Sashe 60
Tantiriya A Gidan Yari Book 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ayi ta min hakuri fans AsmaBaffa [1/25, 8:31 PM] AsmaBaffa: TANTIRIYA A GIDAN YARI BOOK 2 ~YARAN JAURO~ 71-75 Official AsmaBaffa SADAUKARWA NE GA AIDA MAMAN TASNIM Page naki ne Maman Atika Ba editing a karanta da hakur Misam ba Wanda ya tuka shi da kansa ya shiga motarsa ya wuce gidansu,Naila duk ta gama aikinta na shiryawa Amarya gidanta Misam yayi kokari a karasa gidansa cikin kankanin lokaci duk da Papa ya tura musu kudi masu nauyi shi da Rafeeq a accnt,Yana shiga ya samu matar Baba da su Kamal a Palo suna ta yiwa Amarya nasiha,Baba yace to zauna kaima ayi da Kai,ya samu wuri ya zauna,Baba yace kasan dai hukunce hukuncen aure,ba haka kawai ake aure ayi abinda aka ga dama ba,Dan Allah ka rike musu yarinya Amana,ko wani Abu ne ya faru kuka samu sabani ku zauna ku sasanta kanku kinyi Ilimi Kun San komai sai dai ma ku koyawa wani,karku bani kunya,aure sai hakuri sai kunyi hakuri da juna,Kun mutunta juna,ke ki dauke shi shine Shugaba a karkashinsa kike ki Masa biyayya,Kai Kuma ka sani a karkashinka take komai Yana wuyanka,Nan dai Baba ya dinga musu nasiha kamar baza ta kare ba,har Misam ya gaji yace Alhmdllh mun gode Baba zamu yi tashi mu tafi ke. Chika harda kukan karya ita ga Amarya,Misam yace ki daina kuka Amarya Nima sai ki bani kuka zan maye miki gurbin Wanda basa kusa dake iyaye muje gidanmu Kisha Jamilu yogurt,Baba bai gane me ake nufi da Jamilu yogurt ba yace to Maza dama ance bata cin abinci sosai,Kamal Yana boye dariyarsa Dan shi Kam ya gane. Suna fita ya zaga tare da bude mata mota ta shiga ya rufe ya zagayo ya shiga ya ja sai gidan su,sai kace ya Sha wani abin a birkice yake sabo da jaraba,ta lullube kanta da mayafi gaba daya Yana driving Yana kallonta cike da tsantsan farin ciki,tunani ya Lula ma shi tuni Yana hango kansa ma ya fara Kwalbewa da Chika,har ya wuce hanyar gidan nasa bai sani ba,sai da tayi magana ta gaji ta bude mayafi ta leko da kanta tace har yau ba'a zo bane naji ai kace babu Nisa da gidan Rafeeq,slow down yayi yace ta Ina na biyo ne tsaki ya ja yayi youturn ya dawo baya sannan ya shiga layin,Yana shiga layin yaga motar Rafeeq Yana Masa horn yayi kamar bai ji ba,waya kira shi,dagawa Misam yayi Rafeeq yace ka tsaya Dan Allah muyi wata magana,ya zaci serious ne ya tsaya a gefen titi Rafeeq ya karaso tare da sauke glass yace late comer ya ka ganni,Misam ya Kalli Rafeeq ta window yace mene ne? kana bata min time wlh shi yasa nake kaunar Spark yasan muhimmancin bado da shine tuni ya koreni ciki amma Kai dake ta kanka kawai kake yi to na kalleka gashi nan bado duk a manne a jikinka ya fito shike nan? Rafeeq yayi dariya yace dama so nake na bata ma lokaci wlh ana ganinka an San baka cikin nutsuwa ni kuwa fa? Ana ganina an san magidanci ne Wanda yake ji da nutsuwa da kwanciyar hankali,Chika ce ta sauke glass dinta ta sake bude idonta daga mayafin tace Ina kawata ne? Rafeeq yace Malama Kuma ai yanzu ta koma school sabon darasi take dauka,dariya Chika tayi tace kace yanzu Kuma ta koma