Sashe 47
Tantiriya A Gidan Yari Book 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
nayi ta dan sarara da danginta,Kamal yace ka kyauta gaskiya,kaga Dan iskan yaron nan zai riga ni aure ko? Spark yace wai Misam? Ae mana nayi mamaki fa wai gobe Chika zata tafi hado lefenta,su Mima idan suka ga itace ya kenan,Mima ta nace sai taje gidan su Chika wai tasan wacece matar Misam,Kuma fa Baba yayi bincike wlh basu da mummunan hali suna da asali me kyau,ita nasan so take taga masu kudi ne ko talakawa,Misam Kuma yaki yarda sam,Rafeeq dinma gobe za a Kai kudi bata sani ba Kuma sai anzo daurin aure taji an daura da Rafeeq,Kamal suna ta dariya ,yace ni nawa 5mnths aka saka rana wai gidan su Siyama basu shirya ba,normal ne ai suna da hali su Siyama cewar Spark. Sun dade suna Hira da Spark har 11pm sannan Kamal ya tafi gida. Naila ta sa waya a gaba taki bacci tana ta jira Spark ya kirata,ta kira Kuma bai daga ba yace Yana meeting zai kirata back bai kira ba,shi Kuma barinta yayi ta samu ta shakata,wayarsa na hannunsa sai pics din Naila yake kallo da videos dinta Yana so ya kira kar a dame shi ya fiye naci a haka bacci ya kwashe shi,Wayarsa tana silent Naila tana ta kira ba a daga,ta kumbura ta cika fam tace lallai an samu matsala Bado yayi Sanyi,haba ai ni nasan tunda naga Spark ya barni har 3days Kuma ya kawoni da kansa nasan da matsala badan Allah bane,Ashe gajiya yayi Dani,dama Abba yace love zai ja baya gashi Nan tun ba ayi Nisa ba sai ta fashe da kuka uban kowa sai da ya tashi a gidan a firgice an zaci wani abin ne ya faru. Tana ta rusa kuka Hidaya ta fito tayiwa su Abba Knocking suka bude tace Aunty Naila ce ta hanani bacci tana ta rusa kuka,Abba yace dama kukanta nake Juyowa na zaci ma Malam Sahabi ne ya rasu shine yau naji ance Yana zazzabi,tace Aunty ce Kuma tace kalau take,Abba suka je dakin Kubra tace lafiya Naila Baki da lafiya ne? Spark ne.....Abba yace ya rasu la'ilahaillallahu tafiya Abuja ta kamamu cikin dare,dazu dazu aka rabu Kai duniya Abba ya fashe da kuka,Naila sai tayi sauri tace wayata fa yaki dagawa sai text ya min sau uku kalau fa yake,Abba yace amma ke dai Naila anyi Jikar Uban Kubra,Allah ya kwashe miki zunubinki tas Naila, yanzu ki dinga kuka haka sai kace mutuwa akayi,Kubra tsaki ta ja ta koma daki,Abba yace so kike ki kashe kanki da soyayya ai shike nan,Hidaya ya kalla ta tsaya yace wuce ki kwanta Kwaila ke har abada baza ki kiba bane idan ni kika gado kin shiga uku kuwa mijinki ya tanadi Sha ka fashe Kawai kullum tsilai tsilai sai iyayi,aure zan miki na yi miki miji,Hidaya ta kwanta yace ga kanwarki Nan Zarah sai girma take tana ta faman irgar dangi, kullum sai irga su Malam Hallai take Yana kabari,kunya su Naila suka ji suka yi shuru,yace ke Naila in Kinga dama ki kwana kina ihu watakil ma ya manta dake. Naila tana jin haka tace ni dai gobe zan tafi na fasa kwana uku ni dama wlh gidan nan ya ishe ni,gwara Ina gidana da yanzu Ina abinda naga dama,Abba tafiyarsa yayi ya barsu . Spark da asuba ya tashi babu Naila