba bafa haka yake nufi ba,ai yanzu kinfi son miji da kowa me yake fada miki ne a daki Naila? Naila tace Abba rada yake min,Abba yace uhmm muje to gidan yau Yar Inna bata Jin dadi komai na gidan nan ni nayi. Naila gabanta ya Fadi tace Allah yasa ba ciki bane,Abba yace Ina ruwanki da ciki ne ko ba shi ba,baki da kunya fa ke,me yasa ke mijinki baiyi kokari ba,Naila tace ai laifin kwayaye ne,Abba yace ki zauna yarda da likitoci ki Sha wahala bazan bata lokacin yi miki addua ba akan haihuwa sai ta karbu kin fara na jiki a asibiti kin tafi Family planning kice a dakatar da ita,Spark yace ai kuwa kamar mun je,Naila tace Spark muje,Abba ya kalleta yace ba kyau fadar sunan miji kasa girgiza take in aka Fadi Sunan miji,Naila tace ya bamu ji ba to,ai ba a ji Dan ubanki,wani Spark,to Ina alawar taki da kike kiransa da shi ko har an tsotse alawar ta kare? Spark ya dinga dariya yace da saura tana Nan Abba kwali kwali,kuka ta fara min sai na kawo ta,Abba yace rainaka tayi,Kai kayi sake mace ta rainaka ba Rancen kudi take baka ba sannan ba kyauta take Maka ba,babu komai da take baka ka zauna ta rainaka,ai Wanda mace ke bawa Rancen kudi shi ake rainawa me matacciyar zuciya. A Watso sharhi TIKTOK ASMABAFFA AREWABOOKS ASMABAFFA 1 AsmaBaffa [1/21, 9:17 PM] AsmaBaffa: PAID GROUP 300 ACCNT NO 0175487861 YAN NIGER +22790795939 TANTIRIYA A GIDAN YARI BOOK 2 ~YARAN JAURO~ 56-60 Official AsmaBaffa SADAUKARWA NE GA AIDA MAMAN TASNIM PAGE NAKU NE Umu Afrah Fiddausi Yaro Queen Spark suna shiga gidan Abba suka samu Yar Inna a zaune tana ninkewa yara kayan wanki,Abba ya kalleta yace Yar halak taji sauki,Naila Sallama ta kwala dan aji itace Umma Amarya tazo ganin gida gani,Kubra murmushi tayi tace to sannu da zuwa amma shine baza ki fada ba, Spark rike da Yar akwatin Naila da alama za a kwana biyu. Abba yace Naila harda akwati ke bazai yuwu ba zaki asarar ladan gidan miji har na kwanaki, Spark
Chapter 45 · 0% Book details