← Book details Tantiriya A Gidan Yari Book 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 78 OF 87

Sashe 78

Tantiriya A Gidan Yari Book 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

AsmaBaffa [2/5, 10:44 PM] AsmaBaffa: TANTIRIYA A GIDAN YARI BOOK 2 ~YARAN JAURO~ 96-100 Official AsmaBaffa SADAUKARWA NE GA AIDA MAMAN TASNIM PAGE MA NAKI NE AIDA MAMAN TASNIM Tana fita Annoor ya ja wawan tsaki ya zauna,kiran Iman ya gani,wayar ya daga a fusace tace Beb,wane Beb din? Iman tayi murmushi tace wai ba Beb bane,tsaki ya ja tare da kashe wayarsa,Iman tabi wayar da kallo tace a'a to ni me nayi yanzu fa ya bar gidan normal,sake kira tayi yana kallo yaki dagawa,Maryam ya kira yace ta zo,da sauri ta shugo tana rawar jiki dama gata lukuceciya,kujera ya nuna mata tare da furta sit,zama tayi da sauri kallonta ya yayi shi sai yau ma ya kalleta sai yaga ta Masa kyau ta birge shi ma gaba daya,tana zaune bata ce komai ba farin ciki ya kamata tana ta murna,a ranta tace aiki ga me kareka da na tsaya wajen wasu banzayen malaman soro,aiki sai arna wlh. Iman ce ta sake kira ya danna reject,Iman tace Kai ai nasan Office din wlh bari naje ko ba izininsa me na Masa,bazan iya jira ya dawo ba" ni ba me hakuri bace ,ta shirya tare da saka Jilbab dinta ta kira driver tace kaini Hospital din Annoor. Maryam kuwa hannunsa ta riko taga bai kwace ba Kuma baiyi masifa ba,ai shike nan ta fara Murza hannunsa tana shafawa,ba uwar da yaji na feeling bare ma ya kawo,tana wasa da hannunsa tace ko baza ka aure ni ba zan baka kaina a haka,burina ni ya cika ko iya haka tana magana a ranta sabo da har yanzu tana Jin tsoronsa,shi fuska ba annuri kawai Ido ya zuba mata,Iman ce tayi knocking amma ba Wanda ya kulata ta turo kofar ta shugo,tana shugowa ta ga Maryam tana Murza hannun Annoor Wanda yake rike da biro da dayan,Juyowa tayi taga Iman tana gani taci gaba tace my love yau she zaka kawo kudin auren namu? Iman tace auren uwar wa? Ke me zan gani, tasa hannu ta fisge hannun Annoor tace Shegiya mayyar Maza dama irinku ne masu lalata Maza, karya kike wlh Annoor ba abinda zaici da ke,ko aurenki zaiyi wlh nasan to ba lafiya ba,Maryam tayi wata dariya tace kisa Ido ki gani ko dukana zakiyi ne,ke Nan har macece? Iman shake Maryam tayi suka dinga kokawa,Dake Maryam tana zaune ta Mari Maryam har sau biyu ta tuge mata mayafin da dankwali gashinta ya bayyana ba laifi tana da gashi Maryam,da kyar Maryam ta samu ta mike,Kafin ta daidaita Iman ta hankada ta Saman table din Annoor, Maryam ta saki Kara kanta kwam ya bigi Leben Annoor da ya saki Baki Yana kallo, Lebensa zafi ya zaci ma ya fashe,Iman ta haukace Bata ganin kowa Yana ta mata magana bata jinsa ma fridge ta bude ta zaro kwalabar lemon grape wata katuwa da lemon a ciki ta nufi Maryam zata buga mata,Annoor ya riketa,Yana cewa zan mareki Iman me ya kawo ki nan?kwalabar ya kwace Maryam ta fice da gudu ta bar Office din. Iman tana haki da jijjiga tace wlh idan baka rabu dani ba zan kwashe ka da mari,Ido Annoor ya zaro bai ma San sanda yayi murmushi ba yace ni din zaki mata? tace nawa kake wlh marinka zanyi,ta hau searching Office,ta