← Book details Noor Al Hayat Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 138 OF 168

Sashe 138

Noor Al Hayat Complete Hausa Novel · about 4 min read

baya ci, ya girgixa kai ya dauke kai daga abincin, ajiye serving spoon din hannunta tayi ganin alamar ana kiran wayarsa da ke jone a caji, ta mike ta nufi inda wayar yake, tana isa ta dauka tana kallon screen din "Ameerah" sunan da ta gani kenan jikin screen din, ta dinga kallo xuciyarta na bugawa, picking call din tayi kafin ya katse ta kai kunne tayi shiru Khadijah na jin an daga ba a ce komai ba tayi shiru ita ma don it's unusual of him kuma tana jin muryar little Amira a wajen, Kamar ance Sudais ya daga kai ya ga jiddah tsaye har lkcn wayar na kare kunnenta fuskar nan nata a murtuke, ajiye Amirah yyi kan kujera ya mike da sauri yace "What's that u are doing Jiddah?" Ba shiri Khadijah ta katse wayar ta ajiye ta tabe baki ta yi kwanciyar ta. Jiddah na masa wani kallo tace "Wato dai da gaske aure kake shirin yi saboda baka da tsoron Allah ko Aliyu?" Ya warce wayarsa a hannunta yana mata wani kallo yace "Don't you ever dare pick my call again malama" daga haka ya bar parlorn ya wuce sama, Xaunawa gefen kujera Jiddah tayi lkci daya hawayen takaici ya shiga sakko mata, ai da ta sani kawai guduwa daki tayi da wayar tayi pick din call din ta sussurfa ma shegiyar dake kiransa xagi, to Wai wacece wannan Amirar? Sai yanxu taji tana mugun son sanin wacece ita, ta kalli Yar ta dake xaune tana kallon tv, lkci daya lkcn da ta haifeta ya dawo mata, ranan sunanta bayan ya sa sunan mahaifiyarsa babu yanda bata yi da shi kan cewar da Khaleesat xata kirata ba yace inaaa bai san xance ba sai dai Amirah, da ta tambayesa me yasa sai ce mata yyi sunan wata frnd dinsa mai muhimmanci a rayuwarsa ce kuma yana ji da ita sosai shi yasa xai kira 'yar sa da haka.... Jiddah ta mike da sauri xuciyarta na bugawa ko dai ita ce wannan mai kiran nasa yanxu, ita fa dama tun lkcn taji ta tsane koma wacece Amirar nan, shi yasa har yanxu da kyar take kiran Yar ta da Amirah, a bayan idonsa dama kiri kiri Khadijah take ce mata, wayarta ta dauka ta shiga dakin da ke parlorn ta kulle kofa ta shiga neman number Dr Yusuf tasan duk yanda aka yi baxai rasa sanin wacece Amira ba, bugu biyu ya daga bayan sun gaisa yana tsokanarta wai ta sa abokinsa ya mance shi gaba daya, ta xauna gefen gado tace "Dr dama tambaya ce na kira in maka don Allah..." Dr Yusuf yace "Toh Ina ji, Allah sa na sani dai" tace "Uhm nasan ka ma sani, wllh in gaya maka abokin ka ne duk ya ishe ni da wata Amira nayi nayi ya gaya min wacece ita ya ki, har cewa yayi idan na cinka wacece ita to xai bani kyautar mota, toh ni dai duk iya tunani na rasa gane wacece amma na fi tunanin frnd dinsa ce kilan da yake ji da, shine yanxu na kira ka bani satar amsa, dama wllh motata ta isheni sabuwa dal nake so, Kuma kasan barrister baya saba alkawari plss Dr ka taimaka" dariya sosai Yusuf yayi yace "Wai Amira?" Gabanta na mugun faduwa tace "Ita fa Dr..." Yace "Yasan baxa ki taba sanin wacece ita ba, Kuma xancen gaskiya babu wani mota da yake da niyyar baki don yasan ko xa ki shekara kina naxari baxa ki san wacece ita ba, it's not even possible, Ni kuma yanxu idan na gaya maki kika fada masa he will suspect ni na gaya maki don duk abokansa babu wanda yasan ta sai ni...." Jiddah tace "Haba Doctor, shi kansa yasan ai alkawari yayi baxai saba ba, Ni dai fa damuwata mota, don Allah ka gaya min ai bai san ina da number ka ba he won't suspect anything" Yusuf yyi murmushi yace "Toh xan gaya maki indai sabuwar mota kike ma" ta baxa kunne tace "Yauwa nagode sosai Dr" nan Dr Yusuf ya fara bata labarin Khadijah tiryan tiryan babu abinda ya boye a duk labarin har ranan da Mami ta rabasu na karshe. Gaba daya xufa ya dinga karyo ma Jiddah taji cikinta ya hautsine, Jin Yusuf yace "Hello" cike da karfin hali tayi dariya tace "Ikon Allah, Allah sarki, to nagode Dr Allah saka da alkhairi Allah ya barka da Amina, sabuwar mota kam dole a ban" daga haka tayi masa sallama ta katse wayar dai dai lkcn da aka bude kofar dakin kafin ya kai ga shigowa tayi saurin boye wayar hannunta, ya shigo yana kallonta yace "Files da na bari kan dinning kafin nayi tafiya, Ina kika ajiye min?"
Chapter 138 · 0% Book details