← Book details Tantiriya A Gidan Yari Book 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 63 OF 87

Sashe 63

Tantiriya A Gidan Yari Book 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

AsmaBaffa [1/27, 10:32 PM] AsmaBaffa: TANTIRIYA A GIDAN YARI BOOK 2 ~YARAN JAURO~ 76-80 Official AsmaBaffa SADAUKARWA NE GA AIDA MAMAN TASNIM PAGE NAKI NE Maman Murtala Mima sai da suka shirya tsaf ba motar shiga a gidan kaf tace yanzu taxi dole zamu shiga sabo da idan nace lallai mota zan Nemo asirinmu zai tonu,fita suka yi suka shiga taxi zuwa gidan Rafeeq,suna zuwa suka ji kida ta window palon suka leka suka hango Malama Ikhram da Ango Rafeeq suna ta Yar rawar su irin ta turawa cike da nishadi,Mima bakin ciki yazo mata wuya tace wai me siyar da maganin gargajiya na mata Allah ya sawwake ta Murda kofar Tare da banko ta ciki,Rafeeq ya juyo ya gansu yace lafiya? Mima ta fisgo Hannun Ikhram tace yau sai kin tafi gidan ubanki ne?,Ikhram Jikin Mima ta fada sannu da zuwa Miman mu, Mima ta fara banbareta daga jikinta amma taki sakin Mima,Rafeeq yace Allah sarki kaunar surukai ta motsa,Mima ta ture Ikhram ta karfin gaske tana zage zage,su Anan sun tsaya suna mata wani Shekeke,Mufee tace aikin banza anzo cin arziki,Ikhram tace sannunku masu arziki Ina abin yake idan aka yi comparing da kudin wani ai talakawa zaku tashi,Ke ki kiyayeni na fiki iskanci wlh ni bazan dauki raini ba,ba wacce ta isa ta takani,mahaifiya dai zan iya mata biyayya amma ba ku ba,ai ko yayyensa ne baku isa ba,masu takama da kudin Uba sai ku bari ku nemi naku tukun,wannan jahilci ne da hauka da kauyenci ko ince gidadanci menene Hakan? Mima tace to fitsarriya wato ke kunyar Amaryar ma babu,Ikhram tace Ina na ganta dama Banda ita Baku ga irin wa'azin da nake bane ai Kinsan kunya babu,wai Nan kunya kuke nema a wajena Allah sarki ai ban San Inda take ba Dan ni ban taba haduwa da ita ba, Ikhram tana magana tana fari tana jujjuya idanu kamar ta Sha kwaya,Rafeeq shi Kam ya mato sai kallonta yake kamar ya samu tv, Anam tace bari na dakko mana lemo, Ikhram tace Baki isa ba ko kitchen dinki ne ,zata wuce ta fisgota baya,Haly ta taso zata mareta Ikhram tace Inama Allah yasa kin mareni yau Kisha kallon yanda ake Hawa bori da tsakar rana,da na nuna miki baki da hankali. Dai dai nake da kowa ni ke nifa Aljani ma da zan ganshi in ya zageni sai na rama wlh,ni kizo Ina auren Yayanki kice zaki mareni ai kuwa da anyi ta yau,Mima tace kuzo mu tafi ,Taga masifar Ikhram kamar baza ta kare ba, Yar gidan waye ke sai na binciko tsatson ki cewar Mima,Ikhram bata yi magana ba sabon da ai uwar miji ce,zadai ta kula yaran, ta zauna albarkacin Rafeeq baza ta kulata ba uwa ai uwa ce,Rafeeq yace Mima Ina zaku je ne haka?Mima kamar tayi kuka suka dai fice suka tafi gidan Misam sabo da bankada,lokacin Chika ce kawai taji ana kwankwasa kofa,lekawa tayi ta Yar kafa Taga sune kawai tayi wucewarta taki budewa bugawar duniya taki budewa,sai tace Ina zuwa sai suji shuru,suka sake bugawa tana Jikin kofar tace Ina zuwa amma shuru kake ji sun San Kuma suna gida,Mima tace muje kawai haka suka juya suka tafi gidan Spark, Yana kwance yayi pillow