← Book details Tantiriya A Gidan Yari Book 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 87

Sashe 25

Tantiriya A Gidan Yari Book 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

gane gaskiya na maidata gida,cikin ikon Allah ta samu miji na gari me kudi ya aureta a ta biyu a Nan Jigawa kaima ka Santa Nabeel kana zuwa kaji asalinka,tana da yara shida yanzu da Mijinta,Kuma itama ni na mata kayan daki da komai,babanka yanzu ban San me yake ciki ba amma dai nasan ita mahaifiyarka ta sani tunda ta fada min. Sai ke Laila Mahaifiyarki Zahrau,yaren Edo state ce,ba musulma bace a lokacin tayi aure a Lagos Bata taba haihuwa ba,kasuwanci ya kawo mijinta Arewa Kano,ya Dade a Kano katsam sai ta musulunta wannan yasa ya mata duka ya saketa,ya fadawa iyayenta suma suka ce basu ba ita kar ta dawo wajen su,akwai wani malami babba Malam Yusuf a unguwar da suke shine ya musuluntar da ita,bayan abinda mijinta yayi mata sai ta koma ta fadawa Malamin,ya lallasheta yace ta dawo gidansa ta zauna,haka ta koma can da zama sun Saba da matansa,tana sha'awar namiji amma kowa a musulmanmu sunki aurenta da ta samu saurayi sai iyayen saurayin su hanashi aurenta suce ai Tubabbiya ce sabon musulunta ce,kowa ai ta cewa Tubabbiya ce ana kyararta ana ganin ma kamar ba wani addini take ba,to yare sun Saba da saka kaya damammu,tana yin shigar da taga dama Malamin ya koma sha'awarta sabo da rashin Imani ya fara nemanta har ya dirka mata ciki,Kuma bayan zance ya fito yace karya take,naje unguwar lokacin wani uzuri ya kaini na harkar siyar da mota naji matasa suna labarin ance Malamin ma yace korarta zaiyi,Ni Kuma sai ta bani tausayi Naje nan ma nayi shishishigi nace cikina nane,dama Malam Yusuf mufita yake nema sai ya kebe dani gefe yace na aureta,yasan fa haramun ne amma ya aikata nace bazan aureta ba ya nace, to ni ba wani jajirtacce ba kawai nace a daura Allah ya yafe min,aka daura aure na tafi da ita gidana,Satin latifa biyu na saketa Kuma ban taba ma shiga dakinta ba,bayan ta haihu ta zabi suna da kanta aka sa miki Laila,bayan ta yaye ta barni ke ta Samu miji Isa na aurar da ita na mata komai,Laila kina zuwa Kuma ke sai da na miki aure muka je da Latifa wajen Malam lokacin cuta ta kamashi yaga mutuwa da wuri ya amsa cewar ke yarsa ce Kuma ya Sanarwa danginsa kaf suka yafi juna da kyar,amma iya mamanki kika sani kawai. Sai Kai Haidar tunda still ka girmi Annoor daga Laila sai Kai tsiranku ba yawa,Annoor yace nine karami ma kenan,yace kwarai kuwa,Abba yace mu aci gaba sauri muke ka tsaya surutu,Dan Allah Jauro mene haka haba komai sai kayi kunbiya kunbiya. Mummy kuwa ta Kai sati guda Baseeru kullum sai dai yazo ya kwashi harka ya fece,Hakan ba karamin Kona mata Rai yake ba kullum da karyar da yake shirgawa ko ruwanta baya sha,yau Mummy ta gama girki tace yau dole sai Baseeru yaci abincinta,tana kitchen ta bude abincin tana zuba Masa magani a ciki,me aikinta ashe tana labe tana kallo tana dauka a wayarta,Mummy Bata sani ba Baseeru ya hada baki da Yar aiki tuni ya biyata wasu kudi,ficewa tayi da sauri bayan ta gama dauka ta kira Baseeru a waya yace Mero ya akayi? Mero tana kasa da Murya tace shegiyar ta zuba Baseeru,dama