← Book details Tantiriya A Gidan Yari Book 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 87

Sashe 27

Tantiriya A Gidan Yari Book 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

randa guda,Dana kalleta sai da na sake kallonta sabo da nonuwanta sai an hada kaina dana Hashimu,suna zuwa Dennis yace shi Dan Enugu ne shago yazo ya bude a garin Tudun wada Yana siyar da kayan masarufi. To Saratu Kuma kawarsa ce suna mutunci shagonsa a Jikin gidan su Saratu yake,Saratu in taje shagon sai Dennis ya dinga bata biscuits da alawa,idan yaga ba kowa sai ya dinga tattaba mata kirji,a hankali Saratu ta saba sai ya fara kashe mata kudi Yana siya mata har kayan Sallah,su Kuma wasu iyayen babu bincike idan suka ga namiji Yana bawa yarsu Abu basu bincika akan wanne dalili wasu ma karba suke suna Murna,Dennis ya lallaba Saratu ya dinga kulle shagon da ita a ciki idan ya faki idon mutane har ya samu ya dirka mata ciki. Dake yare ne Yana da wayewa har kwayoyin Hana daukan ciki yake bawa Saratu tana Sha,sun dade suna tafka masha'a ba a sani ba sai da Saratu ta daina Shan magani bai sani ba tayi ciki,har ta samu mijin auren za a mata aure kawai sai ciki ya bayyana,da iyayenta suka fara dukanta sai tace Dennis ne,Mutanen kauyen suka ce sai Dennis ya bar musu gari,shine Dennis ya dauki Saratu a boye ya taho da ita wajen Likita ya biya kudi za a cire cikin ba tare da sanin kowa ba,can Kuma a gari ana ta cewa Saratu ta gudu ta bar gida. Ina Zaune tare da Likita suka zo za a zubar da cikin nace kar a zubar ni Ina so kawai Dennis yace nawa ne,Likita ba yanda baiyi dani ba akan na fita safgar naki ji muka tafi da Dennis da Saratu gidansu nayi ruwa nayi tsaki nace nawa ne cikin ba ruwan Dennis,Iyayen Saratu sunji dadi sun ganni Musulmi suka ce da Zina da Arne ai gwara Musulmi,sannan gasu da son kudi,lokacin naso idan Saratu ta haihu na aureta kiyi hakuri Karima sabo da nonuwan Saratu naso na aureta sabo da na samu natural Pillow Allah yasa Kuma Saratu da na tafi da ita gidana bayan ta haife ki na Yanka Miki raguna biyu kema na sa miki suna Karima,Bayan ta yayeki ta samu miji naga tana sonsa matashi ne me rufin asiri da na fahimci tafi sonsa sai na aurar da ita ga matashin Abubakar,yanzu yayi kudi sosai ya zama Alhaji Abubakar amma an mata kishiya sabo da itama daga kanki bata sake haihuwa ba. Abba yace watakil kwanta daya ne a duniya Kuma tayi kuskure taje Arne ya mata ciki,Jauro yace su a tunanin Iyayen Saratu idan ta Haihu a bawa Dennis yarsa ko dansa,Kinga mu musulmai munyi asara bamu San ko zai amfani duniya ba wannan dalilin yasa nace cikina nane Kuma na hana Saratu kisan kai tunda zubarwa zata yi. Na rufawa Dennis asiri yaci gaba da kasuwancinsa Wanda har ma yanzu yafi karfin shagon kauye ya koma cikin birnin kano sabon gari ya bude Mall katafare,a dalilin wannan taimakon da na Masa Shekara daya data wuce yace min ya musulunta sabo da abinda nayi Masa,shi baya kyamar Dan shege sabo da su sun Saba ba ruwansu kawai sabo da mutanen gari sunce sai sun kashe shi yasa bai karbi yarsa ba. Karima idan zaki tuna akwai wani yare babban mutum da yake yawan zuwa gidana duk state