da cinyar Naila tana karanta Masa Abu a waya Mima suka banko kofa ba sallama bare kwankwasawa. Yace sai kace yaki ai Kun bani tsoro Mima bai kamata ki biyewa yara ba da girmanki,kaga karka dameni,Mima zama tayi tace gaya min tsakanin ka da Allah Spark Ina Papan ku? Spark yace tunda kince tsakani da Allah bari na fada miki,Naila tashi tayi ta durkusa tace Ina yini,Mima a lokacin tasan Naila ba karamar me ladabi bace, amsawa tayi da sakin fuska,lemo ta kawo musu da ruwa,sannan ta basu waje,Spark yace Papa yana Gaza kasa ta turasu su taimakawa Palestinian,Hannaye Mima ta dora a Kai tace shike nan kace sun tura su a kashe su,wacce kasa za a biyewa wannan kasar har wata kasar arziki ce da zata tura mutum Abu kuma ya tafi yayi,Arham ne ya fito daga kitchen ashe da yace a basar aci tuwo Nan ya gudo yake ta girke girkensa,Mima tace yaushe ka riga mu barin gidan? Arham yayi murmushi yace tuwo ne kawai naji dadinsa shi yasa Inda kisan na shiga jirgi. Mima tace banza taci gaba da magana da Spark tace yanzu ba wata hanya da zai dawo ni wlh gwara ya bar aikin Nan,Amma kuka bar mu muka saki baki muna bacci hankali kwance bayan mahaifinku Yana can cikin wani hali,gaba daya Mima ta tashi hankalinta,Spark yace yanzu me kuke so a kawo muku na abincin? Mima tace Kai dalla yi min shuru wa yake ta abinci mijina Yana tsaka me wuya,ni dai duniyar ta min zafi gaba daya,Arham tashi yayi ya karo karfin AC yace yanzu dai dole kiji sanyin duniya,Mima tashi tayi tace Dan ubanka wai ni sa'arka ce? Ko kakarka ce ni,ta rike Arham tare da mamake Masa Kai,Arham Yana dariya yace kar dai Kiga Ina kama da Papa ki zaci shine ki bari ya dawo sai kuyi soyayyar ku. Naila tana fitowa Taga duk sun shanye lemon akan kwana biyu kawai da basu samu me dadi ba,kitchen ta shiga tana dariya tace bari nayi tsokana ta fito tace ko a kawo muku tea? Haly tace da Madara Dan Allah,taje ta hado musu lafiyayyen tea kowacce ta kawo mata a katon cup har Mummy,Anam tace bread Dan Allah,taje ta kawo musu tace ko a soya muku kwai da chips? da sauri suka ce ei,Spark yace ba sunci tuwon su ba a gida Yana hararar Naila,Naila Bata San horo ake musu ba,taje duk ta soyo ta kawo,Mima tace Allah sarki ta Rafeeq kuwa da ta dinga bala'i tafi 30mnt sai kace me aljanu,Haly tace ni na taba ganin jaraba irin wannan daga magana,Anam tace gwara ita sai da muka tsokaneta waccen marar mutuncin wlh kin budewa tayi ma Sam,Spark Yana jinsu yace ato in baku gode Ni'imar Allah ba ai Kwa gode Azabarsa. Suna zaune gidan Naila kamar kar su tafi dadi ko Ina Kal Kal Yana kamshi ga girke girke sai kawo musu take,minti kadan ta kawo wani abin,Arham Yana ta dariya yace sabo da rashin hakuri wai kwana biyu kawai shine suka koma kamar mayu,Mima har dare tana Jimamin mijinta hankalinta a tashe,Spark ya kwanta a doguwar kujera ya kira Naila dake kitchen Baby....na'am ta amsa zo ki min tausa,Mima tace kaifa Dan iska ne a gaban namu ga kannenka,yace matata ce fa Mima ba Karuwa na kawo ba,nifa babu me zuwa ya takura min a gidana in baza ku iya Gani ba ku tashi,yanzu Spark gobe ma tuwo yara zasu ci? Spark yace ku jika gero ku Kai markade mana ayi musu Koko,Mima