bude corridor ta dakko tsintsiya,yace kizo ki tafi gida,Iman tace sai na duba Office din nan ko laya aka makala Maka,ni dama Maryam din Nan bana kaunarta bana sonta,bani da makiya kamarta Kuma haka kawai ba abinda ta min kawai na tsaneta ban yarda da ita ba ni" Iman ta hau shara ta durkusa ko Ina tana Searching Yana kallonta yana dariya,Iman ta gano Dan Abu kamar kwallon charbi ta dakko shi tace sai naje naji fatawa a kansa wannan ma ban yarda da shi ba,tana dariya ita kanta wasa ta dauki abin" hand bag dinta ta bude tare da sakawa a ciki ta zuge tace tashi mu tafi gida,Inzo aiki kice in tashi mu tafi,kalau kike kuwa?,Iman tace Dan Allah taso ta marairaice,wata kasala yake ji dama ba uwar da zai iya kawai yazo ne,hannunsa ta rike tace muje to wannan motar sai dai driver ya kawota gida anjima,suna tafiya suka fito Maryam bakin ciki ya kamata ganin ya yarda yabi Matarsa,haushi ya kamata ta leko da kanta kanta kadan tace solobuyo, Dolon miji,Iman ce ta ji ta juya Bata ga kowa ba suka ci gaba da tafiya Maryam ta sake lekowa tace Rakumi da Akalaaa.....tayi wuff ta buya,Iman bata ko juya ba har suka Isa wajen mota ta bude Masa ya shiga ta shiga itama ta zauna driver ya ja suka tafi,tunda suka shiga mota Annoor bai ce komai ba duk yanda suke wasa da Iman yau shuru. Kwanciya tayi a jikinsa yace a kaini wajen magani ba kalau nake ba,tunda naji Maryam tana birgeni wlh bani da lfy,Iman tun kafin na aureta nayi miki kishiya ki min magani,a yau nasan ba kalau nake ba ni dai,Iman tace ka auri wa? Daga auren mu sati nawa kwata kwata 2weeks kace aure,Iman ta fara hawaye tace ko ka aureta ba abinda zaka iya fa,Annoor yace ji nake idan ban aureta ba ban cika mutum ba,baki Iman ta bude tace a gaban nawa? Iman tace driver kaimu gidan Kawu. Suna zuwa suka samu Amaryar Kawu tazo gaida Habiba za a musu nasiha Abba yana nan yazo,Haidar duk suna wurin aiki ba kowa,Rahma suna school su,Kawu Yana ganinsu yace Iman lafiya naga kina kuka? Iman tana kuka tace ba dole ba Kawu tunda Kun zuba mana Ido kunki ku Nemo maganin gashi nan aure zai Kara wai,Abba yace Kai Dan ubanka ko Daya baka gama da ita ba ka tafi neman wata,Kawu yace dama zara ce da Kai na baka 'yata" daga aure shine zaka ce aure zaka Kara,Annoor shuru yayi dan gaba daya baya Jin dadin jikinsa. Abba yace ni dama ace dadin mace ya sani da sauki mace ai ya dandana yaji ne shi yasa zai karo aure ya Kuma dandana na wata yaji,Jauro ya furta gane min hanya,Maman Annoor dake zaune tare da Habiba ta Kalli Annoor tace baida hankali waye zai daura Masa auren? Marar mutuncin yaro Kai wlh ka bani mamaki ma,Habiba tace ni na taba Jin irin wannan ma sai yau Kai Annoor gaskiya ka bata wayon ka. Abba yace dama wani me yin kitso ne na kirki aishi daga an ganshi an San ba girma a tare da shi,daga ya daure gashi sai yayi kitso ana ganinsa anga Dan duniya,shi yasa tunda nazo zan daura aure naji gabana na faduwa nace to wannan auren sai abinda Allah yayi,Jauro yace to yanzu ni abinda na fahimta yaron nan maganin musulunci za ayi Masa,Iman Anya kuwa Kuna addua? Iman tana goge hawaye tace ae muna yi har Sallar dare da karatun