Sashe 80
Tantiriya A Gidan Yari Book 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
tace Maryam din fa? shuru ya mata,sharewa tayi tace abinci Yana jiranka ta ja Masa kujera ya zauna tare da serving dinsa,ta zubawa kanta ta zauna itama,yau baza ki bani a bakin ba? Maryam ta baka,taci gaba da cin abincinta kamar ba itace tayi maganar ba,Murmushi yayi ya fara cin abinsa Yana kallonta,dakogowa tayi suka hada Ido, baki ta murguda Masa ta janye idonta daga cikin nasa. Bayan su Annoor sun tafi Abba shi dai ta fiya yayi,Yana zuwa gida ya samu Yar Inna ta cakare cikin Leshi fari yaji doguwar riga ta tsege dauri sai kace matar wani Gomna ta zauna a Palo tana gogewa Hashimu kayan sawa,sau tari kayansa marasa nauyi ita take wankewa ta goge masa,Kubra ta daure fuska da gaske take fushi da Hashimu,Abba ya kalleta yace kinyi a banza fushi da Hashimu aikin banza kenan,kamar baki sanni ba haba Yar Inna,na tuba nace bazan sake ba,yau wurin sati guda ko daki bama hadawa har sai yara sun gane,na gaji zan fadawa Mohsin. Da sauri Kubra tace ka fadawa Mohsin Kuma? ae mana shi ya miki fada ai Kinga kinji kunya danki ya miki fada,Yar karamar yarsa ya dauka wacce take zama yanzu Yana mata wasa yace yarinya Yaya kike jiye min kamshin Yar Inna Yana nan ko kuwa ta daina sawa,ni nasan ta daina saka turaren yanzu tunda bama kwana tare dama Dan na yaba ake sawa to bani Ina zata saka,Yar Inna saura kadan tayi dariya ta daure tace Allah ya kiyaye na fasa shafa turare ni dama badan kai nake sawa ba. Abba yaci gaba da yiwa yarsa rawa tana dariya yarinya yace ke kadai yanzu kike kula nononki ko Yar nan? Dariya Kubra tayi tace ajiye min 'Yata karka lalata min ita,wayar Yar Inna ce tayi Kara" Hashimu ya duba yaga Naila,daga kiran yayi,Naila tace Abba" yace Na'am"gaisawa suka yi tace Ina Umma fa? Yace gata tana fushi,ai fushi take dani mun Kai sati a haka taki hakura,Kubra tana ji bata kulasu ba,Naila tace Abba zata hakura ne,yace Abu yaki ci yaki cinyewa,ka Murda kambunka kawai Abba cewar Naila'' wanne kambu nake da shi Naila ni ba champion ba,ita ce take da Kambun ai,Bata wayar to,Abba ya mikawa Kubra ta karba,Naila tace Umma Ina yini'' ta amsa da lfy ya gida ya mijin naki? Lafiya Alhmdllh,lafiya dai ko? Naila tace dama shawara zaki bani Gani nayi kamar Spark ya juya min baya,Dariya Umma tayi,tace me yayi Kuma,Naila tace to tsakani da Allah Umma yau 3days bai kwalbe ba,dariya Naila ta bawa Kubra sosai,tace me yake yi to,tace daga Office sai bacci,in ya dawo da wuri da wuri ma laptop yake sawa a gaba da takardu ya dinga fama sai ya Kai dare sosai har sai nayi bacci,Kuma a rana sai yaje state biyu uku kullum aiki,gaskiya na gaji ni zamuyi fada da shi,Kubra tace ke yanzu Baki gane aiki ne ya Masa yawa ba,aiki ne ya taso Masa baki san Maza ba kenan,kika San me ya taso Masa ya sashi hakan Koma ba aiki bane ai ba kullum ake kwana a gado ba,dole watarana a samu canji,ki daina damun kanki,abinda kike dai karki fasa Kuma ki koyi juriya a ko wanne hali kika tsinci kanki kiyi hakuri,bare ma aiki ne yasa shi,duk bake kike cinye kudin nasa ba,Naila tace har watana nawa da zan cinye kudinsa kin