Sashe 51
Tantiriya A Gidan Yari Book 2 Complete Hausa Novel · about 6 min read
idan ta shiryu. Naila kuwa bata nuna ta damu ba sai ma kwantarwa da Spark hankali da take yi. Suna masaukinsu a kwance,tana jikinsa suna Hira kasa kasa yace Dan Allah Baby zaki iya yafe mata? Naila ta Harare shi tana dariya tace ni din banza ai ko sabo da Kai na yafe mata wlh da zuciya daya amma sabo da Kai,Ina sonka fa ta rainar min Kai na aureka kaddara ta kaini gidan yari badan haka ba baza ta iya kaini can ba,yanzu Baseeru shi dake bai da rabon wahala Kuma da tsawon ransa gashi ya Sha ras da shi,Kuma ni gashi Sila ta sa mun hadu na aure ka,badan haka ba Ina zanga me kudi irinka, ai ni Alkhairi ya zame min amma idan mun koma dole mu koma gaban hukuma a wanke ni fess sannan naje naga su Dan Indo da Goje su tabbatar,yace Inshaallah indai kin yafe ai shike nan,tace na yafe mata har abada sabo da Kai amma karka fadawa dangi har su Mima na yafe so nake suyi darasi pls,yace Inshaallah Yana murna ya rungumeta kamar zai cinyeta Yana sa mata albarka. A hankali tace Bado Yana bukatar Hallare,Ido ya zaro yace wannan son Hallaren naki kuwa na lafiya ne? Yau how many times muka yi karfa na koma Baseeru da Mummy,Naila tace Kuma wlh ba ciki bane ko ni Ina mamaki naje a asibitin sun min test sunce ba shi bane,naso ace shine na Maka surprise,yace Allah ya baki tace Ameen inyi nakuda ta in haihu,Spark yayi dariya yace ke Nakudar ma birge ki take yi? Naila tace sosai na dinga wash...ahhh Spark....bayana...kuguna...harda yin goho a Saman bed tace sai Da ya fado aji Inya Inya,ace Namiji ta haifa ko mace,Spark ya kama dariya yace haka fa kika yi a first night sai gashi kinfi kowa raki,Naila tace banda haihuwa,Kai yaro guda wasa ne Allah ya bani mace,yace masu Albarka dai,tace ko namiji ne ma Allah ya amfana Ina laifi,Allah yasa ya gado hallarenka matarsa ta kwashi dadi,Naila harda rawa da Kai ana Jin dadi sai Shoky ahhh....Spark dai Yana ta dariya Yana latsa waya,kwanciya tayi a jikinsa tana mika,wayarsa ya ajiye yace idan na kamaki Allah sai kin gudu yau,Naila harda adungure a Saman bed ai haka nake so yeee ai ni sai yanzu na balaga ashe,da ban balaga ba,sai dariya take ba Spark da gaske kullum Naila Kara fetsarewa take a bed,wani abin da take har mamaki yake. Nabeel ne ya tsiri zuwa gaida Abba duk bayan kwana biyu sai yaje,Abba ya gaji ganin yau ma ance yazo inji Nabeel,Abba fitowa yayi yace Kai idan kana da manufa ka fito ka fada sai kace Kaine Jauro sai sintiri kake,nema kake lallai sai kayi Aboki dani Kuma bazan zama abokinka,yau naji yaro Dan Albarka kullum sai kazo wajena na gaji,bana sonka da aboki ni karka ganni wani saurayi saurayi da shekaru na,Nabeel dariya yayi kyakyawa ne sosai,Abba yace yau dinma gaisuwar ce? Nabeel yace ae Kuma yarinya zaka turo min ta karbi sako,Abba yace ai Ina da yaro Aslam me yasa baza kace yaro ba sai kace yarinya,Nabeel yace to a turo Aslam din duk Daya ne,Abba ya shiga ya turo Aslam,Aslam Yana fitowa ya gaida Nabeel Wanda kofar motarsa a bude take ya fito da manyan Ledoji shake da kayan ciye ciye yace Auntynka zaka bawa, yace wacce a ciki? Nabeel yace Yar Kwaila dai gata nan wata kamar tana na manta sunanta,Aslam yace Zarah kenan yace ba ita ba ai na San Zarah