Sashe 38
Tantiriya A Gidan Yari Book 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ko ba kalau yake ba,dawowa farko yayi yaga yanda aka fara hasko su a zaune suna Shan Ice cream,Nan take ya tuna ranar,yaga hotel din tabbas ranar da Iman Bata kwana a gida bane an mata fyade. Yace Innalillahi wa innailayhirrajun ya akayi to ban sani ba ban San nayi ba? Salati ya dinga yi ya ajiye wayar tare da zuba tagumi,tashi yayi ya mike kawai ya ajiye aikin ya fito cike da tsananin damuwa,gida ya nufa Wanda bangaren Yan gida ma kowa ya gani,Iman tana kwance tana chating sakon ya fado wayarta,tana dubawa ta sake kalla wayar tayi jifa da ita tasa hannu a baki sai kuka. Jikinta na rawa ta fito Palo kenan Jauro ya shugo Wanda shima ya kalla,yace ta faru ta kare munafukai Allah ya tonu asirinku,Ashe abinda kike yi kenan,kunci amanata ba a Dan iskan namiji sai mace, da ace baki bada kanki ba bazai taba ko gwadawa ba Iman,kanku kuka yiwa ba ruwan Jauro wlh. Haidar ne ya shugo shima ya gani takaici yasa ya dawo gida ya zaci shi kadai ya gani,Shima Nabeel fitowa yayi Yana dakinsa yau Bai fita ba tunda yaji tarihinsa ya daina sukuni,matan ma duk fitowa suka yi,Rahma da Nabeela,Sajid Yana gani ya goge shi gaba daya a wayarsa,Laila da Karima ma duk gogewa suka yi daga wayarsu suna gidan auren su. Hashimu ne ya shugo ya tsinci labarin yace mu Gani nima,Jauro yace tsaraici ne babu kyan Gani ni na goge ma,Habiba tace abi a sannu ba lallai ace....Abba ne yace yi mana shuru ai ke dama Sailuba ce ko me aka yi dai dai ne,Abba ya shako Annoor yace Dan ubanka tsaya a nan tsakiya mu saka a tsakiya Kai wanne irin Dan duniya ne Kaine Dan Sunna amma sai aka samu abin kunya a wajenka,ya Kalli Iman yace ba banza ba Ashe kike makale Masa ashe da abinda yake baki a sirri. Annoor jajayen lips dinsa ya turo yace nifa ba abinda nayi ban San komai ba,yes Ina son Iman amma bazan taba lalata ba wlh, ni da ace ni dan Kwalta ne ko me mata hudu bazai fada min wankan tsarki ba indai akan Iman ne amma ta ya zan mata haka da hankalina,Jauro yace dan ubanka wannan waye idan ba kai ba? Annoor yace gunki nane amma ba ni bane,ka zauna kana tabe yarinya kana shanye mata kirji kace ba Kai bane,Annoor yace ai Kuma Kawu yafi na sha Wiwi,da mutum ya Sha Wiwi gwara ya sha nonon mace,Abba ne yayi sauri ya toshe kunnensa da hannunsa ya juya wajen Jauro,Jauro shi Kuma Gani yayi Annoor Kuma da gaskiyarsa a nan,Abba yayiwa rada yace kaga Kuma da mutum ya Sha Wiwi gwara nonon matarsa ko ya kace,Abba yace na Dade da sanin haka,yaran nan na yanzu da iya magana suke,Jauro yace muci gaba da yi musu fada,radar suka daina Jauro yace koma me kayi Kaine zaka aureta sai ka karasa ragowarka da ka rage,Abba yace shine magana itama Yar banza fitsararriya ai da Gani zata aikata itace ta bashi dama azzaniyatu kawai,Iman tana kuka tace wlh ban San komai ba fyade yayi min bana kaunarsa bana sonsa ko an aura min shi ya hadu da masifa da bala'i,Annoor yace ni ance miki sonki nake ko ni ruwan Sanyi ne zaki Raina min hankali ko nasan na yi wani abu