babu sex na asuba jaraba Kuma ta motsa,ya jawo wayarsa yaga kiranta yafi ashirin,ya kirata back tana ta bacci bata sani ba. Masallaci Yana zuwa a turbine ba mutunci ya shiga,ana idar da Sallah ya fice yana fushi. Naila tashi tayi sai bayan tayi sallarta itace ta musu abin Kari a gidan,tazo sabo da haushi taga kiran Spark amma taki bi tayi fushi,yau Kuma harda yiwa Umma kwalimar gida aka gyara ko Ina irin babba tazo gidansu,zuwa yamma ta shirya tare da kanwarsu ta rakata Makwafta daga Nan ta wuce ganin Hanan ya ta koma taci gaba ko kuwa,Naila tana zuwa gidan tayi Sallama Baban su hanan ya tarbeta Yana murna yace Naila kece ko ba ita bace ne? Naila tace nice ta gaida shi a mutunce ta Sha kaya masu tsada tana baza kamshi,ta shiga ciki ta samu Hanan duk ta rame tayi baki,Hanan fuska ta bata ta Kalli Naila tare suke da yarta Amal da Zarah,Itama Maman Hanan ko wajen zama Bata bawa Naila ba tace idan Amal kuka kawo bama so kuje da yarku ku rike. Amal tace ni wlh bazan zauna ba Nan gidan koko ake Sha da garin kwakwi sai dai mama ki biyo mu,Naila ta Kalli Hanan tana murmushi tace Hanan ba magana to Ina Kwana ya aka ji da rashin Hallare Kuma ga Sanyi yazo,Hanan ta kalleta tace Yayanki ne Mayen nono a haka zai kare Shegu Yan iska,Mayen nono Inshaallah Nono ne ajalinsa, inshaallah sai yayi bara a titi,Naila tace uban yarki ne ai kuma da yarki za a ci wahalar,na gaba yayi gaba na baya sai labari wlh ai tuni mu mun cuci Talauci dama zuwa nayi na gani kinci gaba da kika ce a sakeki,ai kamata yayi naga kinyi kinyi fresh,Ashe yayana ya iya kiwo yanzu ga halin da kika fada,to Yaya ma ki sani jirginsu yau zai daga sai Dubai zasu tafi Honey moon. Hanan tace idan ban miki dukan tsiya ba Allah ya tsine min Shegu Yan iska masu bin malamai ko me aka muku baya cinku,dariya ta kama Naila tace ai Wanda baya nufin kowa da sharri asiri Bai tasiri a kansa madam ki sani yanzu ma Amarya ciki gareta, jiya ma wlh ni na dafa mata taliya da yaji,kinwa kanki Hanan kiyi karatun ta nutsu ki daina batawa kanki lokaci kina kashe kudinki wajen malamai makaryata,Hanan ranta ya baci matuka Jin Beauty tana da ciki gashi wai zasu tafi kasar waje ita ko tashar kwanar dawaki bata taba zuwa ba. Babar Hanan tace fita ki bar mana gida,Naila ta Bada amsa nan har gida ne? Ke wlh kamata yayi yaranki su tsine miki ma,Baki cacanci uwa ba,Dake ubanki ne ya Haifa min yaran?,ke uwarki ta garin ce? Mene Bata yiwa Hashimu Dolo ba muna da tarihi ai cewar Maman Hanan,Naila tace to ta tuba yanzu ta gane gaskiya yanzu love suke zubawa,ke kuwa fa kin tuba ne?ku baku San mutum in ya tuba a kyale shi ba har mutuwa ana Masa gori haka hausawa muke. Naila kudi ta zaro ya Kai 20k ta mikawa Baban Hanan tace gashi Baba ka ci tsire karka basu ko sisi ciki,ya washe baki yace dama Likita yace jini na yayi kasa na gode miki, Amal tace Mama zamu tafi baki ga yajin bane har yau? Dan Allah Mama mu tafi tare gida wajen Daddy Aunty ta daka mana wani yajin da yawa zata naki,Umma Kubra ma ta hada wani jiya akwai