← Book details Tantiriya A Gidan Yari Book 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 75 OF 87

Sashe 75

Tantiriya A Gidan Yari Book 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

AsmaBaffa [2/2, 8:18 PM] AsmaBaffa: TANTIRIYA A GIDAN YARI BOOK 2 ~YARAN JAURO~ 91-95 Official AsmaBaffa SADAUKARWA NE GA AIDA MAMAN TASNIM PAGE NAKI NE Anty Nurse Zaria Rafeeq harda wani basarwa shi ga me gida,sun tsunduma a duniyar Nishadi kawai suka dinga Jin Door bell tana Kara ta cika ko Ina,Ikhram bata ji bama tsabar tayi Nisa Rafeeq ne yaji,tsaki ya ja yace yanzu haka mayun yaran Nan ne su Arham,fitowa yayi ya bude kofa a fusace sai yaga Naila tare da Hidaya,murmushi yayi yace wai kece dama thank God ma kece shike nan wuce ki zauna wanka take ki jira zata fito bari na fada mata,Naila tace to ya haura sama Yana zuwa Ikhram tace waye yace Naila ce ma ashe ai ta San kan garin rabu da ita sai na idar na sauke farali,Ikhram tace ka bari sai dare Please sai tace mun mata wulakanci,Naila ce fa baza ta ce ba tasan komai Yar duniya ce da kike Ganinta da gidanta kika je baza ta fito ba sai sun gama,wa yace tazo gidan Amarya. Su Naila suna zaune Ango da Amarya shuru shuru basu fito ba,Hidaya tace Anya zasu fito kuwa ko dai ko dai abin akeyi,Naila tace zai wuce shine sai an fito ace mana wanka ake yi,kema kwana Nan zaki fara Hidaya bari a kaiki gidan Nabeel,Hidaya harda rufe Ido tace nidai ba ruwana bazan yarda ba tsoro ma nake ji,Naila tace zaki cuci kanki kuwa mu muna gefe muna Jin dadinmu gwara ma ki yarda yarinya,mu ganshi mijin naki na sake kallonsa na gani ko zan gane kalar tasa Hallaren kin San fa ni me maganin gargajiya ce ato idan kubewa ce shike nan,Hidaya ta nunawa Naila hoton Nabeel,Naila tace ahh da alama doguwa ce kin tsallake rijiya da baya. Suna ta hira abinsu sai da aka kwashe lokaci me tsawo sannan Ikhram ta fito ta Sha wanka cikin material tana kamshi,tace na Dade ko? Ina shiga wanka yace min kunzo,Hidaya tace ai fa mun ga alama,Naila tace Kun dai kwalbe kar a wani yi mana alaye,Ikhram dariya tayi ta mike ta kawo musu kayan motsa baki,tace Naila ya kamata ki bawa Nabeel matarsa wannan wanne Abu ne,Naila tace gobe zasu tafi fa sallama na kawo su dama su Zarah suna gidan Chika su Spark ya tafi da su tun rana,sun Dade suna hira sannan Rafeeq ya fito sanye da jallabiya Yana kamshi yace ba dai tafiya ba? Naila tace ae tafiya zamuyi Baby kar su koma gidan banyi girki ba,Rafeeq yace uhm kaji masoya,dariya suka yi tare da raka Naila suka shiga mota,Rafeeq ya bawa Hidaya 10k,Ikhram ta bata turaruka da kayan gyara Bado. Su ma su Zarah sun samo kudi suka dawo da tsaraba iri iri Spark ya kaisu ya kashe musu kudi,har Hidaya aka siyowa nata,Spark Yana rike da Hannun Aslam suka shugo,Naila tace sannunku da dawowa yanzu muka dawo muma,kayan suka hau nunawa Naila suna Murna,Spark tuni ya wuce sama Yana wanka,su Naila suna ta kallo. Mima ce ta fito ta samu Arham Yana kallo tace Kai wai ka daina zuwa school ne? Arham yace tun yaushe Nima na gudu daga aikin Soja bazan iya ba wlh ai ni yanzu a online nake karasa degree na aure zanyi ni bazan