Sashe 28
Tantiriya A Gidan Yari Book 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
tayi aure tana da tarin samari Allah ya bata farin jini,ta yi yayin tara samari,taci kudin wannan ta yaudari wannan,taci kudin waccen,bata iskanci amma tana bari samari suna latseta kamar yanda kike yi yanzu Rahma,ni nasan gado kika yi,sai da ta gama yaudarar samarinta ko wanne tayi Masa alkawarin aure amma katsam sai akaji ta auri wani Attajiri Alhaji Yusuf, a cikin Samarinta akwai wani Aminu,talaka ne sosai ya sota tsakani da Allah,Yana make make da buga buga ya samo kudi duk ita yake bautawa da iyayenta,tun tana karama yake sonta,shine kudin makarantarta cinta da Shanta komai Aminu Yan gidansu,sun Maida shi bawa,amma bai sani ba ya tafi neman kudi Lagos,ya samo kudi yazo zaiyi gini ya aureta kawai ya samu labarin ai ranar ma za a kaita dakin miji an daura mata aure,Aminu ransa ya baci matuka ya gaza hakuri. Ya samu Yan daba da makamai ana Kai Amarya daren farko Bushra Angonta ya shugo suna hirar soyayya kafin a fara sunna,Aminu da abokansa suka Fado dakin da makamai,suka yiwa mijin duka suka daure shi itama Kuma a wajen Aminu yayi mata fyade ya sadu da ita a gaban mijin suka gama suka fice abinsu,Rahma tace Aminu yayi daidai,ni kuwa banga laifinsa ba an cuce shi,Abba yace yi shuru Muji,Jauro yaci gaba,tunda Aminu suka tafi sai mijin Bushra ya tsaneta kamar ma da saninta aka mata haka,ya dinga gallaza mata Yana gana mata azaba,tayi kuka ta gode Allah tayi nadama,tasan ita ta jawa kanta,tunda ya aureta bai taba saduwa da ita ba,aure ma ya Kara ya rabu da ita ta zama Yar aikin gidansa,ciki Yana fitowa ya tabbatar cikin Aminu ne, bai sake ta ba yaci gaba da gallaza mata. Ni business ne ya hadani da Mijinta har muka Saba yake bani labarin komai,nayi nayi ya hakura ba laifinta bane yace Sam shikam ya sake ta ma,ni kuwa Yana sakinta na dawo da ita gidana da sanin iyayenta,a garin da nake Kuma nace ai aurenta nayi alhalin ba aurenta nayi ba,har Allah ya sauketa lafiya ta haife ki na saka miki Rahma,lokacin haihuwarki Allah ya azurtani har sa na yanka,Ina fada miki a karshe dai Aminu da kansa hakki ya bisa ya dinga nemanta ruwa a jallo. Ni na sasantasu da danginsa da na Bushra ya aureta suna zamansu yanzu yaransu Shida,sannan mijin Bushra da ya gallaza mata sai bayan tayi aure ya dawo nemanta lokaci ya kure Masa Kuma. Rahma tace Kawu ai Nima watarana kace na rakaka unguwar ka kaini wani gida sau Daya yace sune iyayen naki,Rahma tace wlh muna kama da Bushra din Kuma haka kawai naji Ina ta kaunar Bushra,Abba Dolo yace uwaki Umma zaki ce,Rahma tace amma ba ace itace uwata ba sai aka ce ta mutu,Jauro yace ita tace kunyarki take kar a fada muku. Bari muzo kan Iman,Iman Mahaifiyarki ke Mahaukaciya ce,sanda muna zaune a Jigawa,a titi take tsince tsince a bola,mahaukaciya ce ta gaske,duk mutane da dama sun Santa kyakyawar mace ce fara amma ciwon hauka yasa ta koma baka amma da yanayin gashinta ya nuna Buzuwa ce domin da buzaye tayi kama yanda kike me gashin Larabawa haka take,fara ce itama duk da ciwon haukar bai Hana a gane b,to a kwana a tashi ta koma wani