← Book details Tantiriya A Gidan Yari Book 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 81 OF 87

Sashe 81

Tantiriya A Gidan Yari Book 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

bai dameni ba,Chika ta kunshe dariyarta tayi sauri ta juya baya ta saki dariyarta marar sauti ta gama ta maze ta juyo ta kwaso kayan abinci ta kawo gabanta duka,tace duka ni kadai haka mene da mene haka yaran nan ku daina Almubazzaranci Dan Allah,Misam yace kayan mijinta ne fa Allah ya hore Masa Kuma Ina gari ba yaji nayi ba Mima ai dole tayi girke girke,Mima tace to Allah ya Bada lafiyar ci wato ni ka fadawa magana ko Misam ba komai,yace Kai Mima ni na isa na fadawa uwata magana yi hakuri,ya bude mata taga dambun nama,Taga farfesun kaji,ga wata fried rice ga couslow sai kayan Sha,Allah sarki Uwa sai ta tuna su Arham dinta,su suna zuwa suci basa tunawa da ita amma ita tana Gani su ta tuno,tace bazan ci ba ni,yarana suna can tuwo suka ci Ina zan sa dadi a gaba naci,Misam sai ta bashi tausayi sosai yace Allah sarki Uwa wlh duk Wanda baibi uwa ba dole ya shiga wuta,yace to kici naki ki koshi sai a Baki nasu,Mima tace to da dai yafi,ta zauna taci abincinta ta koshi,Sannan Misam ya kira Chika kitchen yace Ina abincina tace gashi,yace to sai wanne? tace sai na me gadi Dana ajiye Masa,yace hada duka ki zubawa Mima karki rage komai,har lemon da kika hada komai da aka yi a bata du,tace har dambun Naman Yana da yawa fa yace bata duka ki juye mata,tace to Allah yasa dai Papa ya dawo haka Dan Allah kuce ta canja ya dawo kar ya shiga hakkinsu,Misam ya tsaya a bayanta kamar kwarto tana aiki Yana faman shashafe mata mazaunai"to ka bari na gama mana,yace Ina zan iya ni fa kin San Ina kunnawa to ba sauki a bani a huta kawai ni Dan wutar ciki ne. Dariya Chika tayi tace Rafeeq na tuna wlh Ikhram kamar handbag duk Inda zaije suna tare,Misam yayi dariya yace wannan ban taba sanin maye bane sai rannan,Spark ya dauki masifa aiki a Office wai shine Sakataren sa,in yaje to Inshaallah sai Ikhram taje tare yake tafiya da ita,ba uwar da yake sai soyayya,Spark zaiyi baki wlh har suka zo suna ta knocking yaki magana gashi ya sawa kofar key,yasa Spark yayi loosing contract din Kuma zai samu kudi masu yawa,Spark ranar tab kinga bala'in da yayi badan Allah ya kaini ba da Sunan Rafeeq korarre sai dai ya koma shawarmar sa. Shine suka canja salo yanzu idan yaje Office 1:30pm Ikhram zata hado basket guda na abinci ta taho ta kawo idan ta kawo abincin to sai an tashi zata tafi,shiga goma fita goma tana ciki mayya itama,karki ce wata uwa suke a ciki ba wai sex suke ba daga Dan Tabesting sai Hira da kallon juna,Rafeeq bai ki ta zauna a gabansa ba ya sata a gaba ya dinga kallo har dare,Chika tana ta dariya ta hadawa Mima abincin komai a flasks masu kyau ta shirya mata a katuwar Leda wacce zata dauke ta kawo mata,Misam ya dauki kayan yace muje mu Kai Mima gida,Chika ta dakko mayafinta suka fita. Chika ce take driving Yana gaba Mima na baya suna ta hira,Mima kamar ba ita ba har mamaki Chika take. Arham suna compound dukkansu ana uban zafi wutar gidan ta dakke an rasa dalili,Mima ta shugo ga Misam Yana sauketa suka juya,tace me ya faru da wutar ne? Arham yace ai mu yanzu Kuma tunda Papa ya tafi Inda kisan sai da ya tsine mana sannan ya bar kasar" bala'i sai afka mana yake iri iri,ba Inda bamu duba ba yaki yi,Kuma mun kira me gyara tsabar rashin Albarka irin tamu yace sai da safe, ga zafi ana yi,gari babu hadari,Shaheed yace Allah ka kawo mana taka iskar ta kyauta Dan uban bature yaje da tasa,Mummy suka gani ta yayo katon carpet ta fito waje tana cewa ku kama min nan,Arham yace to" a kusa dake zan kwanta,Mummy tace kasan Allah wallahi zan karyaka kanwar uwarka guda da girmana da komai tsofai tsofai ka sani a gaba,Arham yace ke Mummy yaushe kika daina saka jean da tshirt,wlh har 3qutr na Sha ganinki da shi kina busa Shisha sai kice tsofai tsofai,da kin San kin wuce lokacin kike sakawa,Mummy tace shisha dai bazan fasa sha ba naga shegen da zai hanani"Kai Shaheed tayani bana son Arham ya taimaka min,Shaheed yace Nima ba wani na kirki bane kadan nake jira,Junior Yana jinsu Yana gefe Yana ta danna waya ya mike yace,wai ayi mace ta haifeka amma ka fita karfi,kawo