tace Koko fa? Yace to za a siyo wake sai ku dinga hadawa da kosai,Wannan madarar da sugar da ka kawo ai sunyi kadan Kuma bama Shan Madara Yar awo,Mima da ita fa ake Albishir da alawar Madara mudai muna so cewar Arham,Mima tace kaga Arham idan Ina magana kana sa min Baki kana bani amsa sai na taka maka wuya wlh,yace sai kace zakara za a yanka,Mikewa Mima tayi tace bar nan wajen ko na hada kanka da bango. Mima tace ku tashi mu tafi,Spark yace ku tsaya driver ya kaiku,Mima taji Haushi gidansa kayan dadi su yaki siya musu tace bar mu ai taxi muka shugo mu koma a ciki,yace to ku gaida da gida,Arham yace Nidai a dinga girki Dani a nan dan Allah yau Ina gidan nan gobe kwanona na gidan Rafeeq jibi kwano na Yana gidan Misam. Spark yace kowa yaci na gidansu,Banda gidana idan hakane to sai dai ka dauki gida daya ka dinga zuwa kana ci,ni nan banda gidana nifa babu me takura min Ina so in sake a dinga kallona,Arham yace kuyi kiss dinku da rungumemeniyar ku bazan kalle ku ba,ai gwara na baka kudin Abinci kullum kaje ka siya,yace yawwa tura min,plate biyu kullum nawa,yace to Hakan ma yayi. Sai da ya bar gidan yaje gidan Rafeeq,Rafeeq Yana zaune Ikhram tana Saman cinyarsa ya shugo taki tashi Kuma,Arham yace ana ta Shan chaji ne? Rafeeq ya mika Masa hannu suka gaisa yace dan Allah ya kaji dumi da muka gaisa?,Arham yana dariya yace a naji zafi zauu,Rafeeq ya nuna kan Ikhram da yatsa wacce tace Arham barka da zuwa yace yawwa,Mikewa zata yi Rafeeq ya rike ta,tana shagwaba tace pls...,sakinta yayi ta tashi tare da wucewa kitchen,Arham ya leka Rafeeq yace mu gani Hallare tana aiki,Dariya Rafeeq yayi harda wani bajewa zaman ma ya wani bubbuda kafa ya kwanta tare da nutsewa a cikin kujera,ga Hallare a mike ko a jikinsa,Arham yace nan zaman angwaye ne haka? Rafeeq ba tare da yayi magana yace hutawa na barta tana yi na bata wahala Kai shege ne ni,na bata kuka ranar da Sai ga sabon Ladabi da sanyin Safiya,yanzu ko fuska na bata sai anji dalilin fushina,Wayyo Ina ganin gata,Arham yace uhm Allah ya baku ku Kuwa,Rafeeq yace sanda Ina Gwauro da ruwan Sanyi nake wanka yanzu kuwa tace ban isa ba ta hana,Arham yace ka yarda Kuma yace wane ubana ba dole ba. Arham yace hmm ni ba macen da ta isa ta sani ko ta hanani,Rafeeq yace tab ni kuwa gani,girki Dan ubanka a jera min hadaddun flask ana ci mana,Ina sani nace na koshi,a dinga lallabani Kaci pls My Heart,ba sai naji Kuma na koma shagwababbe ba ahh sai shagwaba ana Lilita ni,Arham Yana ta dariya yace yanzu duk a 2days aka yi haka? Ana amarci da wasa ne Malam babu lokacin banza a amarci every single minute,second a ciki Jin dadi ake tunda mun gaisa tashi kafin Dan Allah,Ikhram ce ta fito dauke da abinci tace Ango na biyu....mene ne haka? Waye Ango na biyu nine na farko nine na biyu kar na sake ji Bada ni ba wasan kanin miji a gidana Ina wlh ban so,tsakani da Allah ya fada,tace to kayi hakuri bazan a sake ba,farin ciki ya kama Rafeeq yace Kai Malama ce wannan ta gasken ni gani har tsoron fushina akeyi yi. Arham bai dade ba ya tafi gida yace gobe Kuma sai naje gidan Misam na Gani. Washe gari Spark Kano ya wuce Gidan yari
Chapter 63 · 0% Book details