Sashe 22
Tantiriya A Gidan Yari Book 2 Complete Hausa Novel · about 4 min read
da wasu amma basu San su waye su ba,wlh ko ka fada ko Kuma inzo har gida na fada musu ni bazan iya jiran wannan Abu naka ba Jauro wannan ba rayuwa bace,Jauro yace to zan fada ubana,Hashimu yace karka ka fada ma ka gani wlh zanzo na fada ni ya kashe waya,Jauro yace Ina murnar haduwa da Hashimu ashe masifa na hadu da shi,yabi ya ishe ni haba. Na'ima tana can Station an bada bailing ko wacce mata amma Banda ita duk ta rame ta fita hayyacinta,kullum Dan sanda ke kawo mata abinci in yazo sai yace mijinta yazo Yana ta kuka amma Oga ya hanashi shiga,Na'ima tace Allah sarki ni San Jauro Yana so na wlh bazai iya kyaleni a Nan ba,Allah ya isa tsakanina da ku Yan sanda da kuka Hana mijina ganina. Sai yau Allah ya kawo Jauro zai ga Na'ima matarsa,Jikin cail din yazo ya tsaya Inda Na'ima ke tsare hannunta rike da karfen jiki me raga,Jauro Yana zuwa yace Na'ima....Na'imatuta kece kika dawo haka?yanzu Na'ima kece wannan? Yan sanda sun cuceni sai ya fashe da kukan karya,Na'ima ma sai kuka harda yi da karfi na gaske take yi taci wahala, abinci sai anga dama ake bata,Kuma duk da sa hannun Jauro,Jauro kukan karya yake Wiwi harda fyace majina,yace yau zaki fita Na'imatu,na Sha wahala ta rashinki naji jiki,kwanciya ba dadi gida ya zama kango,na sani wlh cewar Na'ima tana share hawaye. Baseeru kuwa har kwana biyu bai je ganin Mummy ba,kullum sai ta kirashi a waya,Chika itama Baseeru ta kira tana Masa warning tace wlh dai karka sake Kaci abinta,karka yi bacci a gidanta ko da rana ne,yace Ina sane ai,yau zanje domin a matse nake zanje na karbi hakkina na fece. Waya ya yiwa Mummy yace zaizo yau da yamma,Mummy ta sa Yan aiki suka gyara gida kamar wani Gomna zaizo,itama taci gayu ta hade cikin material sky,tana zaune da yamma ko Ina Yana uban kamshi. Baseeru ne ya shugo gidan shima anci gayu fes da shi,yana zuwa Mummy harda yin tsalle ta fada Jikin Baseeru,Baseeru ya rungumeta fuskarsa tana kallon bayanta Yana ta zuba gwalo ko uban wa yake wa oho,Mummy sai faman goga Masa kirji take,Baseeru yace yawwa nanika min su,manna su,tace Dear abinci fa? Baseeru yace an samu matsala wlh daga gidan abokina nake matarsa ta nace sai naci abinci na cika cikina ko bangaren ruwa a cike yake taf ba waje,Mummy taji wani ba dadi tace ba komai next time,a ranta tace ai sa guba kauyenci ne yanzu ai na canja salo zaka ci ubanka sai duniya ta San a gidana kake tukun zan gama da Kai,baza ma ka mutu a gidana ba,bare a tuhumeni nasan ta Inda zan kaika lahira. Shi kuwa Baseeru Mummy ya fara sarrafawa gata itama an kwana biyu kadan ake jira ta zurma ya kwashi gara yau ma sosai tun yamma sai magriba ya hakura,tace dole sai ya kwana,Baseeru yace to bari naje Sallah na dawo Yana fita ya fece gidan Daddy Inda yake gadi ya bar Mummy bau tana jiransa. Tunda taga bai dawo ba ranta yayi mugun baci tace wato ya maidani sex machine yazo ya kwasa ya tafi. Wayarta ta dauka ta kirashi,bugu daya ya daga yace Me gidana nane ya kira ni ki rufe gidanki bazan dawo ba,Mummy takaici yasa cikin bala'i tace zaka ci uban babanka Baseeru,wlh dani kake zance,Baseeru yace zaki ci uban Babarki surayya kike ko Yusra wlh zan tsine miki ki San tsinuwar miji Kuma,Yar iska marar mutunci,Mummy tace kaiii wato idan na zageka sai ka rama kana me gadi? Tsaki ya ja yace baki da hankali zanzo gidan sai na ci mutuncinki ya kashe wayarsa,Mummy ta Kalli wayar tana girgiza Kai tace eyyaaaaaa Basiru baza kayi karko ba,baza ka Dade a duniya ba,baza kayi tsawon rai ba,mutum ya lallabani da Yaya ya kare ma. Spark kuwa sabo da haushin Mummy da yaji ta hanashi bincike gashi me gadi ne ya aureta wannan yasa yace nima wallahi ta Abba suruki na bazan boye gaskiya ba, Hakan yasa duk Wanda ya tambaye shi a dangin su ya Mummy Dinka? yace tana gidanta lafiya Lau ai sun rabu da Abban nawa na biyu, yanzu gidanta ya dawo da zama,me gadi ne ashe,da ance a garin ya? Yace kuje wajenta kwaji zancen ba a gulma dani. Yau ma yaje gaida Mima tace Ina Mummyn taka kuwa? Yace hmmm ai ni yanzu na koma Kuma abin tausayi,ya kamata ki tausaya min ni da Naila mun koma yaran talaka, to uban namu na biyu me gadi ne,yanzu ma uwar tamu tana gidanta ya koma zuwa gidanta,Ashe gadi yake yi ba gidansa bane,Auren dauki sanda muka koma mu ai,Mima tace ban gane ba? Yace kije kyaji tushen zancen. Ayi min afwa tunda kuka ga shuru akwai uzuri ne. Masu Sharhi Ina godiya wlh Allah ya bar kauna Mrs chief My love har naga kira Kar ku ce AsmaBaffa wai ko nima na zama Abba Dolo ne yau. AsmaBaffa [1/12, 9:25 PM] AsmaBaffa: Arewabooks AsmaBaffa1 https://www.arewabooks.com/locked?id=65759f207c65b397e88b84b3 TANTIRIYA A GIDAN YARI BOOK 2 ~YARAN JAURO~ 26-30 Official AsmaBaffa SADAUKARWA NE GA AIDA MAMAN TASNIM PAGE NAKI NE MOM SANI