Sashe 42
Tantiriya A Gidan Yari Book 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ne a dangi,Kai kanka ka sani da bana aurenka wlh basu Isa ba duk bani da karfi kasan Ina da hanyoyi,wlh tunda aka zagi iyayena bazan yarda ba, Spark yace rama to zagi nawa,shuru tayi tace dan kasan bazan iya bane ai har abada bazan zagi Iyayenka ba,yace to Kuma mene na fushin? Indai hakuri ne kamar sunzo sun baki har gida,Naila tace yawwa Kuma sai sun gyara min gidan nan tas ayi sauri kar ya huce a hakura gwara yanda suka min na rama da duminta,suyi min wanki da guga,yace to shike nan? Wanne shike nan ai sai na gani a kasa,yau ko bed baza mu hada ba,Spark yace uwarku su Anam Yan iskan yara sun jawo min masifa,saura kadan Naila tayi dariya tace nidai na fada Maka ehe,Spark abincinsa ya ci ya kalli Naila yace zanyi kuka,kayi na jini ma haka nake so. Yana gama ci ya tashi yace zan fita yazo ya mata kiss ta boye fuskar ta da sauri,tace aje wlh a Nemo min hakkina idan ba haka ba zaka dade kana bacci kai daya,ya fita kawai,tace haka kawai a dinga zagina,Saida taji fitar motarsa tace Dan uwanki yana more ni,Mima nan wlh da ace ba mijina bane danta sai na bata fitsarina ta shanye lutuwar banza. Spark gidansu ya wuce direct ya tambaya Ina Papa? Me aiki tace Yana part dinsa yanzu ya dawo,part dinsa ya nufa ya shiga ciki,Yana Shirin shiga wanka Spark yayi knocking,come in ya furta,ya shiga tare da sallama,Papa yace Spark wannan suna naka to shike nan da wani ya fada a banza ai gwara Nina na fada ni da na haifi abina,dariya Spark yayi yace General,yace gidanku ka rainani,Spark yace kune Mazaje Papa,Allah ne yasan muguntar da kayiwa mutane tun Kana yaron Soja zuwa yanzu,Papa yace bayan Kai ka gudu,Misam ma kamar abin arziki daga zuwa training ya gudu,Arham ne kamar zai iya,amma shashasha Rafeeq shi ko gwadawa ma baiyi ba,wai Ina ya shiga ne? Spark yace danka ya girma aure zaiyi fa ya tafi zance Kano. Papa ya zaro ido yace Rafeeq din? shi fa yace duk shegiyar data kalle shi bai yafe ba,to yayi budurwa Kuma aure zaiyi,to ai bashi da gida,Spark yace ai na Gina Masa tare aka fara ginawa da nawa amma nasa yanzu an karasa,Papa yace wow Allah ya muku Albarka Allah ya Kara zumunci,Allah ya muku Albarka,Misam fa yazo rannan yace min wai ya shiryu yabi Allah ya daina yawon yazubar,dariya suka yi,yace wai ya samu mata za a kai kudi gobe ko,Spark yace ae Inshaallah. Spark yace Papa Kara fa na kawo maka,yace to Ina jinka,ya gyara zama a gefen bed din Papa Inda suke zaune yace Anam da dukkan yaran matan gidan nan ne,suka samu matata suka mata dukan tsiya suka fasa Mata hanci irin Jinin da ya zuba Allah ne ya sani,ba abinda ta musu kawai sabo da taje dubiya,ba dama ta shiga dangina sai zagi da cin mutunci ya biyo baya,wlh Papa har su Mummy gaba dayansu sun hanata Shan ruwa,suna kiranta da Yar talakawa,har iyayenta suke ambata suna zagin iyayenta,badan Allah ya kawo ni ba da yanzu sai dai mummunan labari,wata da ludayi,wata da tabarya,wata da plate,wata da muciya sun Hadar mata,duka, zagi, Mari ,rankashi, yakuchi etc a gaban su Mima,suma