← Book details Noor Al Hayat Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 57 OF 168

Sashe 57

Noor Al Hayat Complete Hausa Novel · about 4 min read

ta tilastata da kyar, da tayi ma Aliyu maganan alluranta da ya rage yace driver ya kai ta sai karfe goma shi xai fita aiki, sanusin ne ya kai ta ya maido da ita, kafin yamma taji saukin jikinta sosai sai dai ta rasa irin ciwon da take jin kirjinta ke mata, kuma hakan na faruwa ne in dai ta tuna incident din ranan sai taji mugun faduwar gaba, har lkcn Aliyu bai barin su hada ido a gidan kuma bai ce mata komai, idan tana wuri ma bai yrda ya tsaya a gun, Anty khadijah dake lura da komai har wani farin ciki da nishadi na musamman take ji a gidan, har Mumy ta dinga mamakin yar uwar tata, duk fadace fadace da xage xagen ta rage yanxu hatta Khadijah ta daina hantara nan ko shirin sake komawa inda taje kwanaki kamar yanda aka ce mata ta dawo idan ta tabbatar komai ya wakana a lkcn ma xa a fara aikin, tunanin karyan da xata yi ma Mumy kawai take ta tafi inda xata. Aliyu na bedroom dinsa da daddare baby ta shigo, ta xauna kusa da shi tace "Yayanmu I want to ask you something pleaseee" yana kallonta yace "What?" Ta langwabar da kai a hankali tace "Iman tayi maka wani laifi ne, naga you no longer talk to her, ko ta gaisheka sometimes you do pretend you didn't hear, why please, ka gaya min me tayi maka, gashi ita ma she is always sad yanxu, I've caught her severally tana kuka cikin dare..." Katse ta yayi yace "Na fara wasa da ke da yawa koh?" Da sauri ta girgixa masa kai, ya hade rai yace "Toh tashi ki tafi" mikewa tayi da sauri ta fita ya ci gaba da danne dannen laptop da yake yi. Washegari da sassafe Anty khadijah ta shirya har da kwallarta take ce ma Mumy xata Abuja an kirata wai Yusuf d'anta ba lafiya yana asibiti, mumy jikinta yyi sanyi har da bata dubu goma ta hau mota, ta karba ta yi mata godiya ta bar gidan. Karfe goma saura Mumy ta tafi aiki gidan ya rage khadijah da baby sai Iklima don su siyama sun tafi makaranta, Aliyu ma na sama a dakinsa, tun bayan abinda ya faru tsakanin khadijah da Aliyu ta rage xaman cikin gidan sae Mumy na nan, always a baya xaka ganta xaune ita kadai, yau ma xaune take tayi nisa a tunanin da take kamar ance ta juya taga Aliyu tsaye d'an nesa da ita, mikewa tayi a tsorace tana komawa baya, ya dauke idonsa daga kallonta yace "Iman" hawaye ya cika idonta ta kasa amsawa, karasowa yyi kusa da ita ya tsaya tana komawa baya a hankali, yace "Za ki gane gidan step mum din ki?" Khadijah sai kallonsa take xuciyarta na bugawa, ya hade rai yace "Am asking" a hankali tace "Kila in gane" yace "Ohk... Am coming back now" daga haka ya juya ya koma ciki, ba a dau lkci ba ya dawo, envelope ne rike hannunsa ya mika mata taki amsa gabanta sai faduwa yake, yace "Collect it" hannunta na rawa ta karba, yana gyada kai yace "Go Iman, go back to ur step mum, I can't continue my life the way I want living with you in the same roof, you are now a barrier to my happiness pls ki tafi Iman go anywhere, leave our home, bana son Ina ganinki ina jin haushin kai na cos nobody is above mistake, just go plss" A hankali ta juya masa baya hawaye na sakko mata tace "Ohk xan tafi... thank you very much for all what you've done to me throughout my stay in your home, Allah saka maka da alkhairi duk hidiman da ka min, but ina neman alfarmar ko xan iya yi ma Mumy sallama kafin in tafi, don ban mata hallaci ba idan na tafi bata sani ba" a takaice yace "Noo, just go Iman" ta fashe da kuka sosai tace "Ohk nagode" juyawa yyi ya nufi cikin gida... Sai kuma ya juya da sauri yana kallonta yace "And one more thing... Forgive me plss" ta juyo hawaye na sakkowa idonta tace "I have done that already" yace "Thank you" daga haka ya juya ya shiga ciki ya rufe kofa. Share hawayen idonta da ya ki tsayawa ta dinga yi, dama Hijab ne jikinta kawai ta nufi gate ta fita gidan, da kafa ta karasa bakin titi ta samu napep tana kallonsa a hankali tace "Tasha xaka kai ni" yace "Toh" daga haka ta shiga napep din, har suka isa tasha bata sani ba tayi nisa a tunanin da take, mai napep din ya dawo da ita duniyar tunanin da taje, sai a sannan ta tuna kudin da xata basa, da sauri ta leka cikin envelope din da Aliyu ya bata taga kudi ne me yawa a ciki ta xaro dubu daya hawaye na sakko mata ta shiga tashar ta nufi inda taji ana kiran kano, dama mutum daya ake jira tana shiga motar ta bada kudinta bbu bata lkci suka dau hanyar kano.
Chapter 57 · 0% Book details