Sashe 35
Tantiriya A Gidan Yari Book 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
matan ke ci da kansu suna yan sana'o'i, ko shugowa mutum yayi suna bin hannunsa da kallo ko zasu samu na ci, Ikhram itace ma idan ta samo kudinta a gidan suke karewa kawai taimaka musu take yi badan halin Iyayensu ba sai dan Allah da tausayin yaran. Wanka tayi ta fito,Uncle Yana zaune Yana danna waya a dakin Asabe,yace wanka aka yi? yawwa ko kefa Maza ki shirya,idan aka yi kwalliya ai anfi cin kudin mu,mu Maza ai sai da gayu,wacce bata gayu zata hadu da wulakancin samari kuwa ,Dan Allah ki bashi hadin Kai ko me yake so ki samu ki yago mana rabon mu,ki rama min yanda mata suke cinye min kudi nima ki ciyo kudin wasu Kinga kin rama min. Ikhram tace ba Dan iska bane fa shi,,yace wato nine dan iska? haba Ikhram karki raina min hankali budurwa dake haka kyakyawa me farin jini kice ba a yin komai da ke ai bazan yarda ba,yanzu yan mata duk haka suke,Asabe tace mu take rainawa hankali wai ita ta gari ta gama raba shi ga Maza ta dawo tace daga wa'azi take,Ikhram tana jinsu kayanta ta eba Wanda zata saka ta bar dakin Asabe ta koma na Amarya Rakiya,a can ta Shafa manta da turarukanta sabo da tana siyar da su,wani Leshi ta dakko me tsada ne dark blue and Golden,sai mayafi, jaka da takalmi golden ne, ita dama Ikhram idan ta samu kudi Bata dinka kaya me araha,sai ta dan dade bata yi dinki ba amma in ta samu zata yi sai me tsada,shi yasa zaka dinga ganinta kamar Yar wani duk ranar da bata sa Hijab ba,riga da skirt ne, Yar kwalliyarta tayi sama sama tayi kyau sosai ta fito da kyar take tafiya sabo da yunwa ta gama da ita sai ruwa take sha kawai. Dakin Stella ta shiga Inda Rafeeq yake,Yana kwance a gefen katifar Stella Yana latsa waya Ikhram ta shigo bai taba ganinta a haka ba daga hijab sai kananan kaya,kinyi kyau ya furta Yana kare mata kallo kamar maye,tace na gode, gashi bata cikin nutsuwa sabo da yunwa, tashi yayi yace muje Yana jiranmu kin San gari zaki iya nuna min hanya na karbi motar? tace ae na sani kace ya tafi sai ya bar motar kayi driving,suna fita ya sallami driver ya karbi key,gaba ta shiga ya ja mota suka tafi,yace shopping mall,sai ta nuna Masa Sahad store,a Nan yayi parking ya fito suka shiga. Yace to Malama zabi abinda kike bukata,Ikhram a ranta tace gwara a bani dafaffen abinci naci akan komai ko na samu sauki" ko magana ta kasa sosai sabo da yunwa,yace wai ya na ganki shuru shuru ne? tace ba komai wlh tana murmushin dole,ta fara zabar abinda zata iya saukar bakonta da shi,ta dauki Indomie Eggs,su Lipton,Madara Milo sugar,duk wani Abu na dafawa, na ci shi ta dauka bata dauki komai ba sai iya su,ta dauki wata Rice ta Yar Leda guda uku,ta gama yace Banga bread ba?,maganarta a sanyaye sabo da yunwa tace ba a nan zamu siya ba muje Oasis,yaje ya biya kudi suka kwashi kayan suka zuba a mota sannan suka wuce Oasis nan ma ta dauki bread manya biyu ta dauki wasu snacks din,ta dakko yogurt da lemuka da ruwan roba ta dakko Ice cream ya biya suka fito,tana shiga mota ta bude wani cake tana