← Book details Tantiriya A Gidan Yari Book 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 87

Sashe 24

Tantiriya A Gidan Yari Book 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

da kamarta suma basu da kamarta itace duk taci Kashi da fitsarinsu har suka kawo haka,Habiba tana da Sanyi bata da zafi bata iya fada ba shi yasa take kyale su in tace su bari sai dai tace Allah ya shirya haka take Kuma Allah ya shirya tunda aka tsaya a iya haka. Abba yace madalla ayi a Fadi gaskiya ni Ina sauraro,Jauro yace ah ko Kaine dai aka sameka ta haka ai iya damuwar da zaka yi kenan, Hashimu ka isheni fa,wai sanda na samo su kana nan ne,Abba yace yanzu mun hadu Ina nan kayi bayani sauri muke,nazo gidan Nan a sa'a yau Inama ma sunana Sa'adu sabo da Sa'a ta. Jauro yace Kun riga Kun san sunana Kun San asalina da iyayena,muna zuwa kauye da ku,amma zaku ga tunda kuka fara wayo ban sake kaiku kauye ba,nayi hakane sabo da gudun kar Yan uwana ko wasu a gari su fada muku ko ayi muku gori,shi yasa tun Kuna yara rabon da ace kunje kauye ku mazan kenan matan ma basu taba zuwa ba dan ban bari sunje ba,kunyi kunyi har kuka hakura,sannan ko mazan ma bana yarda su kwana tare muke zuwa mu dawo tare,haka a kauyen ma bana bari su fita ko kafar gida daga gida sai mota duk ba komai bane sai wannan dalilin. Sannan zaku ga bama zama a gari daya, Kun sani farko a Katsina muka zauna,muka koma Jibgawa,na dawo da ku Minna yanzu muka dawo Kano,bana so a San wani Abu a gari bare ma Yan unguwa suyi muku gori shi yasa ban bari mun ta zama a wajen Daya ba tunda Kun sani Allah ya azurtani Kuma Kuma kowa na bashi Ilimi boko Dana addini sannan Kuna da aikin yi ai Alhmdllh. Farko gata Ummin ku Habiba ita na fara aure Kun sani tunda na aureta ban taba haihuwa ba gashi Allah ya sa min masifar son yara,Ina so ace yau ga wannan a karkashi na suke amma Allah bai bani ba,dangina kaf sun tsani Habiba akan cewar itace juya Bata haihuwa,ba zagi da wulakancin da basu yiwa Habiba ba tun Ina kauye lokacin bani da kudi har Allah ya azurtani na dawo da ita birni. Iyayena sun tsani Habiba har cewa suke lallai sai na saketa ko na Kara aure,Hakan yasa tace na rufa mata asiri na Kara auren kawai ko ta huta da gori,ana haka na auri matata ta biyu,itama shuru shuru bata haihu ba tace baza ta zauna ba haka na sallameta, tana tafiya ta auri wani ta samu ciki ta haihu yanzu yaranta shida Kunga ya tabbata daga ni ne rashin Haihuwa,haka na sake auren wata itama ta dinga yi min wulakanci iri iri ko Shekara bata yi ba na saketa taje ta auri wani itama tana na n da yaranta yanzu ta haihu. Na sake auren wata wannan kuwa kullum a zagina take juya marar haihuwa,taimakonka nayi Dana aureka,babu masifa kamar ace mace ta dinga ganin dan ta auri mijinta ma taimakonsa tayi ya shiga uku,ta zageni babu irin cin mutuncin da bata min ba,rabuwar mu da ita shine zagin Habiba da tayi,babu wacce ta isa na aureta ta zagi Habiba na kyaleta,sabo da Habiba nayi nayi akan ta amince na saketa taje ta auri wani ta haihu taki yarda,tace tsakani da Allah take so na, rashin Haihuwa bazai sa ta juya min baya ba,Habiba matar rufin asiri ce,ta karbeni a duk yanayin