suna zaginta Papa. Kuma kar ka ce yaune tunda na aureta ai kasan case din sabo da kawai ban auri Wahida ba,Papa yace in kaso ma yi shuru Ina jinsu suna gulmarta kullum suna zaginta,Spark yace nafi so Papa a hada min su a Guard room su yaran a sa sojoji su Zane min su sannan su farfasa musu jiki yanda ko a hanya harararta ma baza su sake ba sannan suje har gida su bata hakuri suyi mata aiki,Papa yace Kai da na baka securities sojoji ka basu aiki mana amma kar ayi musu Wanda zai musu illa,Spark yace ai dama zuwa nayi na fara fada Maka kar kaji labari baka sani ba ranka ya Baci,yace yi maganinsu dama sun ishe ni da rashin kunya,amma Banda mazan ko? Ae mazan ba ruwansu iya matan ne,Spark yayi godiya ya mike yace Papa Mima ma da zaka sata a guard room da kanka ai da yafi ka gana mata azaba,Papa yace Matar tawa? Wato Kai matarka itace mace ni tawa ba mace bace get out,Spark yace wlh ni da za a sa Mima a guard room murna zanyi har ma sauran Yan uwanta. Spark Yana fita ya kira Arham a waya yace tattara kan yaran gidan Mummy har Anam kaf yaran gidanmu har Wahida ka dakko su a Mota kace Papa na son ganinsu yanzu,idan ka kwaso su ka kawo su gidana karka tsaya sai ka kawo su,Arham yace an gama ai gwara aci Ubansu. Arham Yana shiga gidan Mummy wayo yayi da dariya da wasa yace Papa yace kuje gidan zaiyi baki sojoji yace a kaiku gaba daya abokansa zasu ganku ku yaransa duk su Misam suna can,Anam tace Allah yasa mu samu kudi ta zaro mayafi,sauran Yan matan duk suka taso su hudu,Wahida tace muje nima can zan kwana yau suka tattara,Mima tace ku gyara min bedroom dina suka ce to. Mota suka shiga,Anam tace ai tayi mana kadan a dakko Jeep din can mana yace wata ta hau kan cinyar wata,yanzu fa zamu je,haka suka gamutsa suna ta labarin yanda suka ci uban Naila suna shewa da murna. Basu lura ba sai da aka bude gate din gidan Spark sannan suka ankare,tun anan suka fara salati,haly tace mun shiga uku gidan Spark,Anam tace wayyo Mima Kunga sojoji,suka ga sojoji cikin gida,Anam tace Ina da karamin ciki,Wahida a tsorace tace nima an min cikin shege,Arham Yana dariya harda yin wakar sojoji,sojoji mata da Maza da manya manyan bulalai,suka bude motar suna muzurai come down....Anam ta fito suka rufe sauran a mota mutum daya nema ya dinga zuba mata bulala kamar ya samu dutse,ihu take da kururuwa tana burburwa,Kuma yace tana sosawa ta zube,Spark Yana wajen sai da tayi kamar zata suma yace a kyaleta haka tana da aure wai a haka an raga mata. Aka fito data biyu Wahida tuni ta fara kuka tana cewa wallahi na daina Spark bazan sake ba Dan Allah Kai min rai uwata tana gidan yari,yace amma kin iya zagin matata sa'arki ce? Ku cika mata aiki wani ne ya karbi bulalar ta ko Ina zuba mata yake Jikin duk yayi rudu rudu ba mutunci ihu take tana kururuwa,Naila kukan da take ji ne yasa ta fito waje da sauri ta samu ana jibgar Wahida. Dariya ta dinga yi harda waka Dan Soja tashi sauke farali,Sai da Wahida ta fara shidewa akace ta fara tsallen kwado ita bata da miji,wata Soja ta zuba mata bulala tace start....ta fara tana kuka,Haly jiki na