← Book details Tantiriya A Gidan Yari Book 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 41 OF 87

Sashe 41

Tantiriya A Gidan Yari Book 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tana nuna Me unguwa da yatsa tace Idan na fito Maka da rashin mutuncina dana fito da shi daga gidan yari,idan na fara Maka tijara da wulakancin Dana fito da shi daga gidan yari,bala'ina Dana fito da shi daga gidan yari wallahi sai gangar jikinka ta fita ta bar ruhinka Liman yace ke ko kin haukace ne,Kan Liman tayi kamar zata dake shi tace Kai yane ta Masa maganar Yan daba Ina magana kana magana kana fada min burkutu,ta nuna Me Unguwa tace a fada Masa zan saita Masa zama,sai na hanashi Shan ruwa a kasar nan,sai na maka wanka da ruwan kwata,kayi min sharri kayiwa uwata sharri ka kashe mata aure Dan uwarka, ta ebo kasa ta watsawa Me unguwa a kansa,ya mike yace keee ni... Chika tace uban me zaka iya matsiyaci,Babar Chika ce ta fito da gudu tana kuka tace yau na shiga uku wai baza ki hakura ba, dattijai ne da girman su,ai suci darajar tsufa, dazu fa nace ki hakura,bazan hakura ba sai ya Fadi gaskiya wlh sai ya tonawa kansa asiri zan hakura, matsiyaci haihuwar asara Allah ya isa me shedar zirrrr,kasa ta ebo ta watsa musu ku tashi ta fisgi tabarmar ,Suka mike da gudu,ta dakko dutse Kato suka arce da gudu ana ta musu ihu,sabo da kowa ya tsane su a garin sabo da gulmarsa da bakin halinsu,sun buwayi kowa a garin,Chika birge mutane tayi dama an rasa me yin haka kaf garin sun hana mutane sakewa. Kwana biyu Mummy kwaya ta saketa ta bude idonta ta mike ras da ita ba wani alamun ciwo ko wani Abu,Malaman suna ta karatu aka ga ta mike suka ce Alhmdllh Alhmdllh sun fita sun saketa, inshaallah ta rabu da su kenan baza su sake dawowa jikinta ba Kuma ai anyi arziki,Yan uwa sai rungume Mummy suke,Spark ma ya rungumeta Yana mata sannu,sabo da rainin hankali tace me nayi? Me ya faru dani? Ina Baseeru na? Ina Mero Yar aikina Dan Allah kar ta tafi, ban San me ya hau kaina ba nace na koreta,ku fada min me ya faru Dani ne,su Mima sune masu Bata labarin komai. Mima tace kika Fadi kina dafara,Mummy tace Subhannallah,muka kaiki asibiti Abu dai yaki,Yaya yace a dawo Dake gida,muka dawo dake aka Nemo malamai suka dinga karatun Qur'ani a kanki ayoyi masu zafi suka dinga karantawa,Mummy tace shedan a gidan nan Kuma tasa ta kare,suna ta bata labari yanda Spark ya damu,Mummy taji dadi tace ashe dai Yana son uwarsa,suka ce ai munga zahiri,duk son shegiyar Matarsa Naila da yake yi sai gashi a kanki ya watsar da Yar iska,a nan yake yini,da asuba yake fitowa sai dare,Wahida tana wajen tace mayyar har nan take biyo shi ai,tana iyayin banza ita me miji. Naila Kuma Allah sarki kullum sai ta yo soye soye na sha'awa ta kawo musu amma basa taba gani,yanzu ma sallama tayi ta shugo da basket dinta na abinci,suka ce gata nan jaraba an dafo kayan tsafi za a mallake mu,Mima tace baza mu mallaku ba kuwa Ubanta yayi karya,Naila shugowa tayi ta durkusa ta gaida iyayen, Yan matan kuwa sai harararta sukeyi ana mata kallon banza,duk da haka tace sannun ku ya me jiki? Mummy tace kin ganni ai naji sauki na maye na tambaya Kuma,tace to