Sashe 12
Tantiriya A Gidan Yari Book 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Chika tana ganin Mummy a wajenta tasan ba lafiya,Mummy tace da Chika Yaya kiyi hakuri ki karbi kwananki,Chika tace a'a yau nice Yaya kuma? ai ni wata uku na baki, Baseeru sabo da a Sha amarci lafiya,Mummy tace a'a ni dama bazawara ce 3days akeyi yanzu na wuce sati Ina laifi ma hakan na gode hakan ma yayi,Chika tace wlh tsakani da Allah na bar miki kwana na ko Baseeru? Baseeru yace ei Maman Spark ai kinfi amarya zaki,komai naki yafi min,Chika tace au Baseeru haka zaka ce min? ae baki da wani zaki,Mummy sai taji dadi yaci mutuncin uwar gida ita ce on top kawai sai ta hakura tace muje honey ya rike hannun Baseeru suka tafi,suna fita chika ta dinga dariya wai a dole Mummy ta cusawa kishiyarta haushi da bacin rai. Baseeru sai yabonta yake ya lallaba ya sake kwasar amarcinsa hankali kwance,Mummy taji jiki yau ma. Washe gari da safe Baseeru Yana kwance ya mike a Saman doguwar kujera yayi pillow da cinyar Mummy tana shafa Masa sankon kansa katsam babu Sanarwa sai ga Baban Beauty ya bayyana a Abuja gidansa,Chika mamaki ya kamata da tsoro tace mutumin da yace wata hudu zai yi, ai kuwa Daddyn Beauty ta bangaren Baseeru ya nufa,Chika ta fito da gudu ta Sha gabansa,dama ya San Chika sosai yasan Kuma ance tana gidan,yace Suhailat dama kina Nan kenan? Chika tace ae Daddy Ina yini tana haki,yace lfy Alhmdllh,ka dawo lafiya? Yace lfy lau Alhmdllh,ya nufi cikin part din Mummy,Chika ta sake tare shi tace Daddy dan tsaya dama... dama....uhmmm...tana Sosa Kai,Daddy yace ban gane ba ya tafi zai shiga tace Daddy karka shiga Nan ka koma part dinka na dawo nan,Nan take Daddy ya fahimci bata so ya shiga bangaren kawai sai ya mata tsawa yace matsa ki bani waje kaji yarinya duk yanda aka yi da wata a kasa. Yana shiga ya samu Baseeru me gadinsa kwance a cinyar mace,tsawa ya bugawa Baseeru yace Dan Basi uban me kake min a cikin gida Ina aikin naka na gadi? Dan Ubanka aikin kenan? Karuwa ka kawo min cikin gida,Baseeru a tsorace ya Fado daga Saman kujera ya zube a kasa jikinsa Yana rawa yace Dan Allah Alhaji kayi hakuri ka yafe min ba laifi na bane su Yarka Beauty da kawarta ne suka bani aiki Kwangila nayi zasu biya ni. Mummy mikewa tayi tsaye tace ban gane ba Alhaji Kabir ba dai Kaine me gidan nan ba?,Daddy ya furta Hajiya surayya Ina Dan naki me kike yi a Nan? Mummy tace kawata fa tana biko,Daddyn Beauty yayi dariya yace badai har yau Bata yi aure ba? wlh Kai take jira,kasan tsohon mijinta saki uku ya mata,Chika da Baseeru aka bari sororo,Muryar Mummy suka tsinta tace Ashe me gadinka na aura kenan? Alhaji Kabiru yace da ke baki bincike ba kika aure shi,Baseeru yana gaban Daddy a zube Mummy ta Kalli baseeru idonta yayi jajir sabo da bacin rai,ta rasa ma me zata yiwa Baseeru,Baseeru Mummy ya kalla yace Dan Allah....Mari ta Kifa Masa,Baseeru ya Dafe kumatu shima ya mike ya kifawa Mummy Mari yace karki manta mijinki ne ni a karkashina kike Baki isa kin Mari banza ba,kwadayayya me son abin duniya, badan Kwangilar da aka bani ba me zanyi dake, Ina da ikon auren Matashiya