Sashe 84
Tantiriya A Gidan Yari Book 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Asabe dagawa tayi taji Asabe tana kuka tana cewa Ikhram ki taho Uncle dinki ya rasu yanzu aka kawo gawarsa mota ta make shi...kit ta kashe wayar,Ikhram ta fara Innalillahi wa innailayhirrajun tace duk abinda ka min uncle Allah ka sheda na yafe Masa,Allah gadona da ya cinye kaf na yafe Masa har abada Allah ka Masa Rahma. Kuka ta fara ta kira Rafeeq Yana Office Spark ya saka shi gaba da masifa sai ya karasa aikinsa,Spark Yana zaune a Office din Rafeeq wai dole sai ya gama Yana Nan Yana jira. Waya ya daga ta fada Masa,Shima salati ya saki yace Allah yaji kansa bari nazo,Spark yace waye? Sirikina nane ya rasu Yahuza Donation,Spark yace Wanda yace baza a daura aure ba? Yace ae cousin din Ikhram,yace Allah sarki Allah yaji kansa yace Ameen,yanzu me zaka Bada sadaka wlh ko gidan kansu basu da shi,Spark ya Kalli Rafeeq yace nawa ne a accnt dinka? ai ka sani,sai dai idan Joint Dina da Sa yara zan siyar sai a hada a samu a siya musu gida su zauna a basu jari,Spark yace ka daina wani zancen siyar da joint kudin tallafi na kamfanin nan ai sun taru da yawa a eba a ciki ayi musu komai,Yace to mun gode,wai yaushe za a kaishi? yace kaima kasan yau ne tunda rana ce,yanzu tafiya zaka yi kenan? Yace bata bakinka kake yi ma ai zuwa zanyi na dauki Yar dagwai dagwai ta kafata kafarta in na kaita sai na kama hotel a can kullum naje har ayi 3days sai mu taho gida,Spark yayi dariya yace na gaisheka mazan fama,Ina zan iya barinta haka da yamma na dauki abata mu tafi masauki muyi bacci na kwashi aikin dare da safe na kawota,Spark yayi dariya yace Kai Namiji,Rafeeq yace Namiji ai sai Misam idan ba Chika tayi ciki,Spark kamar shine me cikin harda kakarin amai ohhhh uhhhh....Rafeeq Yana dariya yace wlh da gaske nake wai tsinken pt ta siyo ya bada positive,suka tafi asibiti akace ciki ne 4weeks kenan da samunsa,Chika tana nan da ciki ana amarci da ciki,Kai kuwa Spark ko gado kayi ne na mummynka har yanzu 6mnths shuru shuru kullum Naila sumul,Spark yace Amarcina nake ci dama ni nafi son haka amma yanzu Ina so ta samu cikin sai abinda Allah yayi,Rafeeq yace Allah ya kawo,Misam za ayi Baby ko mace ko namiji sai wani iyayi yake wai shi namiji ne,Spark yace ah yayi gaskiya ya je da zafinsa Kai. Rafeeq tashi yayi suka fito yace nima gida zan wuce na gaji so nake muje aikin hajji ma da Naila da Chika,Rafeeq yace ni shine za a ware ni ba komai,yace alkawarin Chika ne Sanda akayi bikinmu tayi kokari nace zan biya mata,Rafeeq yace okay to Allah ya kaimu,Spark yace kafi kowa cin kudina duk ka isheni haba, Rafeeq yace yanzu ma Ina jiran na taimakon kamfanin za ayi sadaka,Dan Allah kuzo da su Misam da su Arham,Spark yace zamu zo gaisuwa ayiwa Malamar Yan iska gaisuwa,dariya Rafeeq yayi ya shiga motarsa ya wuce gida. Yana zuwa ya samu matar tasa har ta shirya tana jiransa da akwatinta,Yana shugowa ta rungume shi tana hawaye,yace sai hakuri Muma duk lokaci muke jira yana bata baki,yace bari na shirya,tare zamu tafi? Yace ae mana" murna tayi sosai taje ta tayashi ya shirya ta zuba Masa