← Book details Tantiriya A Gidan Yari Book 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 83 OF 87

Sashe 83

Tantiriya A Gidan Yari Book 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

kannenta su uku Maza biyu mace daya. Duk yanda Mamanta ta Kai ga sharewa sai da taje ta dubata,ta sameta tana ta rawar Sanyi tana kuka. Hanan kuwa Amarya bayan kwanaki haka take dama da aikin bautawa suruka,komai itace take wa suruka" bata Isa tayi magana ba sai Jibson yace so take ya shiga wuta, Jibson duk matan da yake aure yawanci Yan mata ne shasha shun yara,da ya auri bazawara tun a kwanciyar aure yaga banbanci Yana samun nutsuwa da gamsuwa sosai,gata dai dai da shi waccen na baya Kuma gaba daya baiyi dace ba basa iya daukan lalurarsa,dama gashi wani sai a hankali in suka gaji shima ya gaji da sunce ya sake su sai ya saki baya jira,amma Hanan Kam yace bazai yuwu ba yanzu yasan yayi aure shi Kam ya samu mace,Hanan Kuma lallabawa take lokaci yayi tace ya saketa,yanzu dadin Hallaren Jibson take ji baza ta iya ficewa yanzu ba. Lubna ce kawar Hanan tazo yau ta samu Hanan a bangaren surukarta ta gama mata aikin komai tayi aikin part dinta Kuma tayi girki ta kawo suna zaune suna hira,Dake bai bada kofar a Raina Masa uwa ba wani ladabi Hanan take mata,suruka sai yabawa take da hankalin Amarya tana addua kar auren Nan ya mutu ta gaji da aure auren Jibson,ko wacce tace ya aureta sai ya aurota shi yasa bai taba sa'ar aure ba ko kadan sai yanzu,Hanan tun tana ladabin dole har ya koma na gaske,Ganin Lubna surukar tace kuje bangarenki mana tunda mun gaisa,lokacin Hanan ta mike suka wuce,suna shiga Lubna tayi dariya tace Anki sharar masallaci anzo ana ta share kasuwa. Hanan tace ke dai bari Inama wannan abin da nake Mohsin nake wa da iyayensa wlh da bazai sake ni ba,mijina son kowa kin Wanda ya rasa amma ya zanyi na riga na cuci kaina,na yiwa kaina,yanzu Kinga nan ma a haka Alhmdllh komai akwai ci da Sha da komai abincin ma me dadi muke ci,ko Dan uwarsa Ina tauna kashin kaza wlh,sabo da shi babarsa yace dole sai taci dadi tunda da lafiyarta,kullum daga soye soye sai farfesu,Lubna tace to gashi kinyi kiba wlh kin Kara kyau,Hanan tace Madara kullum kayan tea lafiyayyu rabona da su tun Ina gidan Mohsin sai yanzu,Lubna tace to ko fasa fitar zaki yi ne karfa ki fice a nan Mohsin yaki Maida ke Dan wlh yanzu wannan matar tasa ta kankane komai,kiyi dogon nazari tunda Allah yasa Jibson ba matsala ce da shi ta kirki ba ki zamanki,Dan Adam dama tara yake bai cika goma ba,daga ke sai suruka,Hanan tace itama Bata da matsala tare muke aikin komai da ita ba me son jiki bace tayani take yi wlh,Kuma ba sa Ido,kullum sai tayi Masa nasiha da fada ya rikeni Amana,Kinga ma ya siyo min kaya set goma shekaran jiya wai du na Kai a dinka min sabo da ba a yi min lefe ba,yace zai siyo min takalma da jakankuna da mayafai,tafawa suka yi Hanan tace ranar in fada miki na zage mun sha love da dare mutuminki washe gari yaje kasuwa ya dawo sai gashi da kaya wai yaji dadin night din,Lubna tace a Kara dagewa,Hanan tace ba fara sonsa ma fa ni, Lubna ta zaro ido tace da wuri haka? Ya iya love Shima duk da