Sashe 29
Tantiriya A Gidan Yari Book 2 Complete Hausa Novel · about 6 min read
rabon gado ta bawa danginsa takardu suka ce ai nata ne ya fada musu kafin ya mutu a bar mata gidanta. Bayan tayi takaba nace ta koma gidanta da zama tunda baza ta aure ni ba, ta koma na daukar mata Yar aiki dattijuwa suna zaune tare,na sata a makaranta ashe tayi primary a secondary tana Ss1,gata da basira kawai nasa ta zana waec take ko,bayan ta fito tayi kyau na nema mata university BUK ta shiga tayi Diploma,nayiwa abokina magana aka sama mata aiki ta fara a ministry of Environment,ta koma karatu tayi HND dinta ta samu Karin matsayin daga nan Kuma ta koma rike kanta da kanta,Kun ganta ai duk Kun Santa tana zuwa gidan Nan wajen Habiba ai. wannan yar Gayun Maman Annoor dama ba kishiyar Ummi bace? Iman ta furta Jauro yace ae kawai fada muke yi,Mahaifin Annoor Yana Nan ance yana America yanzu wai yayi arziki amma ban San gaskiyar zancen ba,Abba yace Dan me Saida yalon tsiya da jaraba. Abba yace masu aure sai a sanar da mazajensu gaskiya idan suna sonsu tsakani da Allah su zauna a haka da su,Jauro yace ai ni bana Abu da ka dakiki Hashimu,kayi using da number six dinka,ta ya zan aura musu banzan namiji wlh duk Wanda ya musu gori nace bazan yarda ba,shi yasa kafin Laila tayi aure na samu mijin ni da shi na fada Masa nace Amana, yasan gaskiya,yace iyayensa suna da matsala idan suka ji baza su yarda ya aureta ba a bar maganar tunda ya sani,to kinji Kuma wlh sun Sha yin fada Ina sasanta su amma bai taba mata gori ko ya fada mata ba. Mijin Karima kuwa kwanaki na kusa kashe aurenta sabo da na fadawa mijin ya sani tun kafin aure yace iyayensa basu da matsala,suma iyayen iya uban ne da uwar suka sani suka ce kar a sake fadar zancen ma bare dangi suji wlh masu hankali da addini,dama su Yan izala ne na gaske ko Yan uwan mijin ba su sani ba sai shi sai iyayensa,Rannan Kuma sunyi fada yayi mata gori,tazo min tana kuka yace mata Yar gaba da fatiha,Karima tazo tambayar waye Ubanta,kokari nayi muka rurrufe zance,iyayensa ne suka shiga lamarin gata Nan itama Yar banza tana sonsa da nace zan kashe aure cewa tayi ta yafe Masa a bar zancen. Sajid mata basu da hankali wasu, shi yasa ban fadawa matarka ba bare iyayenta,in ka yarda da ita kayi mata bayani Yanda zata gamsu idan Kuma zata Maka hauka kawai saketa ka auri wata mata gasu Nan sai ka darje,Abba yace hakane Kam. Dan Allah kar ku bari wannan ya dame ku,abinda zaku yiwa Allah godiya da kuka fada hannun na gari sannan Allah ya yiku a musulmai wannan shine babban gata,ba laifin ku bane laifin Iyayenku ne,karku ce zaku gaje su tunda Kun samu tarbiyya dan Allah ku rike kanku ku bawa mara da kunya. Jauro daga Gani Allah ne yasa ba yaransa zai Raina ba ku zai raina,ni Kun ganni wlh ban taba haduwa da me cikin shege ba sai dai naji labari wai wai sabo da Allah bai kaddara min ba,amma ku duba Jauro a yawon business yake ta haduwa da kaddararsa,gashi Kun zama dangi Kun zama Yan uwa,to me zai dame ku,gashi Allah ya azurta Jauro ashe dan ya kula da ku ya azurta shi, wannan fa abin alfahari ne ma a gareka Jauro,ni kaina Ina kyamar yaran da aka Haifa babu aure amma nayi darasi wlh yau,da Yar budurwar Yata tana nan Hidaya ga me sonta zan bashi ita,ni a nawa hangen da shawara kar ace za a muku aure a junanku,gwara a sirka Madara da Koko ai yafi ko? Duk ku nemi yaran sunna ku aura Kunga ai an sirka gudun haihuwa,yara ake ji gaba kar su yo gado