Sashe 79
Tantiriya A Gidan Yari Book 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
wata uku a dakin Amarya sai kice sati daya kacal sabo da dama ku gidanku Habiba gadon rowa kuka yi wlh,madarar shanu bakwa iya kyautarta,sanda kike tallan fura wacce irin tsada ce baki ba,ana ganinki da kwaryar nono har nunaki ake da baki ga uwar tsada can. Jauro yace karka takurawa matata Kai Yar Innar taka mene bata yi ba,Abba ya gyara zamansa yace Yar Inna ta hau dokin zuciya fushi take dani kwana da kwanaki taki sakkowa,abin ya dameni Kuma Ina Jin Mohsin zan fadawa yazo ya tare min fadan nan,muna zaman mu lafiya na takalowa kaina yanzu gashi Yar Inna ta juya min baya,Jauro ya dinga dariya yace Allah ya Kara,idan ance Maka Dolo kaji haushi,Abba yace ka taba ji nace naji haushi in an ce min Dolo? Ni bana Jin haushi Wanda ya fada shine a wahale bakinsa ke aiki. Maman Annoor kunyar Habiba take ji duk ta kasa magana,Abba yace to Habiba uwargida Kinga hukuncin Allah,haka Allah ya tsara kiyi hakuri da abinda aka miki,ba wai mun Kara aure bane Dan aci mutuncinki ba,Jauro yace ban gane mun Kara aure ba? Na Kara aure dai Kai Ina ruwanka a ciki ,wai Hashimu ko da Kai zamu shiga dakin Amarya ne? Abba mikewa yayi yace a'a Allah baka hakuri tunda baka gane hausar ba,ni na shiga dakin matar wani Allah ya tsare min,Jauro yace to zauna mana a karasa Abba yace a'a,Habiba tace Dan Allah ka zauna a kashe wutar Annoor tukun,da kyar Abba ya zauna,Abba baya fushi ba a fada da shi,yace ai ni Yar Inna yau Alala take mana,idan banci akan lokaci ba akwai kura,dama kadan take jira fushi take yi. Ba a dade ba sai ga Maryam tayi Sallama cikin katon Hijab dinta har kasa,tayi shigar Kamala,ta shugo ta zube a kasa tana ladabi ta durkusa ta gaida su da ladabi,suka amsa,Habiba tace kece Maryam din? Maryam tana kasa da Kai ta dago fuskarta tace nice,Maman Annoor ce ta Mike da sauri tana nuna Maryam da yatsa tare da kiran sunanta tace Maryam kece? Maryam tace kin sanni ne? tace kece dai baki gane ni ba,Ina mahaifinki? tace Yana US Bai dawo ba,Maman Annoor tace to ai ke shirme kike yi Annoor din Yayanki ne Ubanku daya da shi,babu aure a tsakaninku idan baki yarda ba kira mahaifinki yanzu kice waye Annoor. Maryam gigicewa tayi ta rude ta dakko wayarta a jaka tare da kiran Mahaifinta a waya,bayan sun gaisa tace Daddy wai dama kana da Da Annoor? Daddy yace Ina Annoor din? Dan Allah hadani da shi ya girma sosai Ina da pictures dinsa mahaifiyarsa ta tura min ta Whatsapp,Allah sarki ai ubanku Daya Maryam Yayanki ne shine Dana na farko,na zalunci mahaifiyarsa na zalunce shi,Allah yasa mahaifiyarsa ta yafe min,na nemi yafiyarta,yanzu shi kawai ya rage min, inshaallah next week zan zo Nigeria ki kaini Inda yake. Maryam tuni ta fara kuka tana hawaye ta durkushe a wajen tace Dan Allah ku kira Annoor zan tonawa kaina asiri,wlh ban san Dan uwana bane na jini,ban sani ba na cutar da shi,shi yasa aka ce in Allah bai baka Abu ba karka sake kace Kai ta dole sai ka same shi. Habiba tashi tayi taje ta dinga knocking tuni sunyi bacci har Iman din,da kyar Iman ta farka tace Ina zuwa,kayanta ta Maida jikinta tare da bude