← Book details Tantiriya A Gidan Yari Book 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 87

Sashe 6

Tantiriya A Gidan Yari Book 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

bedroom,okay ta zauna da kibiya,gashinsa me tsayin gaske kamar na mace,ko macece ta samu wannan sai ta godewa Allah,Nabeela ce ta fito tayi Shirin fita tace Yaya zanje practical,yace a dawo lafiya Yan mata,Yaya kawata fa ta kyasa tana so wlh kullum sai ta min zancenka,Murmushi Iman tayi tace tazo mu ganta idan tayi mana shike nan,Nabeela tace Yaya kasan Iman dinka tayi saurayi wlh,yace haka nake so ai,dama duk kyawun kanwata ace ba saurayi gashi anyi candy, wucewa Nabeela tayi ta fita,Rahma tana dining me aiki tana shirya mata breakfast kida take ji tana bin Waka sanye cikin Kayan baccinta duk jikinta a waje,Nabeel Yana fitowa a dining ya zauna shima ya saci kallon Rahma ya tabe Baki yace kina cutar kanki da wuri zaki tsufa tunda kika ce Maza zaki dinga mikawa jikinki,Dariya Rahma tayi tana bin Waka tana jinsa tace Nifa Yaya wallahi wallahi ban taba sex ba kawai dai nasan ana Dan motsa min jiki sai club da nake zuwa,ai kin dauki Matakin Kai kanki din ayi sex daga Nan ai sai Sex Kuma ke kika sani idan zaki gyara ki gyara idan ba haka ba kina kallo zaki auruwa,Rahma tayi dariya tace duk iskanci na ai kadan ne akan Laila da Karima ,ai sunyi aure su da yaran su magana ta wuce,Uhm wai Yaya ka duba Laila yanda tayi dacen miji duk iskancin Laila,Laila ce tayi Sallama da yaranta sai ga Karima ma tazo da yaranta da Sajid babban Yaya da matarsa Meenat da yaransa,Annoor suka kalla Wanda Iman ke Masa kitso Yana zaune Saman Sallaya tana kujera,gaba daya bayansa Yana Jikin Iman ya lumshe Ido Yana gyangyadi,Sajid ya dura Masa ashar yace wai mutum sai kace saurayi da budurwa karfa ku manta ubanku Daya,Iman ta gaishe su tace to ni Ina da saurayi na Kuma shi zan aura shima Yaya budurwa zaiyi kawar Nabeela ce,Sajid yace Allah yasa ta dore waccen karon da yayi budurwa ai kece kika koreta duk Inda za a kaita Dake ake tafiya,wai ya Kai budurwa shopping amma ya kyaleta Yana wajen Iman suna ta surutu sunyi banza da budurwa ai dole ta hakura da Kai,Karima tace ke Iman wlh ki gyara halinki Dan uwanki kin hanashi sakewa,ya koreta amma kamar mayya,dariya suka yi family guda suka zauna ana ta Hira suna wasa da dariya kowa uwarsa da ubansa daban amma basu sani ba duk sun zaci Yan Uba ne,Har Gulmar Jauro suke yi da Haidar ya fito yace Wlh Kawu yayi aure-aure wannan son mata haka,tunda naji kullum ni dai burina na so mace nasan wlh gado nayi,Allah ya rabani da aure-aure irin na Kawu,Annoor yace Kawu auren dandano yayi a baya yanzu Allah ya shirye shi ya rike mata biyunsa,shi yasa dukkan mu kamar kowa daban babu me cewa Yan uwa ne mu to anyi aure-aure cewar Karima, tace babu Wanda yayi kama da Kawu,Allah sarki ga matansa Uwar gida uwar goyon mu bata taba haihuwa ba,Na'imatu Amarya ma haka,Gwara da bata haihuwa wannan Amaryar shegiya cewar Rahma,Annoor yana jinsu bai fiye magana a gidan ba amma a wajen abokansa kwallon shege ne ba irin abinda baya fada,a gidan Kuma yafi kowa hankali sai dai shi Bai kula mata ma ko budurwa ce sai dai a hada