na shimfida Dan Allah jeki,ya karbe carpet din ya Kai mata Inda take so ya shimfida mata. Mummy da mificin robarta a hannu tana fifita duk,su Anam suna suka fito da carpet suka baza suka kwanta,Mima ta ajiye abincin tace bari nayi sallah na dawo,Arham yace zamu ci dadi Mima taje ta maulato mana me dadi,Mummy ta kwanta da shisharta a gefe sabo da jaraba sai da ta kira kawarta ta kawo mata jiya,tace Arham Ina zan samu garwashin wuta,Arham yace ki bawa Anam gawayi ma ya isa zata kunna miki shi ta rura miki shi ya kama,Ina zata samu wutar kunna gawayi biyu ko uku,yace a Badonta mana, dazu naji tana Hira da kawayenta tana fada musu mace in tana da wuta a Badonta ta wuce wulakancin namiji,Anam ta naji tace tsohon munafuki dama tsayawa kayi kana sauraren hirata a waya ko,yace to kice Baki fada ba mana,kawaye basu San wutar Badon taki ta Dade da mutuwa ba an sako ki kina Nan a gida kina tsara musu Karya su Kuma banzaye sun yarda,Mummy tace zata aikata indai Anam ce,yanzu Kai shine zaka ce na bata ta rura min sabo da baka da mutunci kaga sakuwarka ce ko, Arham yace ahh to cewa tayi fa wuta ce da ita a wajen ba sai a rura miki cikin sauki ba. Mummy hannunta ta mika zata jawo wayarta kunama ta gasa mata harbi a hannu ta zabura ta mike tsaye ta saki ihu,wani Abu ya cijeni,duk suka tashi kowa ya mike ya arce Mummy ta rike hannu tana ihu tana cewa wuta...wuta...Mima ta fito ta haska wajen ta hango kunama katuwa tace Kunama ce,Arham ya tugewa Haly dankwali yazo ya daurewa Mummy Hannu yace muje chemist suka tafi chemist Mummy tana ihu...Mima ta kashe kunamar ,Shaheed ne ya kira Spark Yana aiki lokacin a Palo ya daga,yace kazo kunama ta harbi babarka,ku kaita Chemist mana ni aiki nake sai da safe na zo ya kashe wayarsa. Naila ya kalla da ta zauna tana kallo Juyowa tayi suka hada Ido yace sorry Yana murmushi,tace ba komai kayi aikinka ai yanzu shine a gabanka,laptop din ya rufe yace me kika ce? Nace kayi aikinka ba komai,kansa ya dafe yace na gaji wlh daga yau na gama aikin nan sai nayi sati ban fita ba,kiyi hakuri ku nake nemowa kudin,Naila tace nifa bance komai ba kayi aikinka,yace ke dai ki Fadi gaskiya,tace hmm wacce gaskiya,in hallarenki kike so ki magana,Naila tace to in Ina so an fada maka zan zauna Ina jiranka ne ai dole ka bani,wato bama Kya missing dina ko? Naila tace tausaya Maka nayi kawai nasan Kuma yanda kake idan na baka magani sai ka kusa kashe ni ranar amma wlh badan haka ba baza kayi aikin nan ba sai dai Kwalbewa,to kawai nasan Important Abu ne shi yasa na rabu da Kai amma sanda zan sa ma kaci ma baza ka sani ba,yace sa min Dan Allah wlh na gama aikin yanzu,Naila tace kazo ka kusa kashe ni,tashi yayi yace Dan Allah ki bani,ko Baki bani ba dai ai na gama aiki zaki ji jiki,sati zanyi ba fita ba shiga,Naila tace to ni yau bana Mood ma,yace fushi kika yi wai? Da kin San matsalar da ta taso min kika ga Ina aikin Nan da baza kice komai ba,Rafeeq ne ya jawo min akan banzar soyayyar sa yaron nan ya cuceni da yawa,tunda na dauke shi aiki asara yake jawo min ba ci gaba,Naila tayi dariya tace sai hakuri ai zai daina ne,Spark yace ai nasan yanda zan Masa Salary zan datse masa,Naila tace a'a ka bari dai zan wa Ikhram magana tunda matsalar ta ce,itace take biye Masa,Spark yace indai tana zuwa bazai iya aiki ba tashi mu tafi dare yayi,9pm dinne dare yayi? Kallo nake Nima ka jira na gama,kitchen ya shiga ya dakko Fruits salat ya fito ya dauketa gaba daya suka shige bedroom. Annoor zuwa dare suna kwance Iman ta shige jikinsa tasa yatsanta a lips dinsa tana shafawa a hankali tana Masa magana kasa kasa,tsoro ma yake ji baya so Sam yayi komai sabo da kunya yake ji ba uwar da zai iya tsinana mata zai kawo,romance din ma ta rage zafi bazai iya ba shi yasa gaba daya ya hakura,kunyar kansa yake ji,Iman Kuma ga naci,Yana mugun sha'awarta amma yaki yarda ma yayi komai bayansa ya juya mata ya kwanta,kamar zaiyi kuka sabo da bakin ciki,Iman tace to tashi muyi Nafeela muyi addua,sai lokacin ya mike,duk basu San Maryam ta karya asirin ba ma. AsmaBaffa[2/7, 8:22 PM] AsmaBaffa: TANTIRIYA A GIDAN YARI BOOK 2 ~YARAN JAURO~ 101-105 Official AsmaBaffa SADAUKARWA NE GA AIDA MAMAN TASNIM Page naki ne Hasiya Muhammad
Chapter 81 · 0% Book details