kango da kwana,akwai wani Hamshakin Attajiri da yake zuwa daga Sudan,ance gidan da yake ginawa ma a lokacin kangon nasa ne,Yana zuwa ganin aikin ginin,daga baya sai aka ga yana daukan mahaukaciyar a mota,za a ga ya fito da ita a sume alamun ko wani magani yake shaka mata sai ya dakkota ya dinga fadawa mutane da larabci bata da lafiya asibiti zai kaita sai ya fita da ita,ana haka haka katsam sai ga mahaukaciya ta fara laulayi,ciki ya fito ya girma ana ta Jin tausayinta,sai da mutane suka fara zargin Dan Sudan din sai kawai aka ga ya siyar da gidan da yake ginawa ba a sake Jin labarinsa ba har gaba da yau Iman ban San waye ubanki ba,Mahaifiyarki Kuma haka cikinta ya tsufa ta haihu a Jikin gidana,muka fito da Habiba Jin hayaniya ana cewa mahaukaciya ta haihu,Habiba ta gyara mahaukaciyar tsaf tare da taimakon wasu mata Yan unguwar, ana tunanin ya za ayi da yaro Habiba tace tana so nace mu dauka muka dauki yaro sannan ita Kuma Mahaifiyarki na dauketa na kaita gidan mahaukata sabo da gudun kar a saceta ko a Kuma yi mata wani cikin yanzu mutane basu da Imani. Kinji Iman yanda kika fito Mahaifiyarki tana Nan tana ciwon hauka,amma tabbas waccen Dan Sudan ana da tabbacin shi yayi mata ciki,Abba Dolo yace Allah ya bayyana gaskiya. Annoor Kai Kuma kasan Mamanka ai kana yawan zuwa wajenta a Nan Kano,to bari kaji Kai Allah ya tsallakar dakai Kai Dan sunna ne Kai kadai ne,Mahaifiyarka Almajira ce da, sadaka yalla ce take bara, tace itama tashi tayi da iyayenta ta ganta a Nigeria amma ba Yan kasa bane suna da asali,talauci yasa take bara suna cin abinci da iyayenta har iyayenta suka rasu,a yawon bara ta samu wani Usman ana ce Masa Shegu,asalin Dan sokoto ne,Yana dan kasa yalo a titi,Abba yace ya Sunanta? Jauro yace Jumana,Jimina? Abba ya sake tambaya, Jumana nace cewar Jauro,Jumana ta aure shi bayan ta aure shi da Shekara ta samu ciki Ashe baya son haihuwa,sai daga baya taji labari Ashe auri saki yake duk Wacce ta samu ciki tana haihuwa zai karbe dansa ya saketa ya barwa uwar gidansa Dan,Jumana kuwa bai saketa da wuri ba amma ya gallaza mata,ita take ciyar da kanta da komai,da ta haifeka yace ba dansa bane,juyin duniya yace ba Dansa bane baya so,Mutane suka buga aka buga da danginsa da kowa yace Sam shi ba dansa bane. Aka kaishi Kara kotu a kotu ya amsa dansa ne amma ana fitowa yace wlh ba dansa bane, ba ya so bazai karba ba sabo da ya ga Jumana bata da gata bata da kowa,sutura sai wani me sai da gwanjo ne ya bata sadaka ta saka maka,da kanta ta rada Maka suna Annoor ba hakika ba komai,a haka take goyaka Annoor ta tafi bara ko sati bakayi da haihuwa ba take bara da Kai a titi,aikin gidaje ma ta rasa sabo da kyawunta babu matar da take daukanta aiki kar ta aure mata miji,wani ne ma a haka ya bata gidansa da bai karasa ginawa ba iya rufawa kawai aka yi a ciki take kwana tare da kai. Mace ce me hakuri da addini,ta tsare mutuncinta Maza suna yawan zuwa zasu lalata ta su bata kudi taki yarda,akwai masu kudin ma da suka ce zasu Gina mata gida ta amince da su amma taki yarda,tana Tara kudin barar ta sai ta koma saro masara danya tana gasawa a gefen titi