shi da ita, bai taba Gani yace Yana so ba. Jauro ne ya fito cikin shiri zai fita daurin aure dukkan su suka ce gaskiya yau Weekend Kawu baza ka fita ba Hira fa zamuyi ta zumunci,Jauro yace Allah na gode Maka yarana Yan Albarka ku bani 3hrs zan dawo,mu bamu yarda ba wlh Kawu sai ka rage mana suka hada baki Dan idan Jauro ya zauna dole suci dariya sabo da shima wani dolon ne,yace to 2hrs suka ce mun yarda,Na'ima Amarya sai wani cin magani take tana Harare Harare ta wuce,Habiba Uwar gida itace ta fito tayi wanka cikin atamfa super tayi kyau ta zauna yaran su Karima suka tafi wajenta da gudu,sannan suka gaisa tace yau yini akazo mana kenan amma waya kuka yi na sani,Karima tace ae mana dama yau muka shirya zuwa. Habiba tace Iman an gama jarabar kitson ne ayi mutum kamar mace,Annoor yace Ummi Kinga kitson nan farin jini yake karawa duk Inda naje wawata akeyi,dariya suka yi Ummi tace ko baka yi kitso ba ai dole ayi wawarka Annoor balarabe haka da Kai,Iman tace Ummi nifa? tace ke ai da shuwa kika yi kama,Iman tace nafi karfin Shuwa ni sadaka yalla ce fa,dariya suka yi. Ba a dade ba Jauro ya dawo cikin yaransa ya zauna Nabeela ce kawai bata nan. Yana zama Karima tana nunawa Rahma Abu a waya tace Kalli Yar karya wai mutum dole sai ya nuna shi me kudi ne a social media,Jauro yace Banga laifin su ba,ace a fili a zahiri ka zama talaka a online ma sai ka zama talaka a'a da sake suyi karyar su wlh ai dukan sai yayi yawa a zahiri talaka a online ma talauci ai bai dace ba,ni Wanda ma suke bani mamaki yaran nan kune Yan boko ku Kara min haske tunda nake a rayuwa ta ban taba ganin kamfanin giya sunyi talla da mutum Yana cikin maye ba,ko Yana tangadi da tangal tangal,ko yana soki burutsu, ko sau daya ban taba gani ba ko a labari,gasu da customers da yawa amma basu sasu a talla wai basa farin ciki da masu Shan ta ne? Dariya su Annoor suka yi Nabeel yace Kuma fa haka ne wlh Kawu,Jauro yace tun Ina yaro nake wannan tunanin ko kunya suke ji ne, mashayan na basu kunya oho. Rahma ce ta daga wayar saurayinta tace Malam karka dameni jiya Dana kiraka da dare matarka ce ta daga ta kashe wayarta ta ja tsaki,Jauro yace maganinki kenan sau nawa ku yan matan Ina gargadinku idan kunyi samari karki sake ki dinga kiransa da dare matukar Yana da mata to yawanci wayar bata hannunsa in kin ganshi a online karki magana matarsa ce a Kai tana patrol,wallahi Ina rabaku mata patrol suke na mazajen su cikin dare basa baccin kirki. Wani Yana can Yana bacci ita ta dauki wayar tana patrol ke Baki sani ba,idan karya nake ga Habiba nan haka take yi musamman lokacin da kuruciya ta,Matar Jauro Ummi taji kunya tace ai lokacin kuruciya ce yace to kunji ko da kunnen ku,Ina so ma next week Kai Nabeel,Annoor,Iman ku shirya muje gidan babban Aminina na kauye Hashimu,Haidar yace ni banda ni? Kai aikinka Yana barinka ka zauna ne kullum kana Office,yace to zanje ai yace Allah ya kaimu sarkin naci,Nan suka yini suna hira gwanin sha'awa. Nabeela dagewa tayi lallai sai da ta hada Annoor da kawarta Sameera ta hada su soyayya, tun bai yarda ba har dai ya yarda,Iman kuwa da saurayinta Huzaifa suna ta soyewa a waya kullum har Zance Yana zuwa,Annoor bedroom din