kofarta tace Umma,Habiba tace taso Annoor ku fito" tana fadar haka ta juya,Iman tashinsa tayi da kyar ya tashi ya zauna kayan ma sai da ta tayashi ya saka sabo sangarta,tace muje Umma suna kira,yace Allah yasa sun Nemo Maryam din na ganta,hannun sa Iman ta kama ta gartsa Masa cizo,ya saki Kara suka fito Yana yarfe hannu. Yana fitowa yaga Maryam a zaune tana sharbar kuka,Abba yace Iman ku zauna,zama suka yi,baka Jin komai sai sautun kukan Maryam,tace dan Allah Annoor ku yafe min,na cutar da ku nasa kunyi Zina Bada saninku ba,tana kuka tana basu labarin yanda akayi duk ta kaisu hotel har Annoor yayi amfani da Iman basa cikin hayyacinsu,sannan ta Fadi duk irin asirin data dinga musu,tace wannan na karshe shine na sa Masa a kasan kujera ya zauna,Iman ta jawo Jakarta ta zaro Dan kwallon abin kamar carbi ta nunawa Maryam tace shine wannan? Maryam tace shi...shi....shine,Annoor yaji komai amma kala bazai iya cewa ba,tsafi Yana jikinsa,Iman tashi tayi ta rufe Maryam da duka da cizo da yakushi,Maryam tana kuka,Abba yace kyaleta Iman ko me zaki yi baza ki iya ramawa ba,cuta ce ta cutar da ku,amma wannan yarinya ke dai lokacin Jima'in cikinki tare babanki yayi da shedan lokaci guda suka aiwatar da shedan,Jauro yace tambadaddiya ba duk yanda aka yi a nono ta tsotso. Cabdi cewar Habiba sai ki je ki karya tsafin naki ko,Maryam ta mike ta fice da gudu tana kuka,motarta ta shiga a lokacin ta wuce kauye wajen Malamin da yayiwa Annoor tsafin hanashi mu'amular aure,tana zuwa taci sa'a Yana Nan,tace Malam ka taimakeni Wanda na baka aiki a kansa kayi min Dan uwana nane na jini ubanmu daya,Malam yace na baki shawara ai tun farko kika dage. Maryam tace da me yasa baka fada min Dan uwana bane tunda Kuna duba ai sai ka sani,Malam yace Allah ne yasan gaibu,Maryam tana harararsa tace ku dai makaryata,Yace ke ki shiga hankalinki badan Ina Tausayin yaron ba wlh bazan karya ba,sai na kassara rayuwarki,shuru Maryam tayi tace nawa zan biya yace dubu Hamsim,haka ta bashi akan ya karya aikin,wani garin magani ya bata yace kije ki zuba garin Nan na magani a hannunki ki kira sunansa sau uku sannan ki bushe garin yabi iska shike nan,Maryam tace zan iya yi a Nan garin? Yace ko a Ina ma,ta karba ta fito ta shiga motarta sai da tayi Nisa da garin sannan ta aiwatar da abinda Malamin ya sata sannan ta shiga mota ta dauki hanya,a ranar ta dawo kusan dare ma ta nemi jirgi ta tafi kudu,can ma haka ta kashe kudi mutumin yace idan ya karya sai ta kwanta doguwar jinya,tace ba komai aka karya asirin. Kawu ne ya kira sunan Iman ku tafi gida to kawai Inshaallah zai karye,Annoor ya mike kawai ya fita Yana takunsa na zaratan matasa,Iman ta bishi kamar kurame ba Wanda ke kula wani,haka driver ya Maida su gida,suna shiga Palo ya rike hannun Iman ya fisgota idanuwansa cikin nata" haka kawai kamar zai dake ta" ya furta da izinin wa kika fita kika je Office dina? Iman tace da Izinin kaina da kaina,naje din fitar tawa ai tayi amfani tunda gashi nan da naje ai tattabeka akeyi dama kullum,haba shi yasa Dan hutun amarci ma kaki yi,Ina da operation yau,jibi Ina da wani marar lafiya critical condition,critical condition ashe