a haka take ci take Sha,sabo da kyawunta ita duk Yan banza ke zuwa nemanta,da masu sonta don sha'awa,lokacin da me gidan yazo ci gaba da gininsa yace tayi hakuri ta bar Masa gidansa,ga lokacin da damuna ana ruwa da dare haka ya korota,ta goyaka ta lulluba Maka tabarma tana tafiya ruwa na dukanta tana rusa kuka,ta samu Jikin bishiya ta fake,ni Kuma na zo Kano wani Business nayi dare Ina sauri zan tafi Jigawa, ga lokacin Habiba ta Murda kambunta tana masifa na Dade ban dawo ba nayi sati biyu a Kano ta gaji da kewa ta ko ba haka aka yi ba? Abba yace haka aka yi ci gaba muna ji,Jauro yace da Kai nake? ko kasan lokacin ne Kai,ni wallahi ka dameni wannan wacce irin hayyata ce,Habiba taji kunya tace lokacin ai da kuruciya,Jauro yace sarkin tsufa ke dai kawai kin girma kullum kin girma haba,Abba yace ke haka ake yi ai sai kice yanzu ma wlh in ta kama Murda kambun zanyi,amma sai ki wani ce ke kin girma shi yasa nake Sarawa Kubra,Yar Inna duniya Labari. Jauro ci gaba yayi yace daga nan na hango mace ita daya kwal a gefen titi a Jikin bishiya,na zaci gamo nayi sabo da kyawunta ya tsoratani,Annoor kayi hakuri naso nayi wuff da Tsohuwar ka na Dade Ina sonta sorry Habiba ranar wanka ba a boyon cibi,itace tace baza ta iya kishi da Habiba ba tayi mata halacci baza ta auri mijinta ba,na buga na buga taki yarda,ai Habiba boye miki nayi amma sai da na dinga zuwa zance,Baki gani ba Ina yawan siyo mata ice cream,Habiba tace ai nasan kana sonta Malam tun yaushe ta fada min a boye tace kar na fada,Abba yace kinyi gulma Habiba kunyi munafunci ai sai ki fada Masa mijinki ne fa,wato ta zama kawa mace tafi miji ko? Habiba tace ni nace kar ya aureta? ni bazan ce ayi min kishiya ba amma in ya auro maraba bana ja da ikon Allah. Hashimu yace karya kike Habiba da wata a kasa,Jauro ka kiyayi Habiba irin kishin karkashin kasa suke yi irinsu,Jauro yace duk ita ta korar min mata,Habiba tace ni a wa tab ka auri dubu ma wlh,Allah sarki Jauro ba a sonka ba a kishinka da ace Yar Inna ce ai yanzu ta fashe min da kuka daga nan Kuma fita ma baza a barni ba kullum sai lallashi,in mata danwake,in mata kunu,in soya mata kwai,Jauro yace kayi asara Hashimu,Habiba baza ta barni na shiga kitchen bama sabo da kauna,Abba yace baka San soyayya ba an barka a Tsohuwar kwalta kana garari,Yaran Jauro sai dariya suke babu shiri. Jauro labari yaci gaba yace Dana kawota gidana,na yanka katon raguna biyu na hakika dama ta sa Sunan Danta,Jumana mutuniyar arziki anyi zaman mutunci da ita har ta yaye Annoor,nayi nayi ta aureni ta ki sabo da a lokacin ta zama kawar Habiba duk da Habiba ta girmeta nesa ba kusa ba,wani me kudi ya fito Yana da mata uku amma baya haihuwa ta aure shi taje a ta hudu, Bata haihu ba kawai matan Nan suka hade mata Kai sai da aka saketa,bayan an saketa ta dawo gidana kana karami lokacin Annoor,daga nan na Kuma cewa zan aureta, na Kai hari na biyu tace a'a ita Habiba kawarta ce amma tana so na,karshe ta sake samun wani me kudi matarsa daya,tun kafin ya aureta yaga me kyau ya siya mata gida me kyau a nan garin Kano ya bata kyauta,bayan sunyi aure Allah ya Masa rasuwa,da akazo