Sha da lemo ko kula Rafeeq bata yi ta cikinta take yi,kamar wani zai kwace haka take ci. Joint na siyar da kaji gasassu ya tambaya ta nuna Masa Yahuza suya Suka je ya siyo musu har Leda uku,fura ya siyo suka wuce gida suka koma gida Inda yace driver ya jira shi, a Nan ya bashi motar yace ya tafi da ita gobe zai kira shi,Ledojin suka shigar ciki duk iya Wanda Ikhram tasan zata yi amfani da su a dakin Stella ta bar kayan sauran ta kaiwa su Asabe har da kajinsu na Yahuza suya,Uncle sai washe baki yake yace ko ke fa,ai Kinga yanda ake harka,da kin zauna shirme,ai haka nake kashewa mata kudi gashi ko yanzu kin rama min,ba karamin cin kudina Yan mata suke ba, Alhmdllh kina ta rama min Ikhram nima kina ciyo na wasu,Asabe ta kalle shi tace kayi asara kar dai ka kwaso mana kanjamau, Ikhram ficewa tayi ta koma wajen Rafeeq dinta. Rafeeq ya zaro 2k ya Bata yace je ki siyo min doyar nan taku naci naji irinta,ai ta 2k tayi yawa yace kije dai ki siyo wacce ta dace ki rike canjin,Ikhram tace taso muje tare mana ai kaga gari,yace jeki dai ki dawo fitowa tayi itama ta aiki yaro ta dawo wajensa,tace me zan fada maka? yace karki damu a siyo doya da kwai,ga nama ga yogurt,lemo,snacks Ina zamu Kai abinci,tace to shike nan,yaron bai dade ba ya kawo doya da zafinta suka zauna tare da baje komai suna ci. Rafeeq satar kallon Ikhram yayi tana ta cin abinta ba wasa ko kulashi bata yi" Sam bata magana,da alama a yunwace take,cikinta Yana fara cika tace Kai kazar ma wata dusa dusa ko? bayan duk ta cinye ta,Rafeeq yace lallai kin koshi da yawa,sai da kika cinye zaki ce kazar Dusa, yogurt ta bude tana korawa tace Kaza bata dame ni ba,nafi son tsire,dariya Rafeeq yayi yace a hakan? duk kin cinye ni ban ci ba,Ikhram ba kunya tace ka bari idan Allah yasa na aureka ka Sha a nono,Rafeeq zama ya gyara Jin anyi zancen da yafi so,yace Allah? tace da gaske tace ka bari ayi aure ka gani in saka a lungu,dariya ce ta kama shi wai shi bai ce zai sata a lungu ba sai ita. Ta kora lemo ta sha ruwa sannan tace Alhmdllh Kai yunwa bala'i ce, yanzu sai ayi wacce duk za ayi,cinyar Rafeeq ta buga kadan tace to ya Abuja dan duniya? Rafeeq shuru yayi Yana kallonta tace mene ne tana dariya cike da nishadi,yace dazu naga ko magana bakya yi na zaci ma ko baki ji dadin zuwan nawa ba,Ikhram tace wlh babu Wanda naji dadin zuwansa irinka,kayi kyau sosai Friend,hannu ya mika mata itama ta mika Masa nata suka tafa,yace yau wai ya banji kalkala bane ba wa'azi bane? Ikhram tace wanne wa'azi hmm dama neman kudi ne kawai ni ba Malama bace, yace inane dakinki a gidan nan ki nuna min? Tace ya kamata dai na baka tarihina,yace Ina jinki" Sunana Ikhram Tahir, asalin Babana Yan Gombe ne,Mahaifiyata ma Hauwa'u yar Gombe ce,Babana Tahir su biyu Iyayensu suka Haifa Tahir da Rumanatu,Rumanatu ita tunda tayi aure ta haifi Danta Yahuza Wanda ake kira yanzu da Yahuza Donation, bata dade ba ta rasu,shi Kuma Tahir Abbana ya dauki Yahuza ya kaishi hannun matarsa ta farko wacce ita bata taba haihuwa ba, Allah ne ya azurta Tahir ya zama hamshakin me kudi