Kai dai wata biyar ko shida tunda cikin Beauty gashi ya fito ma,Naila tace uhm to shike nan Umma zan jure,Ina Hidaya? ta tafi lalle gobe za a kaita gidan miji,Kiwa mijinki godiya dubu dari biyar ya bamu,duk da Nabeel din ya zuba komai na kayan daki sai da ya Bada kudi,abinda muke so aka Kara siya mata,Baki ga gidan Hidaya ba Mashaallah yayi gida na gaske,Kinga kayan ciki du na kasar waje,kitchen ne ba a zuba abubuwa da yawa ba amma duk mun siya an zuba mata komai,zan tura miki ta Whatsapp ki Gani,Naila tace Alhmdllh ai ta turo min Lefenta gaskiya sunyi,Umma tace ai mu sai godiya ga Allah ta ko Ina rufa mana asiri Allah yake Naila tace ai kuwa Alhmdllh. Gobe karfe nawa za a kaita? 5pm suka ce zasu zo daukan Amarya gidanta kusa da gidan Iman Inda Annoor yake,Naila tace shike nan tayi Kawa sai su zauna lafiya kar a dinga kishin faccalanci kishin banza mijin kowa daban amma mata suna kishi, Inshaallah baza suyi ba,Allah yasa cewar Naila tana cewa Umma Dan Allah ki daina fushi da Abba kiyi hakuri,ke Ina ruwanki bana son rashin kunya fa ai dama kunfi sonshi,Naila tace mudai Dan Allah a yafe masa Yar Innar Abba....tana fadar haka ta kashe wayar tasan Umma yanzu sai ta zageta. Wayar ta kalla tace Naila wlh bata da kunya,Abba yace sabo da ta baki hakuri dan Allah kawo min abincina ki ta fushinki,Yar Inna ta mike taje ta kawo Masa abincin,ya bude flask din yace ya naga jullof? tace ae ai tunda naji kana son Alala na fasa yi tunda haushinka nake ji,Abba yace to bazan ci shinkafar ba ni,tace baza Kaci ba? Yace ae bazan ci ba Allah yasa na iya girkin bare ayi min yanga,Abba ya mike ya dauki showel din Baby ya Goyata Charas a bayansa sannan ya mike ya shiga kitchen,ya dora girkinsa,Yar Inna tana kallonsa yana aikinsa,kitchen din ta shiga ta sauke tukunyar,yace mene haka zan Sumar dake,dariya tayi ba shiri tasan ta Ina zai iya ko Marinta ma bare sumarwa,tace dan Allah kayi hakuri kazo kaci abincin nan nawa,Abba yace sai dai kici abinki ni kya min iyayi akan abinci,sabo da Allah mutum yayi ta fushi yaki ci yaki cinyewa,ya dauki tukunyarsa ya Maida saman gas,tace Dan Allah kayi hakuri Kaci wannan,yace wlh bazan ci ba na rantse in ma baza ki bari na dafa ba sai naje na siya,ni ba fushi nayi ba kawai bana son jullof dinne,to me zaka ci? Indomie da kwai zan dafa,to ka bari zan dafa Maka,haka ya hakura ya barta ta dafa Masa,gaf da magriba su Hidaya suka dawo daga lalle tare da Zarah,Abba yace kuzo naga lallen Nan,suka nuna Masa yace gaskiya ta iya Amarya kar fa kisa Ango idonsa ya fado,dariya suka yi,Yace to sai kuje kuyi wanka,Yau Abba Yana zamansa sai ga Yar Inna ta kawo kanta tazo dakinsa ta kwanta,yace kin dawo kenan,tace ae na dawo ko na tafi? Abba yace a'a ni na isa Yar Inna guda. Jauro yau gidan Amarya zai kwana,tana gidansa tare da Habiba uwar gida har dare Jauro yace taso muje na ajiye ki a gida,Habiba tace sai da safe dai Malam,Jauro harda cewa ban taba kwana a gidan wani ba sai yau ki gafarce ni Habiba,Habiba tace kaji da shi in zaka tafi ka tafi dai,fitowa suka yi da Amarya zasu tafi,Haidar,Nabeel,Rahma da Nabeela suna Palo Jauro ya fito ko kunya yace sai da