dai nafi son Mohsin amma Shima dai ba laifi Kuma abinda yasa na Kara sonshi wlh ban sani ba baki ga yanda ya Kai kayan abinci gidan mu ba harda kudin cefane ya bawa babanmu,Kiga fa a yanda aka yi auren nan amma ya iya abin Alkhairi haka in na fita Mohsin bai Mai dani ba wa zan samu kamar sa? Lubna tace shawara gaskiya ki cire fita a gidan nan kiyi zamanki wlh,tace shine Nima nake wannan tunanin ta shiga kitchen ta zubo mata kayan makulashe tana cewa rannan da kannena suka zo Lubna ya basu kudi ya siya musu abubuwa Kuma ya Nemo Napep aka kaisu har gida,Kuma Baba yace idan na sake ya sakeni kar na koma gidansa na nemi gidan wani uban ba dai shi ba,Lubna tace to ki zamanki wlh shawara ce, Hanan tace zanyi biyayya haka na zauna lafiya ya fiye min mutunci ,duk Dan ta zauna sai yabon Jibson take yi Lubna na sake kwantar mata da hankali tayi zamanta. Suna zaune sai ga Jibson ya shugo da Leda,suma ta fito a kansa yayi kyau fiye da kwal da yakewa kansa,Lubna tace ranka ya dade,yace tare da naki sai yau ma za azo Kawa guda,yace me gidan ne nawa baya gari sai da ya dawo,yace Mashaallah a dinga biyayya,Hanan tace sannu da zuwa yace Sweety bayibe(Baby).....ya fada da iskanci wai bazai taba cewa Baby ba sai dai Bayibe...Hanan tace Baby dai yace sai kin haihu sai ki haifi Baby amma yanzu ke a haka katuwa ai sai sai dai Bayibe......Lubna ta dinga dariya,yace wai in tambaye ku suka ce muna ji" Dan Allah a Ina kuka ganni har daya ta kware min? Lubna tace ni na ganka fa naji mata suna ta yabonka ni kuwa nace na gano dai dai da kawata,na nuna mata Kai tace kayi mata,Jibson yace karshen duniya ne yazo dama ance mata zasu dinga Kai kansu wajen mu sai gashi har a kaina a gwadawa duniya,alamomin tashin kiyama har a kaina ya fado,ni Kuma haka Allah yayi ni sai dai mata su dinga zuwa,ni kuwa ban taba turning mace down ba in dai tazo sai na aura wlh ba abinda ya dameni zaka nake da kudina ta wannan barin,amma yanzu Ina fata kar wata tazo Bayibe ta isheni,Hanan harda cewa Ameen Allah ya sa. Suna zaune yace Yaya Hajiyata yau? Hanan tace lafiya take,yace an mata komai? tace ae yace yawwa,kar ayi min wasa da uwata,Da ran uwata ya baci gwara na mutu na huta indai ta silata ce,Lubna tace wlh Allah ya baka zaka yi karshe me kyau,yace albarkarta ce shi yasa kullum sai rufin asiri,Hanan tunani ta Lula yanda ita suke wasa da kula da iyaye suyi ta bata musu rai sai gashi suna ganin Jibson kamar marar hankali ashe ya fisu hankali,a ranta tace itama zata gyara ta dinga yiwa nata biyayya tun da sauran lokacinta,da yamma mijin Lubna yazo ya dauketa. Jibson ledar da ya kawo ya bude ya bawa Hanan,dogayen riguna nane kala uku Arabian gown masu kyan gaske tayi godiya,yace da bakya kula da uwata ko slifas bazan siya miki ba,yanzu Kinga a banza zaki dinga cinye kudina,matan gaba masu zuwa a aure su shike nan sai dai suyi hakuri Kuma kin kwace kudin,Hanan a ranta tace dole na dage kuwa. Jauro kuwa da Amarya a hanya ya siya musu kayan makulashensu,harda Shan maganinsa na Kara kuzarin Maza sabo da yayi Amarya,Amarya Kuma sai kunya take ji,Jauro yace Nima Nan kunyar nake ji karfin hali nake yi Ummu Annoor,kallonsa