yarinya ce sosai,yace Aunty Hidaya? yace yawwa ae ita,Aslam yace Kai kace mata Kwaila sai na fada mata,Nabeel yayi dariya a ransa yace yaro yayi gadon Ubansa,a fili yace to fada mata mana tsoronta nake yi,kace ta cinye idan ba haka ba Ina dawowa naji ance bata ci ba sai na balla ta,Aslam yace a nawa? Yaro da wayon tsiya,yace sa kudi yace dubu daya sai na Maka CID,yace yawwa yaro ya bashi 2k yace idan bata ci ba ka fada min,yace bani number waya zan saci wayar Abba na kiraka,Nabeel ya rubuta number dinsa ya bashi sannan ya tafi. Annoor kuwa tunda akace an tsaida ranar aure duk ya rude da shirye shirye wata Daya aka sa tal,Habiba ta fara gyara Amarya sosai tana zuwa wajen gyara,sosai suke shiri,yayin da Maryam tana ji tace wlh baza ta sabu ba,Kauyen Maman su ta shirya ta tafi,tana zuwa ta samu Yan uwanta na wajen uwa tace Dan Allah wajen gagararren malamai zaku raka ni,miji na samu zan aura naga yanzu Yana min Wala Wala zai gudu,mutanen kauye da masifar son ayi aure ko za a mutu,wata Dausiyya matar aure ta raka tace akwai Malam Musa aikinsa kamar Yankan wuka wlh,idan zai yuwu zai fada miki daret (direct). Suna zuwa suka same shi a zaure ya dawo kenan daga Kasuwar kauye ya siyo kayan taushe,Yace a'a Dausiyya kece tafe? tace Malam Yar uwata na kawo maka,yace mashaallah to ta shugo,Maryam anci wanka ita ga Yar birni ta shiga cikin zauren ta zauna,Dausiyya ta tsaya a waje sabo da sirri. Maryam bayan sun gaisa tace Malam wani nake so kamar na mutu Malam amma yaki so na wata yake so gashi har an sa bikinsa an kusa ma,Malam gashi da kudi ga kyau Inda kasan shi yayi kansa wlh,Malam komai da ake so a wajen namiji ya hada,amma yaki so na,Malam yace Kash me yasa baki zo da wuri ba ai da tuni ma kina gidansa idan da rabo ma an samu. Yanzu bari a fara dubawa aga ta yanda za a bullowa aikin,Kasarsa ya jawo a faranti ya fara Zane Zane,sai da ya dauki lokaci sannan yace babu alheri a auren ku,kece kike sonsa amma shi baya sonki ko kadan, dai dai da digo baya sonki,gashi Nan zuciyarsa babu hasken sonki a ciki duhu dundum,Maryam tace to ya za ayi a kulla kaunar ya dawo Yana so na? Malam Musa yace aurensa fa babu fashi sai anyi shi ko me zaki Masa,Maryam tace to a haukatar da Iman din mana,Malam yace babu Hali babu hauka a kaddararta,duk Kuma Wanda zaki je sai dai ya miki karya yaci kudinki sannan ni bana haukatar da mutum bana kisa Kuma,Abu daya zan iya miki idan anyi auren kar ya kusance ta,Maryam tace yawwa tace Hakan ma yayi,Malam yace indai ya sake ta kwance Mazagi ma'ana tazuge to shike nan sai ya kawo,Maryam harda dariya tace haka yayi ni Kuma zan San yanda nayi ya Soni,Malam yace idan ta tabashi sai ya kawo kawai,Maryam tace wlh yayi min,nawa zan bayar yace wannan karamin aiki ne ki Bada sadaka kawai,ta bashi dubu goma,Malam ya haukace yace zaki ga aiki,ya Saba da mutanen kauye Dari biyar dubu daya akan wannan wani sai yayi kisan Kai. Maryam tana fitowa tace an gama Dausiyya gaskiya ya hadu Malamin Nan,suka tafa tace ai zaki ga aiki wlh,a ranar Maryam ta koma gida birni,Malam yace sati biyu yayi yawa Amarya tana tarewa bazai iya komai ba. Masu Sharhi Ina godiya,Baby Ak Ina godiya sosai. Arewa book AsmaBaffa1 TikTok AsmaBaffa AsmaBaffa [1/24, 5:46 PM] AsmaBaffa: TANTIRIYA