Sashe 62
Tantiriya A Gidan Yari Book 2 Complete Hausa Novel · about 1 min read
itama Yar kadan sai lipton da kudi dubu ashirin inji Spark yace gobe za a kawo muku bread da safe,Mima tace da me kawo sako kace nace Kutmar ubansa ni zai kawowa geron Koko da garin semo,an fada Masa Ina Shan Madara Yar awo,Arham ne ya fito yace laaa mudai a tuka mana tuwon mu sai mu basar kawai mu cinye,Wallahi basarwa kawai zanyi naci,ga kudin cefane ma sai ayi mana miyar kubewa,Kai Dan sako jeka kace an gode Allah yayi Masa Albarka cewar Arham,me kawo sako ya tafi. Mima ta Kalli yaran gidan nata kowacce sai hamma da yunwa tausayinsu taji ba shiri ta shiga kitchen ta fara tuwo zuciyarta tana tafarfasa kawai,haka tayi musu tuwon semo miyar kubewa sabo da yunwa suke ji harda side hannu,Arham ya zubo nasa yace Miya taji daddawa gobe a aike ni na karo wata,Mima kawai hararsa take yi,Shahid yace mutanen da sunyi gaskiya tuwo yayi a rayuwa. Su Haly dai sai side kwano ake yunwa zata halaka su. Tace ku gama da yamma mu tafi gidan Rafeeq da Misam ke Anam Haly da Mufee ku shirya muje sannan mu biya gidan Spark yaci kaniyarsa.