kace yau zaka zo? Baseeru yace Mero Ina hanya ma tasan zanzo,Mero tace to wlh Yana nan flas ruwan hoda Alqur'an karka ci,billahillazi zata kaika kiyama Baseeru,aradu na Gani da idona,kwarankatsa dubu ta dakko he zubawa take he zubawa take yi a ciki,ai kuwa na dauka a waya hine nace bari na fada Maka,Baseeru yace Na'am Mero to he aka yi Yaya? shima yayi mata irin hausarta ya tsokaneta shi a dole wayayye,Mero tace hine hine nace uhmmm....Dama....ta rankwashi kanta tana sosawa taci gaba da magana Hine nace dama uhmmm...abin nan...abin Nan....................... Ina son Dan Hajiya Spark mijin wannan me kyau din, Ina gani suna zuwa tare wajen Mummy wallahi ni hi nake so,na fasa karbar kudin kayi min hanya ya Soni ya aureni wallahi Baseeru Ina sonsa tunda kaga Kai mijin uwarsa ne ko? Baseeru ya sheke da dariya yace Mero Ina laifin kice kina so na ai nine daidai ke,Mero tace cabdi jam hummm uhmm wallahi ni Spark nake so jikinsa me kyau so nake nima na dinga rungume hi,rannan matarsa haka ta dinga rungume hi suna ta wani umhmaahchacha da Baki yana tsotse mata kumatu na gani a Jikin mota suna ta yi,Nima ina son irinsa gahi Yana ta kamhi kullum wallahi Allah ni hi nake so,ko Kuma idan bazai so ni ba ai akwai kaninsa wannan yaron Arham ko Rafeeq Ina sonsu a bani Daya. Baseeru yace Misam fa tace kuturun Uba wallahi hima Ina sonsa na ma fi sonsa a kan Arham sabo da su suna da kudi,hi kuwa Arham din nan agogo ma siya Masa akeyi gahi ya dinga zazzago wandonsa duwawunsa a waje, Allah ya kiyaye amma ko hi na samu Ina so zan karba da hakuri,amma dai ni tsakani da Allah Spark nake so yafi kowa haduwa,Idan ya Kalli mutum sai naga wani tauraro a idonsa,rannan da yayi dariya Allah sai da nayi hawayen farin ciki sabo da kyau,nidai na rantse da Allah idan ban same hi ba zan fada kwalabati tunda gidan Nan babu rijiya. Kadan zan Baku tunda sharhi kadan ne suka yi jiya. In Baku Sharhi na daina yi da yawa wlh. AsmaBaffa [1/13, 9:42 PM] AsmaBaffa: TANTIRIYA A GIDAN YARI BOOK 2 ~YARAN JAURO~ 31-35 Official AsmaBaffa SADAUKARWA NE GA AIDA MAMAN TASNIM Page naki ne Maryam T Baliya Baseeru suna haka da Mero sai ga Spark yazo gidan a galleliyar motocinsa biyu tsala tsala bakake,yau harda escorts dinsa,motar aka bude masa ya fito sanye cikin kana nan kaya Yan ubansu kana gani kasan ba karya ne,zagawa yayi da kansa ya budewa Naila mota ta fito cikin Egyptian gown white me adon Maroon,ta Sha kyau matuka sai kamshi suke yi,hannunta daya ya rike dayan hannunsa Kuma rike da robar ruwan,suna tafiya a nutse,Naila tace sai na ganni na dawo Yar gajera a kan ka,yace ba dole ba Maza wasa ne,murmushi tayi,tace zan sha ruwan,Spark ya bude robar ya bata a baki ta Sha shima ya Sha suka yi gaba,Mero waya take amma tunda ta hango su ta kasa magana sai da Baseeru ya gaji ya kashe wayarsa. Mero ta zubawa Spark Ido kamar mayya suka zo suka wuce Mero,har sun wuce Spark yace wait ya dawo baya Inda Mero take, yace ke cire min abinda kika gani a jikina,kina ta kallo na,Naila ta karaso wajen tace mene ne? Yace yarinya sai kallo na take kamar taga namiji da nono a kirjinsa,Naila tace Mero ki kiyayi halaliyata, Mero bani da mutunci in na tashi yanka Miki rashin