Dake,wlh ka sani Allah ya is....kafin ta karasa Kawu ya sharara mata Mari,yace ya girme ki kice zaki zage shi,wa yace ki bashi hadin Kai kece babbar marar kunya ai,Annoor harda fari da Ido ya Kalli Iman,Abba yace baka kyauta ba Jauro shima a mare shi ai shine Jagora,wlh sai an mare shi ya kamo kunnen Annoor Yana cewa ya lalata yarinya marainiya ga halin da take ciki Kuma ka mare ta,Jauro yace na tsani rashin kunya ni bana son yaro ya raina babba,wlh ni na rike ku ba Wanda ya isa na sa doka ya tsallaka,na Sha fada miki bana son rashin kunya shi zaki zaga,Bai girme ki ba? bana fada muku cewar za a iya wasa da dariya amma banda Raina babba bare ki zage shi,tare kuka yi iskancinku ki dawo Kuma kina shirme,ko bakya so sai kin aure shi,shine ma gatanki ki sani,yasan asalinki kin San asalinsa sannan ga abinda ya faru a tsakaninku wa kike nufi zai rufa miki asiri idan ba shi ba. Iman tayi tsaye Sororo tace ai shine ya min fyade shi yasa ya min dinki ya bani kwayar Hana daukan ciki sabo da yasan ya cuceniiii....ta karasa da kuka,Habiba tace na yarda dake Iman sabo da Sanda ake duba ki ya zaci ciki ne Dake har da suma Yana gudun abin kunya,Jauro sai lokacin ya tuna da abinda ya faru a baya,yace biri yayi kama da mutum,Abba yace na dawo bayanki Iman Kai Annoor jakar ubanka lalatacce,Jauro ma yace mun gane gaskiya Iman kece da gaskiya. Annoor yace amma Abba ku tuna fa wlh ban sani ba ta ya akayi idan Ina nemanta ban San tayi ciki ba,ta ya Ina Likita zance a duba ta ai baza kuji labarin ba ma,Abba ya sake daga kai sama Yana tunani yace kafi Iman gaskiya Annoor,Jauro yace ni dai Ina bayan Iman,Abba yace na zabi Annoor,Habiba tace Dan Allah wannan abin nasu fa bincike ya kamata ayi da alama basu San sunyi ba,sannan a duba waye ya turo sakon,a tsaya ayi Duba da bincike,amma ku kanku an kasa gane me gaskiya a ciki,kuce Kuna bayan wannan anjima ku koma bayan wannan ba shine ba,Abba yace to gwana ta gwanaye.. Nabeel yace gaskiya ne Ummi ni na yarda dukkansu baza su aikata ba,kowa yayi hakuri a dauka kaddara ce ayi musu aure a hankali ma gaskiya zata yi halinta,Allah baya bacci. Rahma headphone dinta ta gyara tace mu akewa kallon Yan iska sai gashi,Yaya Annoor har baya so Iman ta zauna da kayan bacci a gidan nan ana tattalinta,gashi ashe mu namu me sauki ne, Allah ya bayyana gaskiya amma tunda aure zaku yi ai normal ne,Nabeela tace gaskiya wlh da matsala ayi bincike sosai,Rahma tace Yaya Annoor har duka ne yake idan ya ganni da wani Ashe shima Yana dan ehhh ehh...Jauro ya galla mata harara tayi shuru. Haidar yana jinsu baiyi magana ba sai daga baya yace Annoor an Sha dadi shike nan gori ya kare,Iman ta huta da gori,inji wa yace gori ya kare?Annoor ya tambaya ai magani ta bani tayi min fyade Kuma sai an biya ni Sperm dina da aka sa nayi asarar 'ya'ya na a banza, an zalunce ni an yi min fyade sannan abin haushin ma bana hayyacina,ban San nayi ba wannan shine ya dame ni wlh ni,tunda an riga anyi ai aji dadin kawai amma kawai an zalunceni ban sani ba ai sai naji dadin sannan a tuhume ni da