Allah ya Kara sauki suka ce Ameen a fusace,zata mike kenan suka ce dauke Abincinki ki kaishi can Palo baki saci,ko Kinga Jikin mu da yunwa?cewar Anam da wata kanwar Mima. Dauka Naila tayi ta fito ta shiga kitchen ta juye a flasks din Mummy ta tattara nata a basket din ta fito ranta yana mata suya sosai,tunawa tayi da maganar Abbanta fadan da yayi mata tayi hakuri kawai ta zauna ita kadai,lokacin Spark ya fita Yana waya. Tana zaune suna ta zirga zirga suna jefar mata da magana,Anam ta fito tace wlh Ina Nan sai na rama dukan da kika Sa Yaya ya min,shegiya Yar gidan Dolo,ubanki Hashimu dolo to Munji labari KwarKwar ne ubanki,ashe ma wani bi ta can ne wani shagiri girbau ne ubanki. Naila kasa jurewa tayi tace ke Ubanki fa waye shi kakanki ma nasan asalinsa manemin mata,Dan bariki,gwara ubana halitta ce ta Allah,talauci Kuma ai ba Wanda yazo duniya da arziki,haka Yayanki ya gani yace yana so,Kuma dole a zauna dani ba yanda za'ayi,sai ma na fara zube muku yara tukun,ke dalla talakawa,ai duk mun kwakwulo komai naki,marar asali dama da Gani Yar kauye ce,wata ce cikin Yan matan budurwa tazo tace Yar gidan Hashimu Dolo da Kubra suka kwashe da dariya suka yi gaba. Mero tana zaune a daga wajen kitchen a bayan kujera tana ta recording basu sani ba,tace kamar na kunnawa mijinta yaji,Naila ji tayi cin mutuncin yayi yawa tana magana Kuma zasu yi mata duka ta mike zata tafi,budurwar ta fisgo hannunta tana cewa wa kika cewa Kakansu Manemin mata?,Naila tana Juyowa ta sharara mata Mari,wai wai wai ai duk fitowa sukayi,Yan matan suka tararwa Naila suna dukanta kamar Allah ya aiko su,ga Naila ba karfi,hancinta ne ya fara fitar da jini ta fara habo sosai, Spark ne ya shugo Yana can Yana waya. Suna ganinsa suka gudu iyayen suna kallon yaran basu iya tsawatarwa ba. Spark yaga Naila a kasa tana ta habo duk da Bata ji rauni ba sai iya habon,dagata yayi da sauri kamar zaiyi kuka ya dakko tissue ya bata yace jeki wajen mota, ya leka wajensu a daki yace ni wannan ai ba so na kuke ba,wlh bakwa kaunata ban sani ba ashe,yace duk iyayena ne ku da kannena ashe ni ba kaunata kuke ba, shike nan gwara da aka yi yunwa halin kowa ya fito. Mummy tace tab an tabo tsiya wlh shike nan duk Yan matan Nan sun shiga uku wlh ko a hanya kuka ganshi ku gudu,mu Kuma ya daina zuwa wajen mu,Mima tace gashi kuwa da iya daukan mataki,Spark ficewa yayi ya koma Inda Naila take Jikin fanfo ya hangota ta kafa kanta ruwa me Sanyi yana zubo mata,Mero da gudu ta fito tace bari kaji abinda suka mata, ta dannawa Spark recording ya karba duk yaji,ya goge daga wayar gaba daya,ransa ya baci,habon Yana tsayawa ya riko Naila ya goge mata ruwan ya sata a mota,tace da mota nazo yace bari zan sa a kawo motar gida,suka shiga sai gida. AsmaBaffa [1/19, 2:26 PM] AsmaBaffa: PAID GROUP 300 ACCNT NO 0175487861 ASMAU GARBA MUHAMMAD GTBANK YAN NIGER +22790795939 TANTIRIYA A GIDAN YARI BOOK 2 ~YARAN JAURO~ 51-55 Official AsmaBaffa SADAUKARWA NE GA AIDA MAMAN TASNIM PAGE NAKI NE UMMU KHINAL Naila kawai takaicin ta Bata rama ba,ga ba su Chika ba kowa bare ta sa a daukar mata fansa,a ranta tace Ina ma Chika Na nan nasa sa azo har gida a zane su,takaici