Maryam ce take baka critical condition a jikinka, maimakon nayi aure nayi kiba kullum sai ramewa nake yi Ina Dan wuya sabo da halinka,auren zumunci ko tsiya a dake ka a hanaka kuka,Annoor Yana ta kallonta sai masifa take shi da ta yiwa laifi ta bishi Office ba izinin sa. Sai da ta gama tace Kuma wlh baka isa ka min kishiya ba,babu kishiya sai dai ka sake ni,haka kawai da me zanji,ko tarihina ya isa ka tausaya min,ai dai ko da asiri to shima Yana iske hali,dama wa yasan me kake yi in ka fita,wasu likitoci wani tsoron Allah ne da ku dama,in ka fita dama haka kake yi da ma'aikatanka idan bakwa yi ta ya zaka bari ta dinga tabaka direct. Annoor sai da ya bari ta gama sannan yace Iman ni kike fadawa haka? ae din Kai matsa can ko Dan ka rainani nima fa shegiyar kaina ce,dariya yayi kawai yace to Mama Iman zo ki dake ni mana kawai. Iman sama ta haura da sauri,zama yayi a rantsatsen palon nasu Wanda ya gaji da haduwa ba abinda yake sai kamshi,kwanciya yayi Yana dafe kansa da yake Masa ciwo,Iman bata sake fitowa ba sai da ta Dade Sannan ta fito sanye da guntuwar gown wacce da kadan ta wuce mazaunanta,Yana kwance ya lumshe Ido yaji taku ya Dan bude idonsa kadan,Iman ce ta wuce tana tafiyarta tana latsa waya,idonsa ya lumshe da sauri yace Annoor ba kayan aiki namijin hotiho ga Abu amma ba dama,yanzu ko tabawa nayi shike nan kadarina ya karye Kuma,Bai san an karya asirin ba yaki yarda ya taba Iman,Inda yake tazo zata zauna tace matsa ko na zauna a kanka,tashi yayi ta zauna ya kwanta tare da dora kansa a cinyarta,gashinsa ta shafa tace ya jikin? yace Ina ruwanki ba tafiyarki kika yi ba,dariya tayi tace to kayi hakuri haushi naji, kawai kin rainani sabo da ba abinda nake iya tsinana miki,wanne irin ba abinda kake tsinana min? Ba fa haka bane kawai kishi nake yi Kuma kasan ya zama dole tunda Ina sonka,haka dai kika ce amma ni nasan kawai Dan ba abinda nake baki ne,ba haka bane haba Beb ta shafo gemunsa tana murmushi,kanta ta duko a hankali tare da Dora lips dinta Saman nasa ta shiga tsotsa tace yau fyade zanwa mutum ko Banana tayi aiki ko kar tayi dole ma tayi,dariya yayi ba shiri yace Allah sarki Sweetener tana rashin lafiya, amma fa kina kiss din nan ta mike so take ta kawo nasan baza ta Kara 1mnt ba sai ta kawo,Iman ta mike tace bari na kawo Maka fruits" ta mike ta shige kitchen ta fito dauke da bowl ta kawo Masa gabansa da fork spoon a ciki suka fara aikin Shan fruits din,tace me zan dafa ne yau? Yace komai da nake ci ai kin sani in ma baza ki dafa bama a fadawa Rahma ta kawo mana daga gida,ko nayi mana order, Iman tace zan iya mana,Kitchen ta shiga ta dora girkin,miyar jajjage tayi da kifi sannan ta dafa musu farar shinkafa ta hada couslow tayi lafiyayyen zobo ta tafasa da bawon Abarba da kayan kamshi,bayan ya huce tayi blending Banana ta juye a ciki ta zuba sugar yayi mugun dadi ga amfani a Jikin Dan Adam ta shirya a dining sannan ta ganshi ya fito da alama wanka yayi cikin t-shirt fara me gajeren hannu da 3qutr yayi kyau matuka sai kamshi yake,gabansa ta karaso tana murmushi ta furta kayi kyau,Hugging dinta yayi gaba daya a jikinsa tare da furta I love you" da shagwaba