← Book details Noor Al Hayat Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 46 OF 168

Sashe 46

Noor Al Hayat Complete Hausa Novel · about 5 min read

ba ai sai kallon mutane kamar bakauyiya" turo baki tayi ta dauke kai ta bar wajen, Anty Khadijah da taji komai ta mike kamar jira take tace "Ae da ka fasa idon, tunda kai ka hallitar mata su, kuma bakauyiyar ce uban waye ba daga can ya fito ba? Idan ba munafurci da borin kunya ba ka nuna ka san ta ne balle ta gaisheka, ina ce kai ne ya kamata kace A'a iklima ce... ashe kun xo, yaushe ku ka xo ya hanya, amma kayi gum da baki tunda ba tarkacen da uwarka ta saba kwasowa bane, to wllh iklima ita ce dolen ka ba su ba, kuma baxa ta yi gaisuwar ba, ni din ma ba a walakance ka gaisheni ba kake jiran 'ya ta ta gaisheka kawai don kun ga mutum na xaune gidan ubanku, bari ka ji.... yau sai uwarka ta rabu da ku amma ni muna makale ko min wuya don nice dolenta ba ku da ta samu a gidan nan ba, uwan mu daya ubanmu daya da ita, tun kan ku xo duniya muke tare, munafuki kawai" daga haka ta ja hannun iklima dake tsaye kusa da ita ta wuce sama tana cewa "I can't wait ranan da tarkacen da ku ke debowa da har suke neman haddasa mana matsala xa su kunyata ku a gidan nan, wllh sai na xuba ruwa a kasa na sha don farin ciki, ke kuma iklima ko da wasa kar ki gaishesa ya fasa idon mu gani tun ance masa kwai ne" Aliyu ya tabe baki ya mayar da dubansa kan laptop din gabansa, baby ta karaso dining tana kallon Aliyu tace "Anty Khadijah can just shout for African ehennn, I don't even like that her daughter that is eying me since, it seems she even used my sponge to bath this morning coz it wasn't d way I left it" shi dai bai ce komai ba, ta bude masa textbook din math dinta tace "Yaya koya min assignment don Allah" ya kalli book din sannan yace "Ki je ku yi da Classmate din ki mana" Baby tace "Iman?" Yace "Yes" ta ce "She told me she is not feeling fine, kayi mana sai in kai mata ta yi copying nawa, she is even lying down now" yace "Me ya sameta?" Baby ta bude hannu tace "I don't knw, or may be it's because Anty Khadijah ta doke ta daxu, kasan duka tayi mata daxu fa" yace "Duka? Why? A ina ta doke ta?" Baby tace "Dakin can ta shiga ta mata dukan shine ni kuma naje na gaya ma Mumy a sama ta sakko downstairs tayi ma Anty Khadijah fada sosai, har sai da Anty Khadijah tayi kuka, I even saw her packing her load but I don't knw what made her Change her mind kuma" yace "Kira min ita" ta ce "Iman?" Yace "Ehh" tace "Noo daxu da naje tana bacci na tasheta, shine kyauta tace kar in kara tashinta tace mata kanta yana ciwo sosai, kuma kamar Anty Khadijah ce tayi causing din ciwon kan coz she hit her head on the wall many times" Tashi Aliyu yyi yace "Mu je wajen ta" baby ta mike ta bi sa suka tafi dakin kyauta, kwance take kan gado kyauta ta rufe ta da bargo bayan uban rub da ta shafa mata a jiki, ya isa kusa da gadon Baby na biye da shi, sosai lebbenta yyi ja kana ganinta kasan ta ci kuka ba na wasa ba, ya kai hannu forehead dinta ya ji har ya dau xafi, baby ma ta taba tace "Kaji jikinta da xafi koh, Anty Khadijah ce tayi causing din komai" juyawa yyi ya fita ya wuce dakin Mumy, yana tsaye har mumy tayi hanging kiran da take tana kallonsa tace "Ya aka yi Abuturrab?" Yace "For God sake abinda Anty Khadijah ke yi a gidan nan is getting out of hands, why will she just best someone's child the way she did" Mumy tace "Na fa yi mata magana nasan baby ce da gulma xata gaya maka, wllh ni kaina nayi mamakin abinda nayi mata daxu cos gaskiya I am nt happy" yace "Toh yanxu da ta sa ma yarinyar xaxxabi fa?" Mumy tace "Toh sae in ce Allah ya saka mata, don yarinyar dai bata mata komai ba" juyawa yyi ya fice daga dakin ya harari saleem da fitowarsa daga dakin Anty Khadijahr kenan ya sauka downstairs ya koma dinning ya xauna, mumy ce ta sakko ta shiga dakin kyauta, jin xafin jikin khadijah ta tada ta ta wuce sama da ita xuwa dakin baby, baby da ta biyo su ta xauna kusa da khadijah da mumy ta kwantar saman gadonta tace "Mumy let her be staying in my room sae mu dinga assignment tare ba sai ina xuwa dakin kyauta ba" Mumy tace "Tafi ki kira min yayanku" juyawa baby tayi ta fita ba a dau lkci ba ta dawo tace yana xuwa, mumy na ta jiransa har ya shigo da sallama tana kallonsa tace "Ko xaka samo mata magani don Allah Aliyu" ya karaso gadon yana kallon khadijah, mumy ta mike tace "Ae ita ma ga nata can ana gallaza masu kuma bata yarda don tana ma 'ya yan wasu bne" daga haka ta fita Aliyu ya bi bayanta, baby kuma ta xauna tana ta kallon khadijah.
Chapter 46 · 0% Book details