tsaya bautawa kasar da bata da alqibla ba,ai tunda aka balla min kafa da kyar na tashi na cika rigata da Iska Nima,yanzu Papa Bai da magaji kowa ya gudu sai Junior shima Yana sanin ciwon kansa zai arce wannan bakar azaba haka,Mima tace to tashi na aikeka gidan Mummy tun jiya nake kiran wayarta tana ta ringing ba a dagawa je ka gano min lafiya take kuwa,kayi sauri kafin magriba tayi,ya mike yace to dama a shirye yake cikin kana nan kaya sai ya wuce kawai. Yana zuwa ya iske gida a bude ba kowa,me gadin ma babu,ciki ya shiga a hankali Yana sallama ya samu wayoyinta a Saman kujera da takarda a gefe. Arham takardar ya dauka ya fara dubawa a hankali yaga ta rubuta Spark dana ka sanarwa Yan uwana ni na gudu Inda baza ku sake Ganina ba,Allah ya gani nasan prison za a kaini karshe,bazan iya zaman gidan yari ba,kuyi hakuri da rashina na shiga duniya,idan da rabo Allah ya hada mu watarana,Ina me baku hakuri da hukuncin da na yanke,ka sanar da Yan uwana Ina musu fatan Alkhairi,ga wayoyina nan na barsu kar ma ku neme ni baza ku ganni ba nayi nisa yanzu haka Ina hanya. Arham Yana gama karantawa ya kira Mima ya sanar mata komai yace Mima Yar uwarki dai ta arce tace kuyi hakuri da ita ta shiga duniya,Mima tace ban gane ba,yace bari na zo gida ki gani,Spark ya kira yace babarka ta gudu fa ta bar gari tace baza ku sake Ganinta ba,kazo gidan Mummy gidanku kazo ka gani yanzu,Spark bai bata lokaci ba ya iso gidan. Takarda Arham ya nuna Masa,Spark ya karba ya karanta,Yana gamawa yace shike nan naci gadon gidan da sauran kadarori,dama gado ance jeka Inda ba a sonka,wani can sai yazo yaci gadonka,Arham yace au haka zaka ce ma uwar taka guda to Nima a bani Daya motar ladan bincike dole a San min ganima,Allah yasa ta bar gwalagwalai da shike nan ni na samu jarin aure,Spark yace baza fa ta wuce tayi hanyar Lagos ba,bari ka gani,Arham yace Dan Allah kyaleta muyi rabon gado Ina ruwanmu tunda Kai baka yi dacen uwa ba,Allah yasa ma kana da Naila ta karbi Duty tuni,Spark yace wlh kuwa na saki nonon uwa na kama na mata Kai muje baza tayi 24hrs ba zan sa a dawo da ita. Spark ya kira wayar sojoji ya basu sanarwa da number motar da tafi da ita da komai na motar da hoton Mummy yace kar ta kwana a dawo da ita gida,Sojoji suka bazama kamar za a kamo shugaban Yan ta'adda,can Hanyar Lagos suka tsinci Mummy goslow ya riketa,dama sojojin gaba aka yiwa waya aka basu sanarwa,babu bata lokaci suka saka Mummy a motar su suka dawo da ita Abuja. Tunda Mummy taga anyi hanyar Abuja da ita take kuka kamar ana yanka ta,kafin gari ya waye an dire ta a gidan Mima. Kin shiga tayi ciki ta sojoji suka rakata da bulalai amma basu taba ta ba,Arham yace yawwa gwara ki bar mana wasiyya baki da baki shi yasa naki bacci wlh Ina ta jiranki,Arham tashi yayi ya kwankwasawa Mima kofa cikin dare yace kanwarki ta dawo ki fito,Mima ta fito da sauri ta rungume Mummy suka dinga kuka tare,Arham ya shiga kitchen ya cikowa Mummy plate da tuwo yace Maza a zirara loma ibtila'i ya fada mana kullum tuwo gashi har mun fara dan ciki kwajaja babu vitamins. Tafiya Arham yayi ya kwanta abinsa ya bar Mima da