Sashe 26
Tantiriya A Gidan Yari Book 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
shi fa wato banda hankali? Mero tace kina da daidai naki hankalin mana amma ai ana haifar yaro yafi uwa hankali,ko ni ai nafi babata tunda tana zagin Baffan mu taci kwalarsa ni nake mata fada,Spark yace Mero na baki Arham ganin Arham ya shugo gidan da kakin sojojinsa,Arham yace ban karba ba wlh, Allah ya kiyaye ai gwara a bani Wahida duk da ta girmeni,Mima tace Allah ya Maka albarka na baka ita,gwara fa nace ba cewa nayi a bani ba,Wahida kyakyawa ce amma farin jini shi daga Allah yake bashi a kyau,ni bana sonta yace,Mima tayi shuru kawai. Mummy tace ke Mero tashi ki bar min gidana ayi kauye,Spark yace ba Inda zata je wai Yan aiki ba mutane bane, Dan kawai tace tana so na,duk uwa tana so ace ana son danta amma ku in mutum bashi da kudi Bai Isa ya motsa ba,yanzu wlh da wata Yar gidan me kudi ce tace tana so na da yanzu kuna murna Kuna cewa na Kara aure,amma sabo da tana karkashin ku tazo daga kauye,aiki fa taimakon juna ne mutum ya Maka aiki ka biya shi ai an taimaki juna,Dan Allah ki kyaleta ku Kun san ba sonta nake ba bazan Kuma Kara aure ba to mene laifi Dan tace tana so na? Mero na gode kinji Allah ya baki miji na gari,karki Kuma fadawa namiji kina sonsa,ki bari Allah zai kawo wani ya soki a yanda kike har kuka sai yayi a kanki. Mero hawaye ya zubo mata tace ni waye zai so ni bare ma yayi kuka ma a kaina,bani da ilimi,Yar kauye Kuma mu talakawa ne ai mu Kam bautar masu kudi muka zo duniya,Spark yace Baki sani ba Mero ko ki auri Wanda ya fini ma,tace to Allah yasa tunda Allah kace,ai dai kace kar na sake fadawa wani Ina sonsa ko? Spark yace ae ki dinga Jan aji kina yanga,tace to na gode,Naila hawaye take tace wlh bazan koma gidan kaba mayaudari,dama Abba yace namiji ba Dan goyo bane,Mima ta harari Naila tace ke komawa zakiyi sanda kike makale Masa duk rashin kunyar da kika mana wai ke me miji,Mummy ta tuntsire da dariya tace muyi zaman mu karki koma kinjim Spark ya zauna a gefen Naila ta matsa nesa tana fushi,Mummy da Mima farin ciki ya ishe su, Naila da Spark yau anyi fada,rada yayi wa Naila yace jibi zan kaiki gidanku Kano ki yini,Naila tace bana so itama cikin rada ta fada Masa tana goge hawaye,tashi tayi ta shige kitchen,abinci ta Gani Mummy ta shirya Naman ne ya birgeta ta dauki daya ta fito ta manta da muguntar Mummy ta fara cin Naman tuni,Mero ta kwala ihu tayi tsalle ta fisge Naman hannun Naila ta jefar. Tace kar kuci wallahi Mummy ta barbadawa Baseeru mijinta magani ko na mene ne oho,Spark zumbur ya mike yace wlh idan matata ta mutu sai kowa ya mutu,Naila ciki ta rike tace kwadayi na ya ja min shike nan Kuma ni a kaini asibiti wayyo Abba,Baseeru ne ya shugo ya samu abinda akeyi yace yawwa ke Mero kunna video a kwashe abinci a Kai su wajen gwaji idan ta tabbata gubar mutuwa ce to na shigar da Kara kotu. Mero ta kunna video ta nunawa Mima,ta nunawa Spark,Mummy hankalinta ya tashi sai gumi take,ta mike da gudu zata je ta kwashe abincin ta zubar Baseeru ya tare kofar kitchen ya jawo