budurwa dan na rufa miki asiri ma,Daddy ne yace to matsalar aure ba a shiga tsakanin mata da miji,sanda kuka hadu kuka yi aure ban sani ba sabo da haka bazan shiga ciki ba,su Kuma Wanda suka hada wannan gwaramar zasu ci ubansu bari naje na samu Suhailat. Mummy fuuuuu ta haura sama ta fara hada kayanta tana hawaye tana zage zage tana dura ashar Baseeru Allah ya tsinewa uwar da ta haifeka shege Dan shegiya,Dan kut...Dan burar....wlh sai kasan ka yaudare ni sai naga bayanka,Baseeru ne ya haura saman shima yaji tana ta zaginsa ya shiga tattara kayansa yace yau sai bakin gate,my love hakki na ko za a Dan Kara min? Mummy kukan kura tayi ta cakumi Baseeru da kokawa,Baseeru ya kama nonuwan Mummy biyu Yana lagude su ta saki ihu tare da gartsa masa cizo tace sai Kaci kanin Ubanka da yayan Ubanka tsinanne talaka,gayyar tsiya gayyar na ayya gayyar talauci,ka zuba maniyyin talauci a jikina Allah ya isa,maniyyin da miyar kuka ce da tuwo suka sa ya taru shege Dan wahala. Baseeru yace sabo kike ana rubuta miki zunubi kina zagin mijinki,tace ka sake ni wlh,yace daram wlh ba saki duk Inda kika je Kuma sai na zo na karbi hakkina gwara ma ki bini dakina na gadi mu zauna a can,tace sai dai kaje da uwarka matsiyaci ta tattara kayanta ta fito tana hawaye,sai ga Spark yazo gidan tare da Naila,yaga Mummy tana kuka da akwatuna tana fitowa da su,Spark yace Mummy lafiya? Baseeru kofa ya kulle ya buya Jin Muryar Spark. Mummy kuka ta saki sosai kamar yarinya,Spark hannunta ya rike yace Mummy menene dan Allah,tace Ashe Baseeru me gadi ne ya yaudareni suka hada baki da Suhailat yarinya karama ya aure ni,sun Raina min hankali na hada jiki da gayyar talauci ashe me gadi ne,Spark yace Kinga illar rashin bincike Mummy,sai da na fada miki tuntuni kika nuna bakya so ma a shiga harkar ki ke,Mummy ta sake sakin sabon kuka ta Dora kanta a kirjin Spark, Naila Dake gefe taji haushi an haye mata kirjin miji,Bangaren Chika tana sanin asiri ya tonu komai shirin su ya rushe tuni ta tafi da gudu ta tattara nata ya nata ta shiga motar Misam ta tafi wajen Misam kafin ta gudu ta koma Kaduna garinsu wajen iyayenta,aiki ya rushe,Beauty ta kira ta sanar mata itama Beauty wayoyinta ta kashe kar ma Daddy ya nemeta ya sameta. Naila kuwa sabo da taurin kanta ta gani da idonta asiri ya tonu ko a jikinta tana kallon Spark duk ya damu kamar aurensa ne ya mutu sai Tausayin Mummy yake Yana lallashinta,bai nuna mata yasan me gadi bane yace ashe me gadi ne Mummy? tace bakin me gadi ma dan iska talaka shi yasa ni na Dade Ina Jin warin talauci a jikinsa,Spark yace uhmmm....zama bai ganmu ba dole muyi yaji sai dai Kuma Mummy ko kina son Dandanon Baseeru a hakura ya biki gidanki ku zauna tare Kinga ya zama mijin Hajiya,Dandanon banza Kai dalla dauki akwatuna ni ba ruwana karewar lalacewa ace me gadi na aura,saura naji ka fadawa su Mima kace Ashe me gadi ne wlh sai kaci ubanka idan naji zancen nan a wajen dangi aje ayi min dariya. Naila ta kalla tace to algunguma saura naji zance na yawo wlh kece sai na sa an sakeki,Naila idon Spark ta faka tayiwa Mummy gwalo harda daga mata gira, Mummy tace