Mummy,Mima tace yanzu Mummyn Spark mene ne abin guduwa sabo da Allah? Mummy tace au ke baki ga abin guduwar bama? Prison fa tab ai karku sa rai zan zauna tunda an kamo ni amma sai na koma sabo da ni bazan iya harkar gidan yari ba,Mima tace tunda kin San kin aikata kiyi nadama ki tuba sannan ayi miki hukuncinki gidan yari ai ba mutuwa bace da kudinki sai ki koma VIP nasan Spark wlh zai kula dake,Mummy tace kaiiiiiii....shike nan duk su joint joint, wuraren shakatawa, chashewa ace duk Ina gidan yari,bazan iya ba Allah ya Gani Istingifari dai nayi. Mima tace yanzu in kin bace mene amfanin Hakan? Ni yanzu baki San damuwa ta,Mummy tace dan Allah ki barni naji da tawa koma mene taki da sauki,Mima duk da haka tace wlh sai na fada miki ta kwashe yanda suka yi da Papa ta fada mata har abincin da yake basu yanzu,Mummy tace shi yasa na dinga mamaki Banga Yan aiki ba, lallai General bashi da mutunci ashe haka yake,ki duba sanda Yana sonki kafin ya aure ki harda hawaye ance baza a bashi ba ya dinga hawaye Yana rokona na baki shawara iyye yanzu ya manta wato,sai da ya gama dake kika Tara Masa yara da jikoki duk ni'imarki ya gama kwasheta shine zai koma Baku tuwo,Mima tace dadin abin ma Nima na gama kwashe tasa ni'ima r wai aure ya Kara a can,Mummy tace tab Kinga jarabawa" sun Dade suna hira kafin daga bisani suka tafi bacci tare suka kwanta suka kwana suna hirar su . Washe gari da safe Mummy ta shirya kokawa gidanta tana fitowa sojoji suka dawo da ita ba shiga ba fita,Mummy tace wannan wacce kaddara ce haka a barni naje gidana naci abinci me kyau sai ace a Nan zan zauna,Mima tana kitchen ta tafasa ruwan Lipton tsura da sugar,sai dumamen tuwo me zafi Mima ta kawo mata tace gashi ki gasa cikinki sannan kici tuwo,Mummy yunwa ta dameta haka ta kurbu tsuran Lipton sannan ta jawo tuwon ta fara ci,Mummy tace ai ni tun yanzu ma an yanke min hukunci a gidan yari,haka ake yin tuwon? Shi yasa aka ce mata su dinga girki ko da ace da Yan aiki, yanzu sabo da Allah sai kace Ina gidan Ubale a kauye, Kai gaskiya Mima ki canja,tana Mita tana ci haka ta cinye sabo da yunwa. Mima dakin Arham ta shiga Yana ta bacci tace tashi Kai ta fisge bargon,a hankali ya bude idonsa yace Baby zo Saman bed,Mummy ta rufe da duka Dan ubanka sa'arka ce ni,Yan iskan yara watsatsu tambadaddu duk Kun lalace, Arham yace to Gani nayi bazawara ce,a hankali dai Kuna ta zama zawarawa,Dan Basi dinma yayi saki uku,kaga ni aikena zanyi gidana ka kwaso min wayoyina da duk wani kayan abinci da suke store na ka kawo su gidan nan,yace to bari na fito,wanka ya shige ta fito ta samu su Anam an tasa tuwo a gaba,Mummy ta dinga dariya kamar ba gobe tace amma ubanku ya iya iskanci,waye me kawo garin tuwon ne? Suka ce danki ne,tace wlh nasan sai shi. Yau Hidaya zas u tafi Spark yace Shaheed yazo ya rakasu a jirgi,sai murna suke zasu hau jirgi,Nabeel waya ya kira Hidaya tace yanzu zamu taho fa,Nabeel yace zan dauke ku a airport, dama yanzu zan fadawa Yaya yaje ya dauke mu amma tunda kana nan sai kazo a airport,yace Kuna shiga jirgi ki fada min,tace "to" ya kashe wayar,Baki Hidaya
Chapter 75 · 0% Book details