ya kulle ya sa key ya zare key din ya jefa a aljihu,Mima ce ta sake karbar video din ta gani tace Alhmdllh ko ma mene ba a Naman ta zuba ba a cikin Fried rice ta zuba gashi,Spark ya karba ya kalla yace duk da haka ban yarda ba ya dauki Naila suka tafi asibiti,aka auna komai na Naila,yace ayi mata medical checkup,komai a duba, a garin yin medical check up Likita yace Yana son ganinsu sabo da ko wanne test asibitin sunsyi indai kace medical check up to fa ba ruwansu matukar da kudi na komai ma sai sunyi Maka. Naila Likita suka samu a Office suka zauna gabanta na dukan tara tara ko wata masifar aka gano mata,Likita yace Spark matar nan taka a Ina ta girma ne? Spark yace a rigar Fulani,Likita yayi murmushi yace ai naji ma maganarta nayi zargin haka sannan mun mata test har na koyayen haihuwa,Spark yace na saku kuyi mata wannan,ni nace ayi mata har da shi? Likita yace Kai fa kace min duk wani text na tabbatar da lafiyar Dan Adam matarka kalau take ba wani Abu bane shawara zan baku. Spark yace Ina jinka idan ma ta hana sex ne bazan ji ba bazan hanu ba gwara ma karka fada,Likitan yayi murmushi yace ba shi bane,yace Mrs Spark kina Shan madarar shanu sosai wacce ba a dafa ba fresh? Naila tace sosai lokacin ma Baki muke sawa a Jikin nonon saniya idan mun raka Shanu kiwo,yace to a cikin nonon saniya madarar ba kindirmo ba,akwai wani sinadari a cikin nonon saniya wanda Yake kashe kwawayen haihuwar dan Adam, Ina so in tambayeki kin taba ganin wani cikakken dan Fulani na riga ya tara yara da mugun yawa? Naila tace a'a ai sunyi yawan gaske ka gansu da biyar wlh Mafi yawa cikakken dan Fulani na riga baya haihuwa da yawa duk da ana samun masu Haifar yara da yawa amma sai an tona,Likita yace to Alhmdllh cikin nonon saniya akwai wani sinadari Wanda ke kashewa mutum kwayayen haihuwa,idan an barshi an dafa ya zama kindirmo to sinadarin Yana mutuwa ko ya ragu yanda bazai cutar da mutum ba. Naila tace to yanzu Likita kwayayen nawa sun mutu na zama juya ko kuwa? Likita dariya yayi yace basu mutu ba amma duk kusan sun kare saura kadan,shawara zan baku a tattala kwayayen Nan indai kin samu ciki a kula da cikin sannan kar kiyi family planning Dan kwan ki basu da yawa kinyi sa'a ki haifi yara uku ko hudu,Spark yace to ni ai Alhmdllh wannan ai murna ya kamata kace zaka tayani,dama burina yara uku ko hudu,Likita yace Allah Yana da Iko akan komai zata iya ta Haifa su wuce Hakan ma, Spark yace wlh ni bazan bari matata tayi min kwanika ba planning zata yi,Likita yace kar ka bari tayi planning Yana kashe kwayayen mace,zai iya karasa mata su,Naila tace bazan yarda ba ma doctor wlh in kaga nayi planning sai dai idan na haifi hudu,Spark yace ai shike nan 'ya'ya sun fini ko?Idan ban haihu ba ai kishiya zaka min wlh bazan yarda ba babu wani soyayya da zaka rudeni da ita akan Jin dadinka,da Kaine kake so ban isa ba ai,Spark yace Likita ka hadamu fada ka kyauta ka barmu bamu San ikon Allah ba kaje Na'ura ta nuna Maka karya. Koda suka fito Naila tace ni dai mu dage da sex ko na samu da wuri kar Kwan su karasa,Spark