din da na koma Yana zuwa da Sha Tara ta arziki,har dinkuna Yana miki,Yana daukanki ya fita Dake kina karama ya kaiki wuraren shakatawa lokacin Christmas da Sallah idan tazo,yawanci ma ke bana siya miki Abu shine yake miki,sannan tunda ya musulunta ya auri mace Musulma Zainab kin Santa yazo da ita wajenki,sannan Kinga ya haifi yara uku yanzu kannenki ne,Karima tana hawaye tace dama Uncle da nake cewa Mahaifina nane? Jauro yace tabbas. Tace ai ko rannan Kawu yaje gidana ya kawo min Leshi da atamfa da shadda harda kayan yarana,Jauro yace mahaifinki ne to,sannan ya siya miki gida da fili takardun suna hannuna tunda ya musulunta yaji ance baza kici gadonsa ba tunda ba a same ku ta hanyar aure ba,Jarin da kike juyawa kina siyar da magungunan mata shine ya bani kudin yace na Baki ki duba sana'ar me kyau kiyi. Abba yace wlh na Dade Ina mamaki gaba daya Karima kalar inyamurai ce da ita har hasken fatar irin nasu kana ganinta kaga Igbo,Jauro yace wlh da tuni an markade ki a Injin nasara nace a bani Ina so,Karima tace na gode Kawu,Abba yace sai wa Kuma?Jauro yace sai Haidar,Abba yace Dan ubanka marar ji bude kunnenka shike nan yaro sai dai a samo Maka mace a dangi,Jauro yace ai ni da nake so ka bashi Hidayan ka,Abba yayi dariyar yake ya share zancen yace ci gaba kaga. Haidar watarana da dare na dawo daga Adamawa na biyo ta garin Gombe Jikin wata bishiya a bayan gari,lokacin duniya na kwance naga wata me tsohon ciki tana murkususun Nakuda tana kuka da alamar haihuwa zata yi,na tsaya na taimaka mata na kaita asibiti bamu Dade da zuwa ba ta haifo Danta namiji santalele,Ina waje Likita ta fito ta kirani tace wacce ta haihu tana son Ganinka,Na shiga tana kwance taji jiki gaskiya sosai,Jaririn ta Mika min na karba tace sunansa Aliyu Haidar, na baka shi ka rike shi da Amana,a Nan ta bani tarihinta tace ita marainiya ce,aka kaita aikatau gidan masu kudi a garin Abuja,me gidan da take aiki a gidansa matashi ne sabon aure ne shima,matarsa zasu yi shekaru daya da ita,shine watarana matar tasa tayi tafiya ya mata fyade ta samu ciki,da suka San tayi ciki suka mata duka suka korota,gata marainiya bata da wajen zuwa Yan uwa sun takura mata,haka ta dinga yawon aiki gidajen masu kudi kowa ya ganta da ciki baza ta Dade ba zasu Kore ta har cikinta ya tsufa haka take yawo gari gari tana Fadi tashi,Haidar yace Allah sarki Umma ta,Babana ka cuceni bazan yafe ba tunda ka wahalar da uwata, Jauro yaci gaba yace karshe da cikin ya isa haihuwa sai ta dawo gida tana zuwa Yan uwa suka koreta shine ta fito daga lokacin ta fara nakuda na dauketa na taimaka mata. Naso na aureta Haidar amma Allah bai sa min sonta da aure ba,Kuma kyakyawa ce sosai wlh kamar Yar India,gaka Nan kamarta ka dakko sak Amma tace hancin ubanka kayi ita bata da hancinka,na dauketa ta zauna da mu ta yayeka,itama ta samu mijinta ana kiransa da Alhaji Tijjani Salo,me kudi ne a kasar waje suke rayuwa sai dai tazo da yawo Allah ya azurtata yanzu in ka ganta tab,amma itace da kanta tace baza ta dawo ta ganka ba idan ka girma sabo da ka karka kalleta a Yar iska ko wacce ta cuceka,Haidar yace wayyo ta fita sol ko ba soso a hadani