gaba da baya ace kowa ba Dan sunna bane ai Kunga yara zasu zo a tambade,ita wannan mannirar a bawa Annoor tunda ta nace Masa kullum duk ta tsotse Masa zakin jiki Yo wannan duk Wacce ta auri Annoor ai ragowarta ta aura,Annoor yace a bani Iman Kuma? kanwa ta ce fa ni a matsayin kanwa nake sonta,Jauro yace to na bawa Nabeel dama ni shi zan bawa,Annoor yace wlh bazai aure ta ba,babu Wanda ya isa ya aureta,Hashimu yace Kai ubanmu ne Kai ka isa kasa muyi ko mu fasa,Kai din banza na baka Iman sai ka aureta,dama Jauro yace kaddara ta fada mata abinda Ubanta yayiwa mahaukaciya shi ya faru da ita dama tunda Kai take rungumewa Kai zaka aureta,Iman tace nima bana sonsa a bani Haidar,Haidar yace Ina da Kunkuma ta ni,wannan jarababben ya caka min wuka a kanki Iman ba ruwana,Nabeel Bai ce komai ba ma shi takaici ya ishe shi. Jauro yace magana ta karshe Annoor zaka auri Iman? Annoor yace ya zanyi zan aura amma dai kanwa ta ce,Abba yace Dan iskan karya,Iman tace ni bana sonsa,Jauro yace auren dole to zan miki shike nan,Annoor kuwa ya kule da takaici tana ta cewa bata sonsa,Abba yace sai a hankali kowa yasan dangin uwarsa dana ubansa,Jauro yace duk iyayen wasu a ciki sun San juna tunda wasu suna gidan na kawo wasu na tara mata da yawa lokaci guda suna shayarwa a gidana,tunda wasu tsakaninsu ba tazara,kafin wannan ta yaye na kawo wasu,ba sharrin da ba a min ba gari. Abba yace bari na tashi na tafi gida tunanin Yar Inna nake yi tana can yanzu ta shirya min girki,Habiba tace baza ka tsaya Kaci namu ba? Abba yace sai kace maye gidana akwai,so kike Yar Inna ta tuhume ni,Jauro ya fita raka Abba suna ta hira,an bar yara da Jimami,Habiba tana ta musu nasiha ta koma kitchen tana hada musu abinci,Iman tashi tayi tana kuka zata shiga dakinta Annoor yayi sauri ya fisgo hannunta,ta fashe da kuka tana cewa Yar mahaukaciya ce ni,ba a San ubana ba,uwata bata da hankali,Annoor yace haba Yar gudulle ta,babu tawakali,Zauna ya zaunar da ita akan cinyarsa,Sajid yace yanzu fa aka fada muku ba muharramai bane ku,Annoor yace baza mu fasa ba kanwa ta ce,karku zugani wlh na taba kirjinta a gabanku,Haidar yayi dariya yace dama so kake Dan iska,ka Dade kana bukata ai dan kayi ba mamaki. Iman kuka take kamar ranta zai fita bata Jin lallashi,Annoor yace mun shiga uku mu Kam ga Dan wajen marar Imani ya bude shi da kyar na dinke,gashi yanzu babanmu ba San Ina yake ba,mu kuwa Ina zamu sa kanmu,Iman tace tana kuka tace wlh ko an min auren baza a samu kaina ba bazan iya komai ba,Annoor yace haba ke kuwa waye baya son kauna da zaki,zaki da maiko fa haba Iman ai dai Kya bari a Kara yi da Lollipop ko ba gaskiya ba?,Iman tana kuka tace ni ba Yar iska bace bazan yarda ba,Annoor yace to ai anyi me wahalar Iman wani ya bude hanyar Dan Allah kiyi hakuri ki yarda da mijinki idan an daura,bana sonsa ko waye cewar Iman,Annoor yace bari na rabu dake sai an miki auren tukun zamu gani,a rasa Wanda za a bani sai Dan uwana yayana har abada Dan gidan nan Yaya nane na jini bazan iya mu'amular aure da shi ba,Annoor yace kafin a daura zanyi gwaji ko da kiss ne Iman idan har baki ji komai ba to shike nan a fasa auren. Haidar yace to fa iskanci ya motsa an samu dama ance ku ba muharramai bane,Nabeela tace Yaya dama haka kake,Annoor yace na wuce haka ma karku raina min hankali ni kadai ne me so wai. Naila ce ta kira Abba zata fada Masa halin da take ciki su tayata da addua ance kwayayenta na haihuwa kadan ne.