rawa ta fito itama kafarta kasa daukanta tayi harda fitsari a wando ta fado macece Soja ta zaneta ga mata ba tausayi tafi kowa Jin jiki,sannan aka fito da Ilham da lisa suma sunci ubansu duk na karshe ma sunfi Shan azaba aka sasu tsallen kwado banda Anam tana da aure ita. Naila tana gani tace a barsu haka suzo suyi min aiki,Spark ya sallami sojojin yace ku taso wlh ko na chasa ku da kaina Kuma Kun San nima Soja ne Allurar nan ta sojoji tana Jinina bani da mutunci wallahi dukan da zan muku yafi nasu Yan iska marasa mutunci,ko yayyena sai na Zane su akan yi min kasassaba da aure na,bulalar ya karba wajen masu gadin gidansa,suka shiga ciki da gudu suna kuka. Naila tana zaune a Saman kujera ta harde Sanye cikin bum short da Yar riga ta cire Hijab din data fita da shi,sai kallon jikinta suke yi ba karya tayi ta ko Ina,Anam tace a ranta dole Yaya ya haukace. Arham shi yayi tafiyarsa dama tuni,Spark a gaban Naila ya duka kadan fuskarsa saitin tata harda dafa gwiwarta yace Baby Allah ya Kara girma me zasu yi miki,Naila tace su share ko Ina da suyi mopping Banda bedroom dinmu,Spark yace Kai ku tashi Yan iska marasa tarbiyya,suka tashi da gudu yace ku fara aikinku,har sun fara Naila tace Kai ku barshi ma ku tafi ku bar min gida bana so kar a lalata min kayan gida,Haushi ya kama su dama burinsu su farfasa abubuwa me amfani a gidan su cuceta sai gashi kamar ta sani ta hana,yace wanki da gugar fa? Naila tace na fasa kazamai ne ban yarda da tsaftarsu ba,wani haushi kamar ya kashe su Anam,Anam a ranta tace wlh zaman gidan nan sai ya gagare ki. Spark yace ku bata hakuri abinda kuka mata ku durkusa har kasa,ba musu da sauri suka zube a gaban Naila suka ce kiyi hakuri suna Jin kamar su kashe ta,Naila tace kanku kuka yiwa ba ni ba,Kuma iyaye na Dan Kun zage su naku kuka zaga,sannan ni Allah ya kiyaye na zagi iyayen ku ko ba komai Ina auren Dan su,sannan Kuma manya ne akan me zan zagi babban mutum Ina da tarbiyya,Kuma Dan Kun min Kuma mata ne za ayi muku,ku auna abin a kanku ace kune a gidan miji danginsa ke muku haka,Anam ke kina da aure amma kin bani mamaki da baki da hankali. Dangin Miji kema kina da su fa,wulakanta Dan Adam ba daidai bane Kuma wannan rashin Ilimi ke damunku da rashin mu'amula da mutane sai iya family dinku,abinda kayi kaima za a ayi Maka wlh,ku sani ba yanda zaku yi dani,Dan uwanku na riga na aure shi mun hada jini. Ku Wannan tunanin ku Kuna kaunarsa? bakwa sonsa tunda bakwa son abinda yake so,wannan shashanci kuke yi sabo da Kuna da kudi bakwa tunanin mahaifinku shine gatanku a yau ya Fadi ya mutu baku da wani gata wlh,kunkuni suka fara,Naila tace ke Wahida ba dake nake ba ba ruwana dake kin ma girme ni sannan nasan dalilinki na miki uzuri,amma ki sani bana tsoron ku wlh ko kadan,na fiku iskanci,a iskanci baza ku kama kafa ta ba,amma a sannu ana nan bari gaskiya tayi halinta zaku San ni ba sa'arki bace a iskanci,idan Kuna tunanin ku Yan iska ne nice iska uwarku da kanta,nice Iskar da kanta, na saita ku a layi ba duka ba zagi ba komai bane a wajena,magana daya idan na fada sai Kun Shekara Kuna