← Book details Tantiriya A Gidan Yari Book 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 87

Sashe 34

Tantiriya A Gidan Yari Book 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

da dafe kumatu,kafa yasa ya kwashe mata kafafu ta Fadi rim a kasa bakinta ya fashe,Misam Yana daga nesa yana zuga yace use your charger,tana yashe a kasa yace ke naki San ko a titi ma naga mutum zaiyi hauka ba gyara shi nake yi wlh,ko ban sanki ba Ina iya tsayawa in chasa ki,ya dinga tsula mata wire,sai da Mima ta fito tana masifa wai haukacewa kayi ne na shiga uku ni dai Ina zan sa kaina? Arham yace Saman pillow mana,Mima ta bi shi da duka ya gudu,Spark yace wlh daga yau duk Wacce ta Kuma zagin matata sai taga abinda zan mata. Mima ta fashe da kuka tace wlh asiri suka yiwa Dana sun bashi manta uwa baya ganin kowa a gabansa sai matarsa akan Naila ka zauna ka daki kanwarka uwa daya uba daya Kuma tana da aure ni dai Ina ganin jarabawa,ya zanyi da rayuwata duk cikinku ba na dauka, to wa kuke so na kama? Arham Yana daga nesa yace Allah,indai Mima zata yi magana ya dinga bata amsa kenan. Spark yace ni fa idan zaki musu fada ki musu wlh duk Wacce ta sake zagin matata ko gobe ne sai na zaneta,me tayi musu a kyale min mata ta wala idan Kuma ba haka ba wlh zan hanata zuwa wajen kowa muyi rayuwarmu daga ni sai ita,nine dolenku ni sai nazo,ta ya za ayi yara suna ba daidai ba baza a fada musu gaskiya ba,Mima tace Kai din dai dai kake yi? ni dai na fada muku ku fada musu gaskiya kar nazo Ina balla yarinya ace nayi laifi,baza su Kara zuwa gidanka ba inshaallah cewar Mima, Spark yace da na huta wlh dama ni takura min suke mutum Yana soyayya ana ta sallama kar su zo ni na zo mu gaisa,abinda take bani duk duniya babu me bani sabo da haka a kyale min abata,Misam yace wlh kuwa kana haka Kai haka sai dadi,suka kama dariya yaran Maza sabo da yanda Misam ya gwada da hannu yanda ake lagude mace, Mima ta juya tace Allah ya shirye ku ni ba fitsararriya ce ba. A cikin bedroom Inda Mummy take kwance a Saman bed bata motsi malamai sun zagaye ta sai sheka mata karatun Qur'ani ake yi,Mima ce a gefenta tana amsawa Ameen Allah ya tashe ki Yar uwata,Mero tana zaune a Palo a cikin yan uwan Mummy,ganin Spark ya zane su Anam shine suka kira Anam da Wahida suna lallashinsu,Wahida tana kuka tana goge lebenta da ya dan fashe tace kawai dan anga babu uwata tana gidan yari shine ake min wulakanci gani ake kamar bani da mijin aure, kamar kowa baya Sona Ina da samarina kawai na aure ne Allah bai kawo ba,Mero kamar an saka da ita tana cikin manyan iyaye duk wulakancin da ake mata da kallon banza amma sai zaraf tayi ta karbe zancen tace ai kuwa mazajen aure basa wahalar samu ki nuna bakya son kudi ki Gani in baki samu miji ba,ko dan talaka ai zai fito,wata ce a cikin kannen Mima ta gasawa Mero Harara tace dalla tashi yar kauye gayyar neman talauci,Mero tace Kuma ai ba daga birni kuka tsiro ba asalin tsoho da tsohuwa daga kauye ne,Maman Rafeeq ce ta fisgo Mero Allah yasa ta kwace ta gudu. Naila ce ta kara so ciki tayi Sallama da kyar suka amsa mata,suna mata kallon banza ta durkusa ta gaida su