da nake ciki,talauci,arziki ga rashin Haihuwa duk tana zaune dani,sannan na Tara mata yara ta rike min Kuma bata taba musu kallon banza ba bare gori,ta rike kowa kamar ita ta haife shi. Abba yace Dan Allah tsaya Jauro bakina Yana kaikayi,Jauro yace Ina ji sarkin shishigi,Abba yace Kuma duk Habiba adalcin da ta Maka baka hakura da yi mata kishiya ba ka Kara auren Na'ima? Allah ya rubuta min ya zanyi,Kuma idan namiji ya Saba da mata biyu baya iya hakura,idan Allah yayi zan Kara idan Allah baiyi ba Habiba for ever Habiba for life inji bature,Habiba harda Jin dadi ta gyara zamanta. Jauro yace lokacin da na bar kauye na koma katsina muna zaune akwai wata yarinya me suna Asiya a makwaftanmu,tana yawan zuwa gidana jininsu ya hadu da Habiba,kullum in ta dawo daga tallan gyada to tana gidana,Iyayen Asiya wasu masu mugun son Abin duniya ne duk da basu da kudi amma wai Asiya da tallan gyada zata ciyar da su,gyadar da gaba daya bata fita dubu daya ba a lokacin wai da gyada zasu ci su Sha,Kuskuren iyaye kenan wasu,Babar Asiya a lokacin tace indai Asiya Bata yi tallan gyada ba to baza ta samu kayan daki ba idan aurenta yazo,sannan bata kauna Asiya ta dawo mata da gyada ba tare da ta siyar da ita ba. Asiya suka takurawa da uban tallan gyada ba dare ba rana,daga nan Kuma suka koma yi mata funkaso da Miya tana kaiwa tasha,to Kun San dai Tasha tana da shugaban ko,to shugaban tasha a katsina wani me Suna Zubairu Dan yayi shi yaga Asiya yace yana sonta,Asiya yarinyar kirki ce wlh me addini da hankali,ta fada son Sarkin Tasha Zubairu Danyayi,shima da gaske aurenta zaiyi suna soyayyar su me tsafta,to gaskiya Zubairu Dan shaye shaye ne shi sosai, sai iyayen Asiya suka ce Sam baza su bashi yarsu ba,har yayi alkawarin in ta aure shi zai daina shaye shaye sabo da son da yakewa Asiya,amma suka ki yarda,Asiya tayi kuka sosai,Baban Asiya sai ya samo mata wani Dattijon mutum tsoho zai mata auren dole,Zubairu Dan yayi sai ya sace Asiya suka gudu,sai bayan watanni biyar Asiya ta dawo gida da ciki kato. Babanta suka mata dukan tsiya suna tambaya waye ya yi mata ? tace gida ,zubairu ya kama musu a Zaria suka zauna abinsu,tace wallahi Kuma akasi aka samu sau uku kacal ya taba amfani da ita duk wannan watanni da suka kwashe,Kuma duk da tana da cikin itace ta gudo amma Zubairu Yana son abarsa. Ya dawo Yace ai Yana sani suka yi haka so suke dole sai an bashi Asiya,Asiya tace nice nan nace yayi min ciki idan aka ganni da ciki dole a daura mana aure, shi kuwa Zubairu ya Shole abinsa,ni kuwa lokacin naji labarin Asiya,iyayenta sun koreta,ni da Habiba muka fita neman Asiya muka sameta a kasuwa take kwana tana tashi ga ciki,ta bani tausayi ace ga ciki mace ta dinga kwana a rumfar kasuwa kamar mahaukaciya sai na dakko Asiya na dawo da ita gidana,tayi zamanta muna kula da ita,Bata da matsalar ci da Sha da sutura har tazo haihuwa na kaita asibiti ta haifo Danta namiji santalele. Na Nemo Zubairu yazo ya dauki dansa yayi Masa Addua Yana ta kuka sosai,a wajen nace Dan Allah ni idan ta yaye Dan Ina so,Asiya da sauri tace mun bar Maka sabo da suna gudun abin kunya. A nan dai ranar suna yaro yaci Suna Sajid na yanka