safen ku,Haidar yace bye Kawu,Nabeel ya fara boye dariya,Rahma tace Kawu sai gobe azo dai a duba lafiyar mu,Kawu yace sabo da rashin Imani Rahma in kuka ganni gobe kuce to da matsala,ya juya ya tafi" ita dai Amarya tuni ta fice kunya take ji. Suna tafiya Nabeel yace yau Kawu za aci sabon balangu,suka kwashe da dariya,Haidar yace kaima ai gobe ne dai zaka ci naka balangun,Nabeel yace irin na karamar Dabba kuwa,Haidar yace to wlh karni zaiyi,yace Dan uwarka ba na kamar Dabbar turawa taji kiwo me Mai,kaga maiko zata yi,to zaka ce na karamar Dabba namanta in banda yauki da karni me zaiyi,Nabeel yace uhm nidai nayi shuru yara na wajen. Rahma tace sai da ka gama sannan kace muna wajen. Chika ce da Misam suke hayaniya su kadai sun cika Palo ka rantse Baki suka yi,kamar yara sai wasa suke kala kala suna dariya,Yana zaune Chika ta haye Saman kafadunsa dokin wuyansa,Mima ce tayi sallama tare da shigowa ciki,Chika tashi tayi gata da wasu shegun guntayen kaya a jikinta,bum short da riga,ba kunya ce da su duk da haka dai taga ai uwarsa ce sannu da zuwa ta furta tace bari nazo ta juya ta haura sama da sauri,abin mamaki Mima bata ce komai ba,sai ma cewa tayi Kuna ta kaya kaya wlh na zaci bakin yara kuka yi jibi Palo yanda kuka Masa pillows din kujeru duk a kasa,ai lokacinku ne kuyi. Misam ya mike tare da zama yace Ina yini Mima,ta amsa da fara'a tace tunda kayi fushi baza kazo ba gashi na sake zuwa ni,uwa ai bata fushi da danta,kiyi hakuri zanzo ne,ba wani zaka zo tun yaushe kake fadar Hakan ka kasa zuwa,ance haushi kaji munce ba bikinka muke ba na Rafeeq muke yi,Misam yace ni dan Baku yi bikina ba sai naji haushi kawai,Mima tace Gani nayi kai da Rafeeq ai duk daya,Misam yace yanzu ba kwace haka mana" koma mene ya wuce Mima,ya gida kwana biyu banga su Arham ba,sun samu shinkafa ai dole ka daina ganinsu,Misam yace Papa yaki dawowa dai,Mima harda hawaye tace abinda ya dameni kenan Misam,shine a gabana,Dan Allah ku roke shi ya dawo dan Allah,Misam yace to munyi munyi yaki ya ma daina daga wayar mu,Mima tace yau ni na shiga uku Kuma a rayuwa,kiyi hakuri zai huce ne,sai yaushe sabo da Allah sai yaushe? cewar Mima tana hawaye,da kyar Misam ya lallashe ta tayi shuru ta goge hawayenta,tace ni nace Masa wlh na tuba ko me yake so yanzu zan canja hali Kuma zan gyara Kuskurena Inshaallah,idan ma ya Kara auren ya taho da matar mu zauna tare,Zai hakura Inshaallah cewar Misam. Chika ce ta fito cikin doguwar rigar material ta fito ta durkusa ta gaida Mima ta amsa Kuma harda sakin fuska,Chika tana ta mamaki a ranta ta mike ta shiga kitchen tana cewa shike nan naci banza,rashin kunyar da nayi mata kafin na auri Danta naci banza,naci banza...naci banza...naci banza....tana yi da Waka harda rawa,a hankali ta leko da kanta tana kallon Mima da Misam suna Hira ta cunowa Mima baki tace naci banza a hankali yanda ba me ji,ta washe baki tana dariya marar sauti tace Kai wallahi naci banza tayi hankali,na gaisheta ta amsa harda fara'a,kitchen ta dawo gaba daya ta shirya abinci da na Sha ta shirya a dining ta fito tace Mima ga Abinci Mima ba a wuce tayi yanzu tace kawo min nan ni yanzu Dining table