lokacin Spark ya shugo palon,tana gaishe su yace taso Baby ya rike mata hannu ta mike ya zaunar da ita a kujera daban yace yi zamanki a nan ba ruwanki da kowa,tace to, rada ya mata a kunne yace kinyi kyau amma an yafo guntun mayafi ga Maza ko Ina,Naila tace Banga babban bane,dole sai ita ba sai a canja wata ba,ai ni ita nake so,shike nan to ya zanyi da ke Allah ya yafe miki,murmushi tayi. Rafeeq baya gari yau shi tun safe ya dira a Kano ya kama hotel zai je gidan su Ikhram ya kasa hakuri da rashinta,tunda suka yi waya ya lallaba ta har ta bashi address dinta wani abokin Spark ya kira a Kano ya bashi mota da driver dan bai San ko Ina ba in banda gidan yari,Driver ne yazo da hadaddiyar mota bai fadawa Ikhram zai je ba sai yamma 5pm ya nufi unguwar su dake Sabon gari Kano,Ikhram a unguwar arna suke Bariki ce dandalin iskanci,duk wasu club da wani wajen karuwanci da iskanci a nan suke,Address din da ya rubuta driver ya dinga bi,suna zuwa layin kadan suka tsaya suna tambayar gidan Yahuza donation. Wata Rafeeq ya hango kamar Ikhram a wata Yar rumfa cikin dandazon mutane tare da wata dattijuwa da alama matar yare ce tana tsaye tana zubawa mutane doya da kwai sai Egg in to Egg wata budurwa tana soyawa,daya kaskon Kuma Ikhram ce a zaune tana ta soya kosai tana zubawa a kwandon tsane Mai tana mikawa matar tana zubawa mutane,hayaki ya tirnike,Kuma abinda ya gani shine Ikhram sanye take cikin doguwar rigar material boubou ta yafa dan siririn mayafi,Rafeeq yace da driver daina tambaya ma gata can wajen wacce nazo wajen masu doya da kwan can,driver motar ya ja suka karasa wajen a hankali,yace jira ni,ya bude motar a hankali ya fito cikin shadda Sky,Rafeeq Dan gayu ne na gaske shima ya Sha kyau kamshi kawai yake,Ikhram bata taba zato ba ko motar bata kalla ba tayi zaton ma masu siyan kayan su ne,ta dukufa tana suya,kamshi taji a kusa da ita ance a bani kosai,dagowa tayi da sauri taga Rafeeq. Dariya tayi tace wow shine ko waya? Dattijuwar ta kira da Maman chinyere nayi Bako zo ki karbeni,Maman Chinyere da bala'i tace to a kudinki na yau sisi bazan baki ba karki ce ban fada miki ba woooo, Kuma karki rasa abinci kizo gidana roko,Ikhram tace na yafe kije da kudinki Madam,kin San halina duk girmanki zan iya chasa ki Maman Chinyere karki Raina min hankali ga mata nan da yawa zan iya komawa wajensu su bani aiki ta ja tsaki. Rafeeq let's go ta rike hannunsa,shi mamaki yake wai ita ya rayuwarta take ne ya kasa ganewa,yace har an nuna mana gidan Yahuza Donation sai na ganki,tace ae ba nisa ai,Rafeeq yana ta kallon Yan bariki ana ta harka da giya musamman da yamma ce kida ko Ina tashi yake,sannan musulman basu da yawa duk yare ne a unguwar. Wani gida suka je Wanda ba nisa da Inda suke soye soye,gidan haya ne da alama irin katon nan ne daki daki ,duk daki uku da toilet dinsu haka gidan yake,duk gidan ya kwararrabe sannan musulman ciki kawai su Ikhram ne da bangarensu me gidan daki biyu ya kama,daki daya na Yahuza Donation ne da matarsa uwar gida Asabe ga Asabe da yaranta har shida duk,daki daya na Amaryarsa da yaranta uku, sabo da kishin da suke ko wacce yaranta