kyau. Abba a hankali yanda ba me Jin me yace yace Dan Nan kayi gaskiya gwara kaji kasan ma kayi amma baka sani ba ai an cuce ka,ai baza ka ji haushi ba sai kayi aure kaji abinda ake ji sannan zaka tsinewa kanka da kayi baka hayyacinka, baka san kayi ba,ni kaina na jiye Maka haushi irin wannan yarinya dakwalwa haka ace baka ji ba ai ka cutu. Jauro ne yace me kake cewa ne wai? Abba yace ba komai dama cewa nayi gwara ma da ya sani Yana hayyacinsa,Jauro dariya ya danne ya fada tunani shima yace Annoor fa an cuce shi magana ta Allah gwara da yaji dadin ma amma bai sani ba. A fili Jauro yace Annoor wato Kai haushi kake ji ma baka hayyacinka? Annoor yace wlh Kawu shine abinda ya dameni ba wani abu ba,tunda kaddara ta faru ya za ayi sai hakuri amma naji abin,a fada mata kawai tayi hakuri ban San komai ba ni kar ta sake tuhuma ta,Dan ni ya dace a lallasa an bata min rai,Haidar Yana ta dariya yace yaro dan ma baka sani ba da kuka zaka yi kawai kace an cuceka,Abba yace Kai kuyi mana shuru da zancen batsa,Iman kuka bazai kaiki ba,sannan Baki da kamar Annoor gwara ma a tattara ayi hakuri kinji,kiyi hakuri magana ta gaskiya ba a kyauta miki ba,shima Bai sani ba,ba a kyauta Masa ba, da ace dai ya sani da yafi din,kiyi hakuri maganar iyaye kina da Kawu sannan baku San dadin iyaye ba me zai dame ku,kawai kiyi aurenki ku dora daga Inda kuka tsaya,Jauro shima yace yo shike nan mece duniyar daga Kano sai kaduna fa,rayuwa hakuri akeyi kowa ba yanda yake so aka tsara Masa ba, inshaallah zan kaiki wajen Mamanki ki ganta,Iman murmushi tayi taji dadi tace Allah Kawu? yace sosai kuwa,tace na gode yace kiyi hakuri kinji ko ma mene a rufawa juna asiri,bana son rashin kunya da shirme,kar kice wannan zai sa ki daina ganin girman Annoor dan kin ganshi ba wando,Haidar dariya suka yi su Jauro abinsu sai addua ko a gaban waye fada suke idan magana ta zo,Abba yace kowa ya goge video din Nan,suka goge,Abba yace ke Rahma ban yarda dake ba muga wayarki karki dinga kallon bawan Allah cikin dare kina rage zafi,Dariya Rahma tayi ba shiri tace wlh na goge ai har abada yayana ne baza mu so mutuncinsa ya tabu ba,Jauro yace yawwa Allah ya muku Albarka,suka ce Ameen. Annoor juyawa yayi ya haura sama yace mutum ya Sha aiki bai sani ba Allah ya isa wlh da banji dadin ba,gefen bed dinsa ya zauna Yana tunano Badon Iman da ya dinke yace nine nayi wai? Kansa ya bawa amsa yace Kaine mana,yace Ashe gwarzo ne ni murmushi ya saki,yace taji Mazaaaa...kyawawan hakoransa suka bayyana,yace Alhmdllh da ba wani Jaki bane,yanzu hankalina ya kwanta haba ai gwara ace nine dama,ni tunda naga wajen nan na Iman da na dinke naga yayi kama da Lolly dita,kamar size dina ne ya shiga ciki,nace ikon Allah kamar ni ashe kuwa nine,murmushi ya saki Haidar ne ya shugo ya same shi a haka,dariya ya bawa Haidar sosai yace Kai nan murna kake yi ma kayi iskanci bayan baka sani ba,ni fa yanzu na samu nutsuwa Kuma da ace wani ne yayi gwara ni,ayi ma ayi bikin Nan wai me ake jira ne? ayi mana auren nan Dan Allah ko na dinga kashe fitila cikin dare. Iman