← Book details Noor Al Hayat Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 95 OF 168

Sashe 95

Noor Al Hayat Complete Hausa Novel · about 4 min read

Silence din kusan 3 minutes ne ya biyo baya a parlorn, a hankali Khaleel ya dago kansa yana kallon khadijah da ta hade kanta da gwiwa, har ransa yake jin shesshekar kukanta, gashi ya kasa cewa komai, he is just lost of words, jinginar da kan sa yyi da kujera na kusan minti biyu kafin ya tashi a hankali ya isa gabanta ya duka ya dago kanta yana kallon idanuwanta da suka yi jajir, ta yi saurin sauke idonta daga kallon nasa kwayar idon da su ma suka sauya kamanninsu xuwa ja wasu sabbin hawayen na sakko mata, har lkcn Khaleel ya kasa cewa komai sai kallonta yake, bayan wasu dakiku abinda ya fito bakinsa cikin xaxxakan muryarsa shine "Forget about sudais, he did what he did for the sake of Allah, eraze him of ur mind"

Da sauri khadijah ta dago tana kallonsa, ya mike ya koma kujerar da yake xaune yace "Yeah, ki mance da kin ma taba sanin sa a rayuwar ki, I mean that sudais..." Khadijah dake ta kallonsa ko kiftawa babu tayi karfin halin cewa "Ko saboda me?" A takaice yace "Ohk, it seems biyansa abinda ya maki kike son yi kenan?? If that's ur wish kema xaki iya taimakon marayu ai, I see no reason for good six years xa ki dinga tunani daya ba, beside he needs nothing from you, domin Allah yayi kuma Allah ne xai biyasa" Khadijah ta hade rai ta mike tana masa wani kallo tace "I regret telling you who i am, of all my story... part din sudais kadai ka ji da kyau halan? Shi kadai ka iya recalling? I just wasted the time I was suppose to use for sleeping" Daga haka ta nufi daki ta bar masa parlorn tana share hawayen idonta, Khaleel ya bi ta da ido ko kiftawa babu, jinginar da kansa yyi da kujera ya lumshe ido a hankali, wani mugun tausayinta ne ke shigarta, Sudais? Abinda ya fadi kenan a xuciyarsa ya bude ido da sauri, can ya tabe baki ya mike, ya fi minti biyu a tsaye yana kallon agogon dake nuna karfe uku saura kafin ya nufi bedroom dinta, xaune ya ganta kasa ta hade kai da gwiwa, Aliyu ne kawai ya fado xuciyarsa... ya hade hakoransa yana imagination kala kala a xuciyarsa, can yyi wani murmushi ya karasa cikin dakin yana kallonta ya durkusa gabanta, da farko rasa abinda xai ce mata yyi, can a hankali yace "Am sorry Khadijah, you misinterpret what I meant, ur story.... It is just heartbreaking, it's sad... you've past through a lot in life at a very tender age, but am happy you proved to be a strong lady, strong lady indeed...." Shiru yyi yana kallonta ko kiftawa babu har lkcn ta ki dago kanta, a hankali ya kai hannunsa ya dago ta suna hada ido ta rufe idon, murmushin sa mai kyau yyi yana kallonta, murya can kasa yace "Those cute boys...." Sai kuma yyi shiru, bayan wani lkci yace "You are going no where from UK, Aliyu ne xai bar maki UK ba ke xaki bar masa ba am giving you my words, kina nan har ki gama karatun ki" ta bude idonta a hankali tace "Ae ya riga yasan makarantar, he will surely keep on looking for me" hawaye ne ya cika idonta cikin sanyin murya tace "Ni ban san me xan masa ba yake nema na" murmushi Khaleel yyi yace "Xai daina neman ki soon" Tana son kallonsa amma idanuwansa are not encouraging, ya lura da haka sai ta basa dariya ya mike yace "Alright then, life moves on, ki kwantar da hankalin ki babu wanda ya isa ya hana ki walwala a kasar nan am assuring you, ki tashi kiyi wanka sai kiyi sllh if you wish and then go to bed, the night is far gone" Khadijah dake wasa da fingers dinta tace "But ina son xan je in ga su Umma..." Yace "When?" A hankali tace "Ko gobe" shiru ya d'an yi kafin yace "Alryt then Allah ya kai mu" Ya fi minti uku a tsaye har sai da ta daga kai ta kallesa ta ga kallonta yake tayi saurin dauke kanta, yayi murmushi murya can kasa yace "Good nyt" kai ta gyada masa daga haka ya juya ya fita duk jikinsa a sanyaye, she is really a strong lady, yana fita ya kulle mata kofar, haka kawai khadijah taji ta samu relieve sosai don kusan ji tayi babu abinda ke damunta a ranta kuma, tashi tayi a hankali tayi yanda Khaleel ya ce mata, sai kusan karfe uku da rabi bacci me nauyi ya dauketa.
Chapter 95 · 0% Book details