ya koma Abuja da zama,suna rayuwa,sai da aka dauki lokaci sannan ya dawo Kano Yana Business,Yana da shaguna a Kasuwar Sabon gari. Har Yahuza ya cika 25yrs sannan Babana ya auri matarsa ta biyu Hauwa'u itama Yar uwarsa ce suna da alaka,matarsa ta farko ganin bata haihu ba gashi an Kara mata kishiya sai ta fita ta auri wani,ita Kuma Hauwa bata Dade ba ta samu ciki,Tahir Yana da cuta ba a sani watarana sai kawai ya fara ciwon ciki,Hauwa tana kitchen Bata sani ba ma ashe ya mutu a daki ba Wanda ya sani. Sai da ta shiga daki ta iske gawar sa ta fito tana kuka ta kira mutane, Yan uwansa suna zuwa suka ce itace ta kashe shi,suka kaita Kara kotu,lokacin sun dauki azzalumin lauya haka babu binciken kirki aka yanke mata hukuncin daurin rai da rai a matsayin ta kashe mijinta ta hanyar sa Masa guba,layin masu ciki aka kaita a gidan yari dake Kano,tun Yan uwa suna zuwa wajenta har suka daina sai dai a turo mata Dan abinda ya samu. Kasan Mamata tana da Yaya kafin ma ayi mata aure to yayarta itace aka kaita Abuja aikatau me gidan yayi mata ciki,ta dawo dangi suka ki karbarta wani bawan Allah ance wai ya dauke ta ya riketa, ta haihu a wajensa ance dai wai namiji ta Haifa sunansa Haidar,Kuma wai a hannun me kudi yake wani Dan Fulani,wlh tana kasar waje bata San na fito ba,nayi nayi Uncle ya kirata ko ya bani number dinta yace baida ita babu Wanda yake da number dinta a gombe sabo da korar ta suka yi sanda tana da ciki,da itace nasan zata rike ni,Kai Ina so ma naga dan nata cousin dina Haidar,ance yanzu ya Kai 30yrs. To Mamata Hauwa a can ta haifi yarta Mace taci suna Ikhram, haka muka taso da ita a gidan yari ban San kowa nawa ba har na Kai Shekara Sha biyar sannan ta kamu da lalurar ciwon sugar, lokaci daya ta rasu a cikin gidan yarin,aka barni ni kadai,lokacin ma'aikata sun Sha furta za a fitar dani a kaini wajen dangi itace ta hana tun tana da rai. Sai da na cika shekaru 17 cif sannan Yahuza Donation yazo ganina duk wannan lokacin me tsawo,bayan Babana shine ya rike shi ya girma ya mutu, Kuma duk dukiyar Mahaifina ko Daya dangi basu raba gado ba, kwandala ba a bani ba,Yahuza ne ya cinye ya dinga neman mata da iskanci iri iri a haka ya lalata dukiyar,komai ya kare karshe ya dawo gidan haya da matan da ya aura. Ko da yazo shi yayi komai aka fitar da ni ya kaini Gombe wajen dangin Ubana, tunda naje can suka kasa rikeni suna wulakantani,komai na samu su kwace basa so naci gaba ma,wannan yasa na dawo wajen Yahuza Donation,shi Kuma bazai Kore ni ba amma akwai wulakanci shi da matansa,sisinsa baza a ci ba amma Yana son a bashi na wani. Yahuza Dan bariki ne Manemin mata Yana caca Yana Shan giya,har asibiti yake zuwa ya Bada jininsa a eba a biya shi kudi yazo ya nemi mata,sabo da haka aka sa Masa suna Yahuza Donation yanda yake donating Blood ana biyansa" Yana da shagon siyar da lemuka amma duk ribar a wajen bariki take karewa da caca,baya iya ciyar da iyalansa bare sauran bukatun ganin na dawo hannunsa ya daina komai,yaransa ma duk makarantar gomnati suke zuwa,kullum idan kaga anci an koshi