Sashe 87
Tantiriya A Gidan Yari Book 2 Complete Hausa Novel · about 3 min read
tace a dawo da ita tausayinka take ji,Likita ne Kai kana da Allura a gafarce mu,Jauro ya juya ya fice yace ka sa key dinka,Annoor murmushi yayi ya rungume Iman,tace kaga dai tausayinka naji nima ka tausaya min yace ya zama dole tawan,da na kulla tsiya da Kinga tashin hankali da kin zauna,Iman tace a'a bazan zauna bama muyi wanka kayi min Allura na samu sauki. Kawu Yana driving yace yau naji kunyar da ban taba ji ba,daga yau ban sake wannan shishigi shi yasa Hashimu ya fada min yace ko an kawo Kara a irin wannan nayi kamar banji ba naki ji gashi naji kunya. Maman Annoor tace amma da ta hakura an gyarata taji sauki shi Kuma an samu makarin maganin tunda akwai,Jauro yace tace Yana da Allura fa rabu da su. GIDAN YARI Khadija wacce aka fi sani da Mero da gudu ta fito daga wani daki wuf ta afka wani dakin na kusa da Wanda ta fito a ciki,tana shiga ta dauki wani karfenta dogo me nauyi da kauri kamar Yar sanda,Wanda a gidan yarin ta tsinci abinta Tana zuwa ta samu Jikin bango daidai wata kusurwar dakin Inda wajen yake a tsage taci gaba cusa Karfenta tana dukan wajen tana bulawa lallai sai tayi kofa,tana ta marmaso kasar gini tana ta fama kamar wata yajuju wa majuju tana ta aikin fasa gini,Matashin Dake cikin dakin ta baya Yana kwance Yana baccinsa yaji abinda aka Saba yi kullum ta bayan dakinsa dake VIP, tashi yayi zaune Yana tsaki. Dan bakinsa karami ya bude yace waye? Mero tana jinsa tace nice kawarka,yace kawar ubanwa? taka ta bashi amsa,ransa ya baci,kyakyawan matashi ne na gaske fari ne amma ba fari karr ba sai Dan Karen kyau,Kana ganinsa kasan bai saba da wahala ba,gashinsa me yawa ya shafa ya dauki wayarsa me tsada dake ringing,yace hello...Abbu...gobara...ta cinye gidan du?...Muryar Mero yaji tace amma dai bata ci mutum ba ko? shareta yayi yaci gaba da wayarsa yace Subhannallah duka yanzu gidanmu ya Kone Abbu? Mero ce ta fashe da kuka daga baya tace shike nan gidan surukaina ya Kone munyi gobara,ta daina bula ginin ta fito tana kuka bilhakki da gaskiya,kowa ya tare Mero me ya faru? gidan su saurayina nane ya Kone gobara aka yi mana,sun zaci gobarar ma da gaske a gidansu aka yi ta. Mutane suka cika dakin su Mero ana ta zuwar mata jaje,Mata sai tururuwa suke yi,Khadija Ashe haka aka yi muku gobara,tace wallahi abin ba kyau gida hadadde an ware min part dina guda za a kaini can in anyi aure amma ba rabo ya Kone yanzu sai an gina wani,labari ya cika ko Ina anyiwa Khadija gobara a gidan aurenta,Dake tayi mugun suna shi yasa kowa yaji labari,shi Kuma matashin da aka yiwa gobarar ma ba Wanda ya fadawa to bama ya kula kowa a gidan,dama dama ma su Malam Jilani Yana zuwa wajen su. Mero tsabar jaraba har su Skola sun Santa su Goje sabo da tsayawa take a Jikin katangar Maza tayi ta surutu tana basu labari,idan Allah ya kawo wani zai wuce yaji kadan, da tunanin su Goje ma Aljana ce a wajen take fitowa tunda basa ganin kowa sai dai suji maganganu" Kuma sabo da tsayin katangar da kaurinta bama a Jin me mutum ke fada sai anyi da gaske. End of book 2 Mu hadu a book 3 Babu hutu Kuma sabo da anyi tsaye tsaye sosai ku dauko shi a shafin mu https://hausanovels001.com.ng AsmaBaffa SummaryInformation DocumentSummaryInformation WpsCustomData TECNO LD7 WPS Office Normal Times New Roman Times New Roman Calibri Calibri !%),.:;>?]} $([{ d20d6ad8a7934b06b14fc386f6c0de0d