Qur'ani shine ma watarana in na tashe shi muyi sai yace shi bacci yake ji. Abba yace wace yarinyar to? wata ce Maryam a asibitin sa take aiki. Ni ban iya bin malamai ba ku dage da addua da Azkhar cewar Jauro,Iman tace ni wlh ko baza kuje ba sai na Nemo magani Ina kallo na tsaya ayi min kishiya 2weeks da aure ai na fado haba kalleni fa wlh bazan yarda ba,Abba yace harda wallewarki Yar nan?banga laifinki ba. Annoor zazzabi ya fara ji harda rawar Sanyi yace in ban auri Maryam ba mutuwa zanyi zuciyata zafi take Kawu,suna ganin Abu kamar wasa sai ya zama gaske rawar Sanyi yake sosai,kujerar da suke zaune ya zame ya kwanta Yana cewa a kira min Maryam ko zanji dadi. Maman Annoor ce tace wannan abin fa ba na wasa bane Aunty Habiba,Iman ta fashe da kuka ta mike ta shiga bedroom tare da fadawa Saman bed tana kuka,Maman Annoor tace lallai ya kamata a Nemo Maryam don wannan wallahi itace ta yi Masa asiri,Annoor ta kalla tace kana da number dinta? Yana rawar Sanyi yace ehh...ya mika musu wayar,Iman ce ta fito da katon bargo ta lulluba Masa ta zauna a gefen kansa" kansa ya Maida Saman cinyarta ya kwanta Yana Nishi a hankali,Jikinsa ya dauki zafi sosai,Kawu yace Iman ku tafi daki ya kwanta,ta mike tare da rike shi ya tashi da kyar da bargon a jikinsa suka shige bedroom dinta na da" Saman bed ya kwanta itama ta kwanta suka shige bargon tare,Rungumeta yayi sosai a jikinsa Yana mata rada a kunne I'm sorry" Nima ban San dalili ba,Iman tana lallaba mijinta tace ko na cire kayan kafin Jin dumin?da sauri yace ae,tashi tayi ta sawa kofar key sannan ta cire kayan jikinta ta shige bargon tare da cire Masa nasa kayan ta rungume shi Kam" sosai shima ya makalkale ta. Maman Annoor ce ta kira Maryam ta zaci Annoor ne tunda da wayarsa ta kira,da sauri ta daga tare da furta my love,Maman Annoor tace ba shi bane Mamansa ce,da sauri Maryam tace Ina yini Mama? wai a dole ita ta gari ce,Maman Annoor ta furta Annoor yace Yana sonki shi aurenki zaiyi,gashi bamu sanki ba ko zaki iya zuwa mu ganki sai muyi miki wasu Yan tambayoyi, Maryam taji zancen aure tace to yaushe kuke son ganina? Yau ma in da hali ai akwai lokaci" okay to bari nazo,tace yawwa gidan Kawunsu ai kin San gidan tunda a karkashinsa kike aiki,Maryam da sauri tace to,Bayan sun gama wayar,Abba ya Kalli Jauro ya tabe baki yace baka iya soyayya ba Jauro Amarya guda tayi abin Azo a Gani maimakon kace ban mu kashe sai ka tsaya sekeke da Kai kamar bishiyar dabino,Habiba dariya ta dinga yi tace ku dai wlh baza ku girma ba,Hashimu Allah ya shirye ka,Abba yace Allah ya shiryeni wlh tunda ba Yar Wanda na lalata,Kuma gani da iyalina muna zaune lafiya har fada nake nema muyi ma ai kuwa ba karamin shiryayye bane ni,Maman Annoor tayi dariya tana dauke fuskarta sabo da Jauro ya kafe ta da Ido kamar wani maye. Jauro ya dawo tsakiyar matansa ya zauna Habiba a gefe Amarya a gefe,ya Kalli Habiba yace black beauty, ya Kalli Amarya Sadaka yalla wace ne zata kwace ni,Habiba tace na bar mata wlh har sati daya kwana,Abba yace ai baki birge ba Nan har kyauta kika yi Habiba,ke da zaki ce Jauro na barka kayi
Chapter 78 · 0% Book details