Iman ya shiga ya sameta a kwance tana chat yace ki shirya yau zamu fita shopping,tace wow amma da Huzaifa ne yace zai kaini,yace to mene a ciki kice ya taho kawai,sai mu hadu acan tare ba damuwa nima ai Sameera zata je Kinga shike nan,tace to tana murna. Huzaifa ta fadawa yace Ina Jin kunyar Yayanki amma ba damuwa ai tunda shi ya amince,tace wlh ba komai ai yayana na musamman ne,Iman da Annoor a mota suka tafi su kadai sai yayiwa Sameera waya wai su hadu a can,Sameera tayi mamaki shi da zaizo ya dauke ta,haka ta tari taxi taje Inda yace,Huzaifa ya kira Iman dan Iman ita ta manta ma da saurayin nata Sam,tace mu hadu a can ai kasan wajen ta kashe wayarta ta juya ta Kalli Annoor suna Hira suna dariya cike da nishadi. Yaya ni....ni....tana zuba shagwaba...yace ke me Baby ..kallonsa tayi muna zuwa Ice cream zan fara Sha,yace uhm naji ni bazan Sha ba yau kina ta jawo min Mura tana kamani,to me zamu ci? Shawarma tace yessss ..itama tayi ya mika mata hannu suka tafa,suna zuwa Sameera taje itama Huzaifa yaje,tunda Annoor yace da Sameera Hey bai sake bi ta kanta ba kawai ya rike Hannun Iman yace muje ciki,Huzaifa ya tsaya Yana kallon ikon Allah. Sameera tace yayanta ne ubansu daya karka damu shakuwa ce muje suka biyo su a baya amma hankalinsa gaba daya akan Iman yake,duk abinda take so shi yake zabar mata da kansa tana nunawa,har layin Inners suka je Sameera tana bayansu itama da basket dinta tana jida,Huzaifa bakin ciki ya cika shi Yana yiwa Iman magana tace Oh Baby kazo ka zabi kayanka kaima ta juya ko sake kallonsa bata yi ba,Annoor ya dinga zabo mata bra duk size dinta ya sani,tace gaskiya kanwata ta girma kice yanzu size ya karu,Iman tayi dariya tace Allah Yaya kana bani kunya da ance maka a haka zan ta zama,dariya suke yi suna nishadi,Huzaifa fita yayi ya jira su a Jikin motarsa,Sameera kuwa bacin rai ita kanta ya dameta wannan ai wulakanci ne. Su kuwa Annoor da Iman ko a jikinsu sai da suka gama,Maryam wacce ta taba tura Yan sanda suka kama Annoor tana labe tana kallo,bibiyar Annoor take kamar mayya,tace Alhmdllh lokaci yayi sai na jaja Maka masifa tunda kaki so na,wannan Iman din ta hanaka komai karshe har wata budurwa ma zaka yi,da sauri ta koma wajen yaranta da ta basu Kwangila wasu kartan Maza su hudu. fitowa suka yi suka yi sai lokacin Annoor yace sorry Sameera Dan Allah shiga mota muje,Sameera ta danne bacin ranta tace ba komai,Iman ma haka ta karasa Inda Huzaifa yake ta bashi hakuri. Masifa ya fara yace kin San wulakantani zaki yi kika ce nazo? tace akan Dan uwana kake kishi,Dan uwana ne fa mene ne haka zargina kake yi? yace no amma kin min daidai kenan? Idan ba dama na hakura...,da sauri ta mika hannu zata rufe Masa baki Annoor ya rike hannunta da sauri ya wayance yace sorry Huzaifa muje mana yawa kake yi,Huzaifa shima dannewa yayi ya shiga motarsa suka wuce garden wurin Shakatawa,Masu bibiyar Annoor Kuma yaran maryan suna binsu,sai da suka samu sit suka zauna wajen na masoya ne,a wajen ake siyar da su Ice cream,cake da tarkace daban daban,Iman sarkin Ice cream irin masu Dan siyar da biscuits cream ta kira bata san ana bibiyar su ba,cikin yaran Maryam dinne Daya
Chapter 6 · 0% Book details