kayansa da duk wani abin bukata sannan suka kulle gidansu ya kira Arham yazo ya dauki motarsa ya kaisu Airport, suka wuce shi Kuma ya tafi da motar abinsa yace banza ta Fadi zan more mota,a motar ya wuce gidan Misam,Yana zuwa ya samu Chika a kwance tana hutawa tana kallon film,Sallamarsa ta amsa tace nayi fushi sai yau,murmushi yayi Yana gyara agogonsa me tsada ya zauna yace Ina yini ta amsa tare da tambayar ya su Mima? Suna nan lafiya,ta furta sannu dan saurayi,me zaka ci? yace abin dadi mana Ina yayan? ya fita" yawwa Arham na aikeka mana,yace Ina? Dan Allah kasar calaba zaka siyo min wacce masu ciki suke ci,Arham yayi dariya yace irin taku kenan kice Misam shi har ya jefa one goal,gaskiya an bar Spark da Chaskarar kwallo har yanzu Kuma ya kasa jefawa Allah ya kiyaye shi da zama Mummy,Chika tace ni ance Maka ciki ne Dani to,shine mana Aunty tun yaushe kuma an gamu,Chika tace dan Allah tafi ka siyo min kafin ka dawo na hada ma abincin,ni yau bana Jin yunwa abin dadi kawai zaki hada min Inci,Yana fita bai dade ba ya siyo mata ya kawo,ta kawo Masa su fruits salat ya sha hadi,ta kawo Masa wata samosa me dadi taji hadi ga nama a soye,ya zauna Yana cin abinsa hankali kwance. Suna ta hira da Chika,Chika tace wai Arham kai baka da budurwa ne? Yace Ina maraya wa zai min aure ni,in kayi budurwa ai kana da kudi har yanzu fa ci da ni ake ko kaina bana iya ciyarwa ta ya zan zauna Ina budurwa tace kudin anko bani da Sisi,tace Data Ina fama da tawa bada ni ba,Chika tana dariya tace haba Arham Ina ganinka babban yaro,yace uhm in munga hadaddiya sai dai nace Allah ya azurta mu amma bazan tare ta ba. Yau da yamma za a Kai Hidaya gidan miji,tun safe take kuka tunda gari ya waye take kuka,wajen Azahar Abba ya shugo gidan,Kubra tace wai yarinyar nan har yanzu taki hakura sai kuka take anyi lallashin anyi taki hakura,Abba yace rabu da ita idan ta fara ciwon Kai taji wuya ta daina ko shi Angon ai zai lallashe ta da Hallare lafiyayya rabu da ita Dan Allah karku sake cewa tayi shuru,Kubra ta dinga dariya tace kaima dai Naila ta koya Maka wlh,yace ni ta gado na Dade da sanin ana kiranta Hallare ke ma kin sani ke da yarenki zaki dinga wani gulma,Kubra tayi murmushi,wajen su Goggo Abba yaje,Goggo da Tani sun dawo,Yana shiga suka gaisa yace barkanku da zuwa,suka ce yawwa yace Amma zaku je ku gano Naila suka ce Inshaallah zamu je mu gano ta. 6pm su Haidar suka zo daukan Amarya a motoci ,kawayen Hidaya kamar yayi sun Sha anko,kawayen Kubra da danginsu na kauye,Amarya wacce ta Sha gyara taci kuka ta gaji ta shirya cikin wani Leshi white and Golden dan gaske da Naila ta dinka mata gown ce hadaddiya daga baya har kasa take ja,da kyar ta tsaida kukan aka mata Yar make up sama sama sannan aka tafi kaita dakin miji,Abba ya riga ya mata nasiha tun jiya shi yasa yau ba a tsaya ba. Habiba da tawagarta suna nan suna jiran Amarya Ango Kuma Yana gida a sama bedroom dinsa ya fito ta corridor din baya Yana hango motoci an bude gate Yana Jin dadi Yana kallo ta samansa. Amarya aka fito da ita Haidar ya kira a waya ya daga yace ka ganni a sama Ina Kallo ya ka gane min Amarya