tayi Yana driving tayi murmushi,yace wannan kunya taki ko budurwar zamani baza tayi ta haka ba,tayi yawa,da budurwar zamani ce" da yanzu ta min kiss yafi ashirin,amma ku s ai kuce Kun girma,ku da ya dace kuyi sabo da kune tsohon hannu karki sake Dake Habiba ta miki kafa in ta kwace ni shike Nan,kar ki ganki jajir ba haskenki zan ta kalla ba babu ruwana da shi"sai na tafi wajen Habiba ta bani nishadi,Maman Annoor ta murmusa kawai,yace kamar ba Yar Boko ba ni da nake tunanin ma kafin muje gida kin min kiss yafi goma a kunyace,dariya tayi ba shiri. Haka suka karasa gidanta Wanda ya gaji da tsaruwa ko Ina kamshi yake,Jauro ya wuce kamar gidansa Yana gaba har bedroom dinta Wanda ya Sha gyara,yace badan aure ba me zai kawo ni nan,sip ta bude ta cirowa Jauro wasu kayan bacci na manya ne riga da wando dogo marasa nauyi sababbi,tace gashi Hubby" Ido Jauro ya zaro yace me kika ce? tace gashi Hubby fa nace harda shagwaba,Jauro yace uhmm yanzu nasan kinyi makaranta,auren me Ilimi yayi a rayuwa,dariya tayi ta shige toilet,tana shiga Jauro ya nuna kansa da yatsa yace ni Hubby yo ai Ina Jin ko Annoor ba a kiransa da wannan suna shi da yake matashi bare Kuma Nabeel da ya auri Yar tatsitsiyar yarinya, Jauro kana shanawa dole na fadawa Hashimu yaji sabon sunana,Yar Innar tasa duk wani yabonta da yake bata taba kiransa da Hubby ba ,sai da ta fito tace kaje kayi wanka,Jauro yayi wanka ya fito suka shirya ya jasu sallah bayan sunyi adduoi suka ci kayan makulashen su harda bawa Amarya a baki. Bayan sun gama kowa ya koshi zama suka yi suna hira sabo da abincin ya narke yabi jiki,Jauro mikewa yayi tare da zama a Saman gadon Yana addua,zama tayi itama sannan suka kwanta gaba daya tare da shigewa bargo,Jauro ya fara soyewa da Amaryarsa gwanin birgewa haka suka tsunduma a wata duniyar ta musamman,Jauro Jarumi ya jiyar da Amarya dadi ya jefa ta a farin cikin da ta dade bata samu ba. Yahuza donation ya fito daga gidan giya a make Yana tafiya Yana tangadi bai kula ba ya hau Saman kwalta wata karuwar mota tazo ta make shi nan take ya fashe a titin ko shurawa baiyi ba yace ga garinku Nan,mutane suka cika a wajen dake popular ne kowa yasan shi sai jimami akeyi aka dauki gawarsa da Yan sanda bayan an gama duk abinda ya kamata aka kawowa iyalansa,Iyalansa Asabe sai kuka da ihu,yaransa ma haka,Asabe tana kuka tace wlh nasan matukar mutum yaki jin tsoron Allah ya tuba karshe wani a kan aikin banzar zai mutu,gashi Nan ance daga mashaya ya fito,anyi anyi ya daina yaki gashi mutum Yana ta abu bai san Kwanansa ya kare ba a duniya,shi yasa ake so mu dinga tuna Allah da mutuwa tana iya riskar mutum a kowanne hali,babu batun sai da cuta. Amarya tana kasa tana ta birgima ana bata hakuri tana cewa yaranmu nake ji Asabe yaran mu,duk da haka shi din katanga ne a tare damu,komai lalacewar me gida to me gidane wlh kawai muyi Masa addua Allah me yafiya ne zai iya yafe Masa,Asabe tace amma ba haka aka so ba ka mutu a wannan hali,waya suka dauka suka dinga kiran danginsu da danginsa na birni dana kauye. Ikhram tana zaune tayi wanka kenan suka kirata,tayi mamakin ganin kiran
Chapter 83 · 0% Book details