a dakinta suke kwana ana musu shimfida a kasa ita Kuma matar da shi suna Saman gado kamar rayuwar arna. Ikhram babu dakin da zata Kai Rafeeq ko daya sai kujeru farare ta aro musu guda biyu,suka zauna a Jikin katanga,Donation ne ya shugo cikin kana nan kayansa yaci zanzaro gashi Dattijo kana ganinsa kaga dan duniya,murna yayi ganin Ikhram da me kudi yaga katuwar mota a waje dama Mayen kudi ne Kuma ya matsu shi dai Ikhram ta bar Masa gidansa tunda baza tayi abinda yake so ba. Uncle sannu da zuwa nayi bako,Yahuza yace madalla,Rafeeq ya durkusa ya gaida shi ya amsa Yana washe baki,ba ruwansa yace Ina Stella.... where are you come,Stella ta fito wata matashiyar arniyar ce Karuwa ce Yar gayu da ita,yace ki bawa kanwata dakinki zata yi zance tayi bako, Stella tace dama fita zanyi zanje na'ibawa a can zan kwana ko kwana zasu iya yi,Rafeeq Yana Jin haka yace ai kwana zanyi dama,Ikhram ta Harare shi,Uncle harda Jin dadi yace ba damuwa daga nesa kake ko? yace tun daga Abuja Uncle,Yahuza yace ahh dole ka kwana ai dole a baka masauki,Stella jaka ta dakko ta fice bayan ta mikawa Ikhram key, Rafeeq yace na gaji dama Yana dariya a boye,Ikhram tace shiga, suka shiga dakin Stella ya Sha uban gyara sai kamshi ko Ina Kal Kal komai na ciki me tsada ne. Ikhram tayi bako bata da ko sisi,Rafeeq driver ya sallama yace yaje gobe zai neme shi,su kansu yaran Yahuza da matan haka suka yini da yunwa ba ayi girki ba,bare Ikhram rabonta da abinci tun jiya da dare,fitowa tayi taje wajen uncle tace Uncle Dan Allah ko rancen kudi ka bani na samu na sallami bako,Dan ubanki me yasa bakya wayewa Baki ga yanda ake karbar kudin samari ba ai su suke nada kudi ana musu girki Muma idan ya bayar a dafa damu muci arziki,Ikhram tace sai kace Karuwa,yace to ki barshi haka dan tani,komawa tayi wajen Rafeeq kamar tayi kuka tace Masa Ina zuwa again ta fice duk Wanda ta sani suna mutunci taje neman bashi bata samu ba dake Bariki ce ba mutunci,sake dawowa tayi ta kasa shiga dakin da Rafeeq yake ta fara hawaye sai data yi kuka sosai marar sauti sannan ta goge hawayenta ta koma ciki,kallonta yayi yaga alamar kuka tayi,yace Ikhram mene ne? tace ba komai,Driver din yayiwa waya yace ya kawo Masa motar,driver yace gashi Nan,yace je ki shirya mu fita,tace daga zuwa Kuma ban kawo Maka ko ruwa ba fa, yace ba komai je ki shirya dai,Ikhram fita tayi ta karbo Masa bashin ruwan roba kato Eva da lemo a wajen me kanti ta kawo Masa,yace wa ya saki,tace ka Sha bari na shirya ta fice. Masu Sharhi Ina godiya Dan Allah kuyi following dina Arewabooks AsmaBaffa1 TIKTOK AsmaBaffs AsmaBaffa [1/16, 9:33 PM] AsmaBaffa: Paid group 300 ACCNT NO 0175487861 ASMAU GARBA MUHAMMAD GTBANK YAN NIGER +22790795939 TANTIRIYA A GIDAN YARI BOOK 2 ~YARAN JAURO~ 41-45 Official AsmaBaffa SADAUKARWA NE GA AIDA MAMAN TASNIM PAFE NAKI NE MAMAN SAMHA Yaran Yahuza Donation duk kana ganinsu abin tausayi sai iyayen ne mata suke samu suka Dan siya musu wani abin suka sa a bakin salati, shi Yahuza ya riga da yaci me kyau a waje ba abinda ya dame shi" Yayi mutuncin gaske ya bayar ayi girki sau Daya a rana, yawanci
Chapter 34 · 0% Book details