ne ya ishe ta wai Ubana KwarKwar,nawa iyayen ma da sunfi nasu hankali,tace wai Abba ne shashasha,Spark Yana driving Yana kallonta,yace kiyi hakuri please,Naila tace ba komai hawaye ya zubo mata,duk abinda kaga ya sa Naila kuka kasan yayi Muni bata kuka. Hawayenta ta goge da mayafinta wani yana sake fitowa,parking yayi a gefen titi,yace baza ki hakura ba kenan mu koma a rama miki? Naila ba kunya tace ae,murmushi yayi yace sarkin ramuwa,ni kike aure ba su ba me zai dame ki,nine idan na miki zaki ji haushi amma su mene su,Naila tana kuka tace amma ubana aka zaga wlh sai na rama zan hakura,kawai dan Ina shuru sabo Kai kawai nake kyalewa,ba Wanda ya isa ya sani hawan jini sai na tafi gidanmu bazan iya zama a dinga zagin iyaye na ba,muna da rufin asiri ba Wanda zai dinga ce min talakawa tunda ci, sha da sutura basu gagare mu ba. To kiyi hakuri please my love,Naila tace wlh bazan hakura ba sai sun zo har gida sun durkusa sun bani hakuri ko Kuma kaje can su baka Bado,murmushi Spark yayi yace ni din? tace da waye to? ta dauke Kai ta Kalli Jikin window can,hannunta ya ruko ta fisge hannunta,Kuma bazan sake zuwa gidajen danginka ba ko wace bazan je ba ko su waye tunda babu mutunci,Spark shuru yayi Naila tana ta faman Cece kuce,yanzu laifin ya dawo kaina kenan bafa ni nayi laifin ba,Kuma kin San ko waye ya miki Ina rama miki fa sai in ban sani ba,Naila tace yo Kuma dai wannan na baya ne ya wuce magana ake a yanzu,ba wani batun yaji a daina shiga safgarsu ai Anji tsoro, su zo su bani hakuri,ba ruwana da Wahida bata dameni ba nasan kishi take,kannenka nake magana su zo har gida su bani hakuri. Spark yace zasu zo indai wannan ne kiyi hakuri kinji Baby, Naila taki dariya Sam,yace my love,taki kula shi, sweetheart,Babyna,my Apple? Bata kula shi ba,a haka suka koma gida ko gama parking baiyi ba ta fice tayi ciki, direct Bedroom dinta ta wuce bata ma shiga dakinsa ba,Spark yace ikon Allah ni ba da laifi ba yara sun jawo wlh sai kunci burar....bari na fito,wanka ya shiga yayi har da yin shiga ta musamman kamar zai je daurin aure, kace wani ango ne ya Sha shadda fara tas,harda yar hula,duk dan ya birge Naila ta daina fushi. Kitchen ta fito ta shiga ta fito dauke da cup na juice a hannunta ta zauna tana kallo tana Sha,fitowa yayi taji kamshi na dabam ba Wanda ta Saba ji ba,wurin Steps ta kalla ta ganshi yayi masifar kyau kamar ta lashe shi,idonta ta dauke taci gaba da kallonta,tunaninta ma fita zaiyi sai taga yazo ya zauna yanda zata kalle shi,suna facing juna ya tsura mata Ido,a hankali ya furta yunwa nake ji fa,ba tare da ta kalle shi ba ta mike ta shiga kitchen ta kawo Masa abincinsa ta jera a gabansa ta koma ta zauna,yau ba mutunci ko zuba Masa baza ayi ba. Kallonta yayi yace zan danna phone Dina a zuba min,tace bazan zuba ai an iya zagin iyayena,Babana bai bada ni dan a zage shi ba,Spark gefenta ya dawo ya zauna, zata mike ya rike ta yace bafa ni na miki ba Naila me yasa kika kasa ramawa? In sun miki ki rama shine kawai,ba Kya ganin Mero ramawa take yi,in kika tsaya jiran Yan gidanmu baza su gane ba,Naila ta kalle shi tace ni da Mero daya muke? tana auren wani
Chapter 41 · 0% Book details