da ita Dan Allah a fada mata Dan dakan kukan ta ya girma gani ma ni Ina Jin dadina,Kawu Ina da Kai wa zan zauna Ina damuwa da shi,Ni wlh har abada ma bana son ganin Ubana,Jauro yace yo me za ayi da shi tambadadde,amma dai Yana nan a Abuja lokacin mun kaika can ya mana korar kare yace sharri aka Masa matarsa ta Goya Masa baya Yana Nan ko sunansa Alhaji Kabeer ko wa na manta da matarsa da yaransa amma naji kamar ance matar ma basa tare ko an kamata oho dai nasan gidansa, Haidar yace kyale shi zan tayar da kura in na samu time inje dole ya bani kasona na kudinsa kafin ya mutu,Abba dolo yace a'a mahaifi ne kaji ,Abi a sannu,Haidar yace ni babata a sannu ya bita ya mata fyade gashi nan ya jawo min na fara tambadewa nima amma daga yau na tuba wlh na daina ko Dan Na farantawa Kawu rai,Kawu yace kowa ya tuba Dan wuya ba Lada da ai Ina fada muku gaskiya bakwa ji,dariya Haidar yayi Dan shi yafi kowa fara'a a gidan Jauro. Abba ne yace Rahma,Jauro Yace Nabeela dai,Annoor yace na girmi fa su Rahma amma ake tsallake ni,Hashimu Dolo kawai ya karbe zancen yace naka labarin yayi Muni da yawa sai a karshe,gaban Annoor ya yanke ya Fadi,Iman tace nifa? Yace kece Auta fa 'Yar jakar Uba sarkin son namiji Jauro ya furta. Nabeela ta zuba tagumi Jauro yace Nabeela Babarki ai kin Santa sunanta Halima Yar Bauchi ce soyayya ce ta rufe mata Ido wani saurayinta Umar Kwalta ya dinga yaudararta ita Kuma tana sonsa sosai duk abinda yace sai tayi,shi Kuma baya sonta tsakani da Allah lokacin muna Niger Minna,na Sanshi ya sanni abokinane a garin,baya son Halima da aure da iskanci ya sota ya lallaba ya mata ciki a dakinsa,mata masu biyewa soyayya Dan mace na son namiji duk abinda yace tayi sai ta aikata sabo da kar ransa ya baci ko kar ya fasa aurenta,basu San sakin jikinki ga da namiji Yana rage soyayya ba ko da Yana sonki,har dama dama ma Dan romance akan ace kin bashi kanki daga lokacin ya gama sonki,Halima bata gane ba sai da ya mata ciki,Allah sarki Halima sabo da wannan bakin cikin Mahaifan Halima suka mutu,babanta ya fara mutuwa sai uwar sabo da Hawan jini ne ajalina uban Halima,ita Kuma Babar Halima ciwon zuciya. Halima ta rasa gata gashi ciki Ya girma ta bani tausayi ita kadai a gidansu kamar mayya,dama basu da wani gata tausayi ta bani yasa naje na dawo da ita gidana itama ta haihu,ta tuba ga Allah sai kuka ko yaushe,Shima Umar Kwalta yayi nadama na hada su aure,bayan sunyi aure da Shekara daya ta samu ciki da cikin a jikinta Allah ya mata rasuwa,shima Umar shekarunki biyar a duniya Bai Kara auren wata ba mota ta Kade shi ya mutu,Nabeela lokacin kina wajena Shar da ke abinki. Nabeela tace yanzu dai kenan iyayena sun mutu? Jauro yace ae sai yan uwanki na wajen Uba Dana uwa suna Nan sanda kina yarinya na Sha kaiki fa sabo da irin wannan ranar yasa na dinga wahala sai da na San asalinku da dangin ku ,suma suna zuwa ganinki kina karama sabo da Dan uwansu ya mutu kakarki ma ta wajen Uba tana yawan bugo waya taji kina lafiya. Nabeela tace Allah yasa mu dace suka ce Ameen. Rahma kuwa ke ki saurara kiji labarinki, Mamanki,Bushra wato a Yobe state take, kafin
Chapter 27 · 0% Book details