ni kike yiwa gwalo kina daga min gira Innalillahi wa innailayhirrajun,Naila tace me nayi ta marairaice ta fara kukan karya ni dai an tsaneni tunda aka kawo ni ta juya zata tafi,Spark ya saki akwati da sauri ya rukota yace I'm sorry Babyna,ya Kalli Mummy yace zan tafiya ta wannan ai bai dace ba yarinya tana baku girman ku bakwa gani,wlh na gaji ana hanani sakewa yanzu idan tayi fushi fa ni za a jawowa a asarar na yau dana asuba,so kuke na tafi Office a birkice ai akwai dangi a karkashina suna aiki Ina zuwa a birkice duk korar su zanyi dama ai dangin kune kuka sa na basu aiki,wallahi idan aka min asarar na yau gobe duk sai na kore su daga aiki. Naila bayan Spark ta koma ta buya ta leko Mummy ta sheke da dariya marar sauti,Mummy ta kalleta ta ja Kwafa,Naila ta samu ta yiwa Spark kiss a bayan riga bai sani ba,Mummy ce kadai take ganin iskancin da Naila take yi mata,harshen ta zaro ta lashi rigarsa a hankali shi bai sani ba,Mummy ganin rainin yayi yawa tace zaki bayani sanda na sa ya sakeki,Spark yace wa? waye zai sakar min mata? Kai dalla dauki muje shashasha wlh ba banza ba asiri tayi maka,Spark ya wuce da akwati Mummy ta dauki Daya suna tafiya yace munyi yaji Babana ya kori uwata Kuma, Naila tace da Mummy kawo na daukar miki akwatin,baza a baki ba fitsararriya marar tarbiyya,Naila tabi bayan Spark tana cewa yanzu shike nan auren ya kare? Baby aure rai ne da shi karka zama silar raba sunna,tsakanin mata da miji sai Allah,baka sani ba ko tana son abinta,Mummy tace har abada bazan so Baseeru ba shege bakinsa kamar robar kwasar tuwo" muje gidana Allah yasa ban zuba 'yan haya ba. Spark ya tuka motar sai gidan Mummy ya kaita can sannan yace da Naila muje madam,Mummy tace ban gama da Kai ba zaka tafi,yace dare yayi Mummy sauri muke yi we have a lot to do,aiki ne dani sosai,kin San ni Busy man ne yanzu tunda na ajiye 'yar Baby ai ba zama kuma,daga Office sai aikin Jihadi,wlh daga aure na zuwa yanzu Allah ne yasan yawan arnakun da nake kashewa kullum,idan na shiga sulken yaki to sai ta Allah Kuma,Naila tace ga Kuma Salkar ruwanka Ina mikowa,Yace ai ba karamin taimakona kike yi ba yau ma ki cikata da ruwan Zuma,Mummy tace Dan uwarka tashi ka tafi Ina fada Maka matsalata kana wani zancen kisan arna,wai Dan ubanka ni banyi auren bane sai kace Kai kadai ne kayi aure,tashi ka tafi ni na rasa dalili ma da bata yi ciki ba har yanzu ai baka cika jarumi ba tunda banga tana laulayi ba har yanzu ta fi wata guda a gidanka wannan masifar taka ai yaci ace ta fara laulayi tun sati biyu da kawota. Spark ya mike yace muje ni dai a gaban manya nake bazan yi zancen ciki ba ai da kunya abin kunya ne wannan ni kamata na yiwa wata ciki a'a ban isa ba ai ba yanzu ba ai yaro ne ni,dariya ya ba Mummy sosai tace Allah ya shiryeka wato Kai baza tayi ciki ba sai dai iskancin ka iya kenan,abin kunya kike fada Mummy a gaban surukar ki,ya mike Naila ta bi bayansa tana cewa Mummy sai da safe mun tafi,tsaki Mummy ta ja,tace wlh wannan kamar na dade da saninta na rasa Ina na San yarinyar nan anya kuwa a film ne. Spark suna fita ya dauki Naila tana dariya Goyata yayi