school yace,Rafeeq ya furta ai ta shiga Rafeeq College of education wacce yanzu ta koma university ai har degree da masters ake yi a ciki,ai jiya ta Sha Interview duk courses dinta na baya na mata tambayoyi a Kai ba Wanda ta ci carry over ta samu,amma na dauketa a school din sabo da a hankali nasan zata karbi darasi ta gane sosai,Ga ka kaine lecturer yanda ka iya koyarwa ai dole ta gane cewar Misam,Rafeeq yace fasihin lecturer ai sai Kai ai ni Tp nake a ciki,Dan teaching practice ne Kaine, Misam dariya yayi yace wlh zan Maka rashin mutunci. Spark ne ya kira Misam ya daga lokacin Rafeeq ya ja motarsa ya juya gida,Misam ya ja tasa Yana magana da Spark,yace kaje ka Kai matarka muna ta jiranka a gidan matata ta gaji haba wanne irin iskanci ne tun yamma ance ka tafi shuru,Misam yace sai kace Kaine angon ka fini matsuwa ne,ku tafi mana na rike ku ne,haka kace? ae nasan matarka ka biyo sabo da jaraba da naci ka dauketa ku tafi ni karka isheni,Dariyar takaici Spark yayi ya kashe wayarsa yace tashi mu tafi ke,Naila tace Dan Allah ka jira suzo,to yace mu tafi dole ne,ni badan shi na zauna ba fa ka bari akwai sakon da zan bawa Chika. Fushi yayi yace kin San Allah idan na tafi sai dai ki shiga taxi ki taho ya Ina cewa ki taso kina min musu,Naila tace nifa fadanku daban da Misam Kuma laifinka ne ba nasa ba dole yaji haushi,tsakaninku ne anjima zan ganku Kun shirya ni ka rabu Dani kawata tazo muyi magana tukun,Spark fita yayi abinsa Yana compound zai shiga mota Ango ya shugo,horn ya Masa ya sauke glass yace mun zo to sarkin fada,Spark Bai kulashi ba,tace ka jira matarka ku tafi in ka barta ma a Nan korota zanyi kofar gidan,unguwar nan Kuma duk karnuka ne wlh ba ruwana su yagalgalata Kai kayi asara,Spark murmushi yayi,Misam yace ai Nan zuciya kayi ka fito zaka barta baza ka iya ba ai zuciyarka ta mutu murus,Ai Kai zuciya dai yanzu babu a kirjinka indai Naila ce ka shiga uku kuwa ka hadu da jarabawa,wlh ka fara addua tun wuri haba,sai ka shugo kayi mana nasiha in kaga dama,Spark yace in kaga dama yau ma ka saketa saki uku,ko gobe da safe muzo mu iske kayi mata dukan tsiya me ya dameni,ce Maka ayi nasiha zan Maka tab,Misam yace ko jiya ba samu abin bane Kai in baka samu ba sai fada da kowa,Amarya ya budewa mota ta fito,Spark yace Amarya fatan Alkhairi ayi bacci me kyau,ki kwanta da wuri jiki Yana son hutu kiyi baccinki kawai,Chika tace to tana dariya. Yace ki fadawa Naila Hashim ta fito,Misam yace yau ba Baby kenan,suna shiga Naila ta mike tana tambaya ya tafi Dan Allah? Misam yace ba zuciya Yana Nan yace ace Naila Hashim ta fito,dariya suka yi,Chika ce ta ja Naila gefe suka fara kus Kus Naila tana Mata famfon iska sannan suka yi sallama ta fice. Tana fita ya shiga mota yayi mata key kamar zai tafi ya barta,sai Kuma ya tsaya ta bude gaba ta shiga ya ja suka tafi,Spark yace wato bakya Jin magana ko har ni zance kizo mu tafi ki makale,Naila tace baka son gaskiya Yar maganar da zata zo muyi shine abin damuwa,Misam din nan naga Dan uwanka ne sai kuyi fada a rana yafi sau nawa Kuma a ranar kuke shiryawa akan me