ya kalleta yace Wanda ya yarda da Allah ya huta da baki sani ba fa? Duk wannan abin da nake ke bai Kai ki samu ciki ba? Naila tace a kara sauri gudu sau biyar tunda sau biyu sau uku muke yi,yace to bazan yi ba,yawan sex Yana taba kwakwalwar mutum sannan Yana sawa mutum ya rasa Ido da wuri,Naila tace karfin Gani yake karawa ai Halak dinka kake kallo,dariya ta bashi shi farin ciki yake zai more yace a wata majiyar haka naji ance Ido Yana Kara karfin gani Ina kallon Badon matarka,Naila tace ae mana Kai baka yarda ba? Allah sarki ai sai yau na tabbatar a bakinki,Naila tace af a fada mana ai mu mune muka san kan tsiyar,yace naga alama yanzu muje gida direct? tace Mummy fa ai gwara mu koma Muji wanne magani aka zubawa Baseeru,Spark yace ba zai wuce na mallaka ba, ni muje gida Dan Allah ki mallakeni a Bado,Naila tace to muje Allah yasa dai a samu ciki,Spark yace ke wannan ciki ya dame ki,to ta ya bazan samu Yar Minal dita ba na dinga mata kitso da kwalliya,Spark yayi murmushi Yana driving yace Allah yasa,Naila tace Ameen ko dan Mohsin dina in dinga Masa wankan swagg,Spark yace Ashe sunan Mohsin za a fara mayarwa? tace Inshaallah indai namiji ne Rabin raina zan saka Mohsin. Spark yace to yanzu Mohsin ya zama Rabin ranki ni Kuma a Ina nake? Naila tace Kai ai zuciyar ce gaba daya,hannunsa daya ya sa cikin na Naila tare da Maida hannun nata Saman Hallarensa,Naila ta Harare shi tana murmushi tace so kake muyi hatsari ta kwace hannunta. Abba ya baza kunne Yana Jiran Jauro yace baron mata Kai muke jira Karima yarrrrrrrrrr....ci gaba,Jauro ya bude baki ya Kalli Hashimu yace wlh sai na Sha ruwa,Abba yace Habiba hanzarta ki kawo a hado min da Jus wai Juice,Habiba ta kawo,Abba yace Jauro ka tuna yanda muke Shan ruwa a kauye mu kafa baki a Saman Moda kwat kwat kwat mun shanye Maza kayi irinsa bama son yanga tunda har ka koma ga Allah baza ka zama Dan birni ba,Jauro yace inji uban wa? to tsufa yazo Maka baka dawo birni da wuri ba kafin kayi Shekara arba'in ai ka tafi Ingila me tukane Kuma,Jauro yace na daina biye Maka Hashimu naga alama ka kama hayar gida a Zaria,sai da su Annoor suka yi dariya sabo da wai Abba ya fara zarewa shine ya kama hayar gida a Zaria,Abba yace a'a ka manta gida na siya a zaria,shi Kuma Abba yace Jauro kafin ya zama cikakken Dan birni ya mutu Yana kabari shine Ingila me tukane,Haidar yace sabo da ana binne mutum da tukunyar kasa shine wai Ingila me tukwane,Nabeel yace ku Kuna da bakin magana ma yanzu,Haidar yace kashe kanmu zamu yi tunda iyayenmu sun biyewa Dan dadi na mintuna an haifo mu ya zamu yi. Jauro yace Karima....Abba yace ae Karima muna ji,Jauro yace Karima a wani kauye tudun wada Dake Kano state, Allah ya kaini wajen wani abokina Inda a asibitin Tudun wada yake aiki,Likitan amma yayi kaurin suna wajen zubar da cikin shege,a asibitin sa private sana'arsa kenan zubar da ciki,muna zaune muna Hira sai ga wani Arne Igbo me suna Dennis,ya kawo wata mace bahaushiya Yar Fulani me suna Saratu,ya kawo yarinya karama ce lokacin sai kayan nonuwa kamar tulu haka take randamdam