raguna har biyu,duk wani kayan barka na jariri nayi,muna zaune abinmu da Asiya,lokacin na samu iyayenta suka yafe mata sannan suka amince zasu aurawa Zubairu ita,bayan ta yaye jariri aka daura mata aure da Danyayin ta,ya gina musu gida me kyau aka Kai Masa Amarya Kuma a dalilinta wallahi ya daina shaye shaye ya shiryu suna zaman su lafiya da yaransu uku Yasmin,Mufeed da Aryan sai kai Sajid babba,Na sha kaika Kuma kana zuwa da kanka amma tunaninka Zubairu ba mahaifinka bane kawai na auri Asiya na saketa Zubairu ya aura, to kaji daga yau Zubairu shine mahaifinka,Kuma Ina so ka sani kaddara ce babu ta Inda bata zuwarwa mutum,Dan Adam bashi da wayo ko dabara,Iyayenka sunyi kuskure na biyewa son zuciya,Asiya kuruciya da giyar so ce ta kwashe ta,Zubairu Kuma yayi ganganci ya biyewa zuciya,wannan ba wani Abu bane akwai ciwo dole amma ai baza ka kashe kanka ba,ka fawwalawa Allah. Daga Kai sai Sajid ana yayeka sai Nabeel,watarana akan harkar sufuri na naje Jigawa birnin kudu,Ina mota Ina tafiya wata yarinya budurwa tana ta gudu a titi da sassafe fara ce tas Yar Fulani jikinta furu furu,tana ihu tana a taimaketa da sauri na tsaya tazo ta fada motata tana haki lokacin ban tambayeta komai ba sai da ta huta sannan nayi parking nace wacece ke? tace sunanta Sa'ade ita Yar asalin jigawa ce Birnin kudu,marainiya ce iyayenta sun rasu a hannun kanin Ubanta take,tace wani ne yake sonta sunansa Suffiyan akan bata sonsa ya saceta ya boyeta a wani gida a jigawa dutse kwananta ashirin kullum sai yayi amfani da ita har Allah yasa yau ya manta kofa a bude ta fito ta gudo shine tace na taimaka mata,har gidansu na mayar da ita,amma a lokacin Dake Suffiyan me kudi ne Wanda ke rike Sa'ade kanin Ubanta sai yace karya take yi ya zaneta yace karuwanci ta tafi dama,ai shi dama Suffiyan ya fada Masa tana zuwa gidansa,bayan na tafi da wata biyu ciki ya bayyana a Jikin Sa'ade,Kanin Ubanta yace karya take Suffiyan bazai lalata ta ba,shi da matarsa suka dinga gana mata azaba har watarana lokacin cikin ya gima ta kusa haihuwa naje garin na nemi gidan su Sa'ade,Ina zuwa naga ana dukanta ga tsohon ciki tana ta kuka na karasa nace cikina nane ni nayi cikin Ina son abina,ita kanta tayi mamaki amma na dage nace cikina nane,a garin sai da aka cika ana kallona ana tsine min,Kanin Ubanta yace to wallahi sai an daura min aure da ita,akace haramun ne aure da ciki nace ba komai a daura Na bada sadaki aka daura na taho da ita gida,tun a mota na saketa nace ba aure tsakaninmu,itama taji dadi. Haka na kawota itama suka zauna tare da Habiba ta kula da ita har ta haifo Danta santalele kyakyawa gashi nan ranar suna na yanka Masa rago, na rada Masa Nabeel,kayi hakuri Nabeela kai rago daya na yanka Maka. Haka na dinga sintiri da Sa'ade muna neman Suffiyan Wanda ya mata ciki Allah ya taimake mu muka same shi kuma Nabeel sak mahaifinka kayi a kamanni kyakyawa ne amma sai ka dakko Dan hasken mamanka ka sirka da duhun ubanka sai ka zama ruwa biyu ga ka nan rass da Kai,Kuma Alhmdllh da muka je ya karba domin lokacin yayi nadamar Halayensa ya nemi yafiyar Sa'ade ta yafe Masa,haka kanin Ubanta suka daidaita ya
Chapter 24 · 0% Book details