yajin da yawa harda tafarnuwa a ciki ma,Hanan ta daka mata tsawa dalla rufe min baki shashasha ubanki ma yaci ubansa,Naila tace Uwarki ma taci uwarta,Hanan ta taso zata daki Naila ai Naila da gudu tayi waje da su Zarah,Baban Hanan kuwa sai murna yake Yana yiwa su Hanan fadan rayuwa. Naila Spark Yana ta kiranta sai yanzu ta daga tana hanya ta gaza share shi,yaji karar motoci da machines,da fada yace Ina kika tafi haka? Gaida dangi na kiraka kaki dagawa sai yanzu Kuma ka fara min fada,to ya kike ya su Umma da Abba? Kowa lfy suke,yace ke fa? tace Alhmdllh Ina ta Jin dadina,ni gaskiya na fasa barinki Kwanan ki dawo yau,Naila tace tab ai wlh bazan dawo ba sai nayi kwanaki na Umma tace ma sai naje Kauye na kwana biyu wajen Kaka kaga 5days kenan,Spark yace azo a dauki gawata kawai,ni gaskiya ban yarda Malama gida ba kowa,kaje gidan Mummy mana,ya buga ya buga Naila tace wlh baza ta dawo ba, fushi yayi ya kashe wayarsa ya mike a Office ya fito a fusace ba mutunci kadan yake jira ya ci mutuncin mutum. Papa ne ya kirashi a waya yace yazo Yana son ganinsa,ya fito ya nufi gidansu, Yana fitowa a mota Haly kanwarsa haushinsa take ji sunci duka ta bata rai ta taho zata wuce ta gefen Spark Baki ta turo ta Harare shi harda zuwa kamar zata bangaje shi,dama Spark a wuya yake hannunta ya ruko tare da dawo da ita gabansa ya fesa mata Mari har uku,ya rike hannunta ya Murda shi ta bayanta,sai ihu take da kuka yace da wani Soja kawo bulala,ihu ta fara iya karfinta sai da su Mima suka fito,Spark ya sa balulala ya fara tsula mata yaga ma lokaci take bata masa takalminsa me tsada ya cire da shi ya dinga dukanta kamar Allah ya aiko shi gashi ya riketa ram,Su Anam ganin haka sun zaci duka na biyu yake musu duk suka gudu suka buya. Mima kuka ta saki tana janye Spark tace kashe ta Zaka yi marar Imani, ka musu wacceen dukan ashe be isheka ba,Sam yaki sakinHaly yace ki tambayeta me ta min wannan yarinyar kanwar kanwata ni zata bangaje ta harare ni ya sake zuba mata Mari tana ihu wayyo na shiga uku zai kashe ni Papa Mima....wlh bazan yafe ba,tana fadar haka kafa yasa tana fadar haka yayi ball da ita,sai da kowa ya tausaya mata yanda yayi ball da ita sai da bakinta ya fashe sosai,amma kamar ana Masa Allura ya bita jikinsa har rawa yake ya damko ta tana jin wuya ta fara bada hakuri wlh na tuba ka yi hakuri bazan Kuma ba,wata farar kujera ya jawo zai buga mata Mima ta fashe da kuka ta rungume shi ta rirrike shi Dan Allah karka kashe min Yata,Spark yana huci yace ki fada musu kar su sake kulani daga yau bani ba su dukkan matan gidan nan idan ba haka ba wlh ko a hanya wata ta kira sunana sai na nakasa ta,akan wannan tsinanniyar matar taka zaka rabu da Yan uwanka wayyo ni ku kashe ni ku huta,Spark yace ai ba sai mun kashe ki ba idan kwananki ya kare tafiya zaki yi,sabo da na dawo Ina mutunci a gidan Nan shine za a rainani dama ni ba wajen ku nazo ba me zai kawoni Inda ba a kaunata,Papa ne ya kirani badan haka ba ma bazan zo ba,part din Papa ya wuce abinsa,Papa duk abinda suke