Sashe 114
Noor Al Hayat Complete Hausa Novel · about 2 min read
gudu ya shiga titi babban mota ya buge sa" ta fixgo yaron tana huci tace "Shi ya janyo mota ya buge Sudais?" Kai ya gyada mata ta jefa masa wani kallo tace "And you are telling me he is kind yana neman kashe maka brother, daga yau ka sake yarda ko kallon ka yayi sai ya xuke maka jinin jikin ka gaba daya, baka san shi vampire bane" buda baki yyi yana kallonta da surprise, can yace "Me yasa bai shanye mana ba a gidansu?? Anty he is kind fa, ni dai I like him, he was with us....." Tsawa tayi masa ta turasa har sai da ya kusa faduwa hawaye cike idonta tace "Xan fasa maka kai... Nace stay away from him, you have no business with that wicked man" Shiru yyi a tsorace yana kallonta, a hankali yace "But he even told us he is our father not barrister as you told us...." Mikewa tayi hankali tashe xuciyarta na mugun bugawa tace "He is a liar... Karya yake maka barrister ne babanka, ba abinda ya hada mu da shi" cikin rawar murya tace "Tafi ka kamo hannun sudais ku xo nan yanxun nan" da sauri ya fita, yana isa kusa da Aliyu yace "Uncle, Anty tace I shud call my brother now" shiru yyi yana kallon yaran, haka ma Mumy da Umma, Aliyu yayi kasa da kai a hankali yace "Umma ki d'an mata magana ta bari in je da shi, he is sick dole xa mu koma asibiti" a fusace Khadijah dake jin sa ta fito tace "Ina ruwanka da rashin lafiyarsa? Ka bani yarona ai nasan hanyar asibiti, give me my son" tsawa Umma tayi mata ta mike tace "Tafi ki bar parlorn nan kar in bata maki rai, shashasha" ta fashe da kuka ta juya da sauri ta bar wajen, Umma dake kallonsa a sanyaye tace "Ka je da shi, Amma ko xuwa gobe sai ka kawo shi" a sanyaye yace "Na gode Umma" su mumy basu bar gidan ba sai kusan karfe taran dare bayan mumy ta mata bayanin duk abinda ya faru, Umma ta raka su har bakin mota jikinta a sanyaye.