← Book details Tantiriya A Gidan Yari Book 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 70 OF 87

Sashe 70

Tantiriya A Gidan Yari Book 2 Complete Hausa Novel · about 2 min read

Naila bacci ta sake komawa Hidaya ta mike taje tayi knocking a dakin Spark tashi yayi ya bude yace kazo ka dauki Aunty tayi bacci a can,Spark yace Allah ya miki albarka Hidaya ya fito Yana murmushi ya shiga har dakin tana bacci ita da Zarah,hannaye ya sa ya dauke ta chak sannan yace ku sa key a kofar ku ya fita da ita,sai da ya dorata a Saman bed sannan ta farka,Ido ta bude yace tashi Ina da mood,tasan hali ko bata yarda ba ma ta karfi zai mata shi yasa kawai ta amince ta bada hadin Kai,sai da suka gamsu ta gama ihun dadinta amma ta dora da fushinta Yana ta dariya ya rungumeta a jikinsa Yana mata rada,tlyace wani dadi kike karawa fa.
Mima ta gama dafa shinkafa da wanke Arham ya shugo mata da su salat da sauran tarkace na kayan lambu su Haly ta saka suka gyara da kyar a Hakan ma sai da ta zazzage su sannan suka yanka,bayan Nan tace ga Mai can an soya me ci ya zuba,Arham da Shaheed su suka fara ebo tasu kowa a plate suka zauna a Palo,Arham ya Kalli Shaheed yace baza ka hau dining ba yau? Shaheed yace abincin ai ba kalar dining bane shinkafa da waken zaka hau wani Dining da ita asarar lokaci,Arham Yana dariya yace Nima bazan hau dining ba yau she Rabin da kaga Yan gidan Nan a Dining to ba kwai ba Madara iyayi ya kare,Mima sai da tayi Sallah sannan ta fito ta zuba tata tana ci,Arham yace Mima kina wuta,hararsa tayi ta mike ta bar Masa ma Palon gaba daya.
Chapter 70 · 0% Book details