ta? Haidar Yana dariya yace Amarya fa ta karo wulakanci irin kyau haka wlh ban ganeta ba,yace ni dama nasan haka zata dawo sai taji wukar yanka balangu ma tukun,Haidar Yana ta dariya yace ni kuwa yar Kunkumar tawa munyi fada dama kawu bai sonta na tsine mata na koreta,dariya suka yi masu kai Amarya tuni suka yi ciki da Amarya,su Habiba suka sauke su hannu bibiyu da karramawa,Nabeela da Rahma suna can gidan Amarya su suka gyara komai na gidan,sai da suka yi sallar Isha sannan suka tafi da Amarya hadadden gidanta,su Goggo suna ganin gida suka dinga cewa lallai Hidaya ma anyi dace,shi dai Hashimu Allah ya Cece shi,Hidaya tana ta kuka an Rabata da iyayenta,tunda taga an fara watsewa ba kowa sai Goggo da Tani ta rike Goggo tana rusa kuka ni a Maida ni gidanmu....wayyoo....Umma ta....Abbanaaaaa....Goggo ta fisge jikinta suka fice a bar Hidaya tana ta faman kuka,Wanda zasu zauna ma a wajenta duk Goggo taje kowa ya tafi tunda baza ta yiwa mutane shuru ba,suka kira Ango Goggo tace kaje yanzu mu Kam mun tafi tana nan tana ta rusa uban kuka wala'allah Kai ka iya lallashinta ta yarda,yace to bari naje,lokacin wanka yake niyyar yi ya fasa ya kira Haidar yazo ya kaishi can. Goggo tace Naila kuwa tafi dadin sha'ani wlh muka kaita cikin Jin dadi ba kuka ba komai har muna ganin laifinta ashe gwara ita wannan jarabar kuka haka,Kuma yau dai ba kyaleta zaiyi ba,Tani tace Ina fa zai barta ai in zata tsage bazai barta ba sai dai idan suma take,Ina Tausayin Hidaya yarinya ce sosai,Wannan yaran da kike gani ki kiyaye su cewar Goggo. AsmaBaffa [2/8, 8:18 PM] AsmaBaffa: TANTIRIYA A GIDAN YARI BOOK2 ~YARAN JAURO~ 106-110 Official AsmaBaffa SADAUKARWA NE GA AIDA MAMAN TASNIM Page naki ne Umu Afrah Bayan sun koma gida suka samu Hashimu su Goggo suna bashi labarin irin kukan da Hidaya take yi,Hashimu yace duk da haka bata Kai uwarta ba lokacin da tana Amarya,Yar Inna tana ji ta bata rai bakin ciki ya dameta na Abba,suna hada Ido ta Harare shi yace to nayi shuru Harara ta take,Goggo tace Hashimu ai Kai sai gyaran Allah kuma wai ya Kasuwar taka ne? Hashimu yace idan naga dama Ina fita so nake na canja sana'ar masu gidan sunki yarda,bana son wannan wlh ace mutum kullum a runfa Ina laifi a canja min shago cikin sutura,amma Ina rumfa iska ta ko Ina kawai shiga jikina take ba birki,idan shago ne fa sai Yar kofa ta,sai na samu Yar katifa ta a gefe in na gaji na kwanta na huta,ni gaskiya canjawa kaina sana'a zanyi,kayan masarufi zan koma siyarwa kwana Nan,Goggo tace indai zaka yi sana'ar ai Alhmdllh,mu zaman banza ne bama so dama,Abba yace Ina nan dakin nan na gidana Wanda kofarsa take a bude shi zan Maida shago kawai,Goggo tace Allah ya kawo kasuwa. Hashimu yace Tani wai ya naga duk kin Kara fita a hayyacinki ne? fatarki duk tayi yaushi ki dinga Shan ruwa sosai fa da Dan Glucose D ko Kya farfado,wannan irin yangwadewa haka,ga farin naki ma ke ba me kyau ba,irin farin nan hauuu,Tani tace Kai fa ka fiye sa Ido a haka kace baka gulma,Hashimu yace wlh sai na siyo miki ruwan gishiri da sugar kin tafi da shi ki dinga Shan ruwa sosai fatarki ko a samu ta mike. In kunje