mutunci baza ki gane garinku ba wlh,Mero kawai kallon Spark take ta saki baki da hanci ta sa yatsa a baki tace yau naji dadi kayi min magana da kanka,dariya ta ba Spark Dan shi bai taba ganin kidahuma irin Mero ba. Naila wani haushi ya kamata sai Spark yayi murmushi ya juya zai tafi ,Hannun Naila ya jawo let's go,Naila ta dage ta tirje tace bazan tafi ba wlh sai ta fada min dalilin kallon mijina da take yi,ta Kama Mero da kokawa,Mero tafi Naila karfi sau dari,Mero zata tika Naila da kasa,Naila ta dinga kwalawa mijinta kira,Spark....Baby...kazo Spark dariya ta kamashi a duniya ya Dade bai ga marar karfi irin Naila ba,tana cewa zan fadi Spark...Mero tace ni banyi kokawa dake ba amma ai ya halatta mutum ya kare kansa, kare kaina nake yi,Mima ce tazo gidan itama driver ya kawota. Mero ta gani tana kokawa da Naila, Spark Yana ta dariya Dan Naila itace ta Kai kanta dariya abin ya bashi wai a haka fada suke yi,gashi wani dadi yake ji Naila na fada a kansa,ya gyara tsaiwa yace duk a kaina ni kam,Mima tana zuwa ta dakawa Mero tsawa tace Dan uwarki da matar Dan masu gida kike kokawa,Mero tace ni kare kaina nake yasin alqur'an itace ta kamani da kokawa hine ni Kuma....Mima ta zubawa Mero Mari har biyu,tace baki da hankali Yar kauyen inace ke,Spark ne yayi magana yace a'a Mima please mu muka kulata fa wlh Dan Allah ki daina itama mutum ce kamar kowa Kuma tana da yanci, bai kamata ba ai ba baiwa bace,Naila ta kumbura ta cika fam wucewa tayi zata yi kuka ta shige ciki wajen Mummy ta zauna tana kuka,Mummy da fitowarta kenan daga bedroom tace ke lafiya sakinki yayi na fara tikar rawa ko kuwa? Naila tace yana waje shi da Mero tace tana sonsa shine yaji dadi dama ashe yana sonta har dukana tayi,. Mummy tace Kai nidai Mero ta dameni haka Misam yazo ta dinga kallonsa tana cizon yatsa yar iskar yarinya me Spark zaici da ita wannan kazama,ko girki bana sata sabo da kazantar Mero,tab lallai Mero ta girma matar Spark din zata taba,Naila tace wlh har da dukana,su Mummy haka suke matukar ka shiga cikinsu ka hada alaka dasu ko basa sonka to wani bai Isa ya takaka ba indai ba a family yake ba,son kai ne da su sosai,Ina Mero tazo ta koma kauye gidan Ubanta na koreta Cewar mummy. Mima dake tsaye tare da danta suna hira tace mene amfanin Mero a gidan nan gata kazama ga rashin kunya,Mero tazo wajen Mummy ta zube a kasa tana kuka ayi hakuri Mummy tace wlh sai kin tafi ai ba gidan ubanki bane ko kina da gado ne,ki Kalli yarinya kalar Madara kice zaki kokawa da ita,matar dana, baki da hankali Mero,Mero a kasa ta zube tana rokon Mummy tace wlh ban karawa dama son hi nake hine nake kallonsa Yana birgeni,Mummy ta taso da ihu kan Mero Spark ya shugo yace Dan Allah ku rabu da ita sai kace yara Kuna yin wani Abu,Mero na gode da Kauna kinji amma ni ki daina Sona baza ki samu ba,babu wani aure da zanyi kinji,Mero taji dadi tace na gode wallahi, yasin Allah ya baka abinda kake nema duniya da lahira kafi kowa hankali a danginku,Mima tace harda mu kenan ya fi mu wato so kike ki fada mana bamu da hankali? Mero tace a'a amma dai...Kuma...Kuma.....ai...dai....kai yafi kowa hankali na fada da gaske,Mummy tace ni na Raine
Chapter 25 · 0% Book details