zan shiga ni Chika ce dalilin zuwana Kuma kasan a bikina tayi bajinta to Dan na mata mene,ai kin iya zance indai magana ce ba a ka da ke,jiya kiri kiri kika yi baccinki Baki bani komai ba haka na kwana har yanzu,Ina tashinki kika ki tashi,to na gaji bacci nake yi me dadi lokacin,Ina laifi kullum ana baka dan rana daya ai kayi hakuri. Ni dai ana danne min hakkina yanzu,Naila tace bikin Yan uwanka ya jawo,waccen Kuma ai unguwa naje gida,Kuma kwana Nan dole naje kauye wajen su Goggo tare zamu je suna ta korafi baka je ba. Spark yace uhm Allah ya bani Iko tace Ameen,jiya shine kika ce min Ashraf,Naila tace yau ni naga ta kaina to ba sunanka bane? Okay Baban Nasidi Is around the corner,dama Abba ya fada,dariya tayi tace wanne Nasidi? Danki,Allah ya kiyaye a sawa Dana Nasidi,Goggo dai tace in ana fadar sunan miji kasa girgiza take,Naila tace lokacin da na fada bacci nake yi Kai Kuma ka dame ni,kar na sake Jin sunana a bakinki,Naila tace Ashraf din? dariya yayi yace me za a siya miki Yan mata? tace ba komai ahh a siya min tsire da kilishi yau,ya tsaya ya siya musu sannan suka wuce gida. Naila tace Sallar dare zan fara gaskiya ka dinga tashi na Kai kaga watarana kana yi,ke ai naga kinfi kokari wajen karatun Qur'ani da rana ki tayin abinki,Naila tace ai ni na Saba ma ya kamata ka dinga yi,yace ance miki bana yi ne? da asuba nake yi a masallaci amma bana yi da yawa gaskiya,tace good yaushe zan shiga makarantar Monday Tuesday din? ta matan aure ce ake zuwa da 9-12 Naila tace zan dinga zuwa,yace akwai ta Maza Kuma da ake yi a masallacin da nake zuwa duk sati ake dorawa kowa karatu Ina zuwa,Spark Yana zuwa duk sati amma sabo da lalacewa Aya biyu uku duk sati yake dorawa a haka ma watarana sai yayi sati biyu uku bai koma makarantar ba,Kuma idan zai tafi sai ya kankami katon Qur'ani Naila tana kallonsa tayi ta dariya ya iya ba wai Bai iya ba kawai dai zama ba Karin Ilimi da jaddada shi hatsari ne ga Musulmi,sabo da shagala da mantuwa,kullum Kuma Yana Jin wa'azi kala kala na malaman sunna a waya,idan ba a Jin wa'azi sai Addini yayi rauni shi yasa duk rintsi yake kokari a haka ma babu me ganewa sai Wanda ke zaune da shi shine zai gane halayen Spark. Misam Ango ya matsu tunda Naila ta fita yake bin ko Ina Yana kashe light duk ya kashe abubuwan wutar ya ja Chika suka haura sama,Chika tace gidan Nan yayi kyau,yace gobe Kya kalla yau dai ni zaki kalla,tace wanka zanyi yace bana son iyayin Nan na wanke wanken Nan na Amare,yanzu fa kika yi wankan da zanzo dauki ki sai kace wankan farilla duk Amarya sai ta tsiri wankan dare,ki bari mana Ina muka kaiwa Yahudawa hari sai kiyi me dalili amma yanzu wanka ba dalili, Chika ta fara shagwaba tana dire diren kafafu please ta shagwabe fuska,Misam duk sai ya sakwarkwace yace Alhmdllh da na samu wannan baiwar Allah, ni Sallar ma zan iya kuwa,Alwala yayi ya fito sai da yayi tsarki sabo da yanda yake ta fitar da ruwan jarabarsa,a gaggauce yayi Sallar sabo da kar ta karye Alwalar yayi addua yace me Amarya baya rike Alwala, Chika tace uhm tana harari ledar kaji,Misam bai ce aci ba