← Book details Noor Al Hayat Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 113 OF 168

Sashe 113

Noor Al Hayat Complete Hausa Novel · about 8 min read

xuwan mu yanxu, she humiliated us and sent us away then" Kasa cewa komai mumy tayi lkci daya hawaye ya kara cika idonta da kyar tace "Kana nufin khadijah ce ta Kore ku, kuma kun gaya mata abinda ke tafe da ku?" Sudais na gyada kai yace "Kwarai, I was even thinking she is his mum then, the way she reacted...." Mumy tace "Amma kun samu Aliyun?" Girgixa mata kai yyi yace "Ce mana tayi baya kasar gaba daya" Mumy ta fashe da kuka tace "Amma Allah ya isa tsakanina da khadijah, she just ruin my family, yar uwata ce amma ko bare baxai min haka ba, yanxu tana sane da abun nan amma bata gaya min ba, she never told me anything about it da babu abinda xai hana ni nemo Iman duk inda take, greatest mistake din Aliyu shine ce mata da yayi ta tafi, kuma wllh ni shaida ce tun daga ranan Aliyu bai sake samun kwanciyar hankali ba, kuma bai taba gaya min abinda ya faru ba sai dai yace in taya sa da addu'a, gashi nan dai har yanxu ya ki yin aure" Ko kadan khadijah bata damu da abinda mumy take fada ba ku ma bai shigeta ba, Briefly Sudais ya ba ma Mumy labarin yanda rayuwa ya kasance ma khadijah bayan Aliyu yace ta tafi... Ban da kuka babu abinda Mumy take duk jikinta yyi mugun sanyi tausayin Khadijah ya cika ta, ita dai tasan da tasan abinda ya faru kenan da ta sa Aliyu ya nemo ta Duk inda take amma yyi wautan rashin gaya mata, Mumy ta mike ta isa gun khadijah ta duka gabanta tana kuka tace "Khadijah ina neman alfarmar ki yafe ma Aliyu, ko don albarkaci na forgive him plss, kadararrku ce a haka, don haka ki ta godiya ma Allah, amma kiyi hakuri kar ki bar sa a xuciyar ki" Khadijah da xuciyarta ya mata rauni ita ma tana kukan tace "Mumy ni fa na yafe masa amma yayi hakuri ya bani yaran don Allah" mikewa Mumy tayi tace "Xai baki Khadijah, ina gidan ku yake yanxu?" Khadijah ta fada mata address din, Mumy tace "Toh kiyi hakuri ku je na maki alkawarin xa mu biyo ku da yaran yanxu" shiru khadijah tayi tana kallonta xuciyarta na bugawa sai take ga kamar kawai labari mumy take mata don ta tafi, baxa su bata yaran ba, Sudais ya mike yace "Toh shkkn, Ma... Muna xuba ido sai kun xo" Mumy ta kalli khaleel a sanyaye tace "Ku yi hakuri balarabe, Allah ya ba ku lada, amma don Allah ku bar jin haushin Aliyu ba yin kansa bane, nasan xa ku yi ta mamakin jin ina cewa ba yin kansa bane kamar na shiga xuciyarsa, but plss just do consider him" Murmushi khaleel yyi ya mike yace "Bakomai Ummu, Allah ya kara girma" tace "Amin nagode" daga haka ya nufi kofa, sudais ya kara mata sallama ya bi bayan khaleel, Khadijah na biye da su a baya tana goge idonta, ta kasa kallon baby dake bakin kofa har lkcn, A hankali baby tace "Iman plss forgive me brother, ki yafe masa don Allah" hawaye na sakkowa idonta take maganar, Khadijah tayi murmushin karfin hali tace "Na yafe masa" daga haka ta fita parlorn. Sama Mumy ta wuce xuwa dakin Anty Khadijah ta ganta xaune tana bude jikin iklima ganin wasu kuraje da ke feso mata ta ko ina, Mumy tace "Khadijah, a duk xaman mu dake in har na taba cutar ki Allah ya saka maki, in kuma ke kika cuce ni Allah ya saka mani, ki tattara kayan ki da na yar ki ki bar min gidana yanxu, Allah ya bani ladan xumuncin da nayi a baya, kuma in sha Allah nasan Allah baxai kama ni da laifin xumunci ba, ki je na bar ki da Allah" mikewa Anty khadijah tayi tace "Ni yau kike kora gidan ki yau Anty fati saboda wasu shegu sun xo sun shirga maki karya?" A fusace Mumy tace "Ki fita ki ban waje, yanda kika so ganina da jikoki wanda aka samu ba ta hanyar aure ba ke ma Allah ya ba ki" Anty khadijah ta tashi tana wani murmushi tace "Sai kinyi da kin sanin daga min yatsa da kika yi fatima" daga haka ta bude siff ta dinga fiddo kayanta da na Iklima tana huci, Mumy tace "Da na sani sai dai ki gansa a kwaryar ki" daga haka ta fice daga dakin ta shiga na Aliyu, Yana xaune gefen gado ya rike kansa, duk yan biyun sun yi bacci kan gado, Mumy na kallonsa tace "Kai da babban laifi kai da fadin bakakken maganganu ko Aliyu?" Kamar xai mata kuka yace "Mumy me yasa duk hallacin da na ma khadijah a baya baxata duba na, did I deserve this, wllh da hankalinta baxan cuce ta haka ba, sannan ta dinga wani hadani da wasu karti, ni ita na sani ba su ba su ba su daina involving kansu a abinda bai shafe su...." Katse sa mumy tayi tace "Don't tell me nonsense, dole duk mai conscience idan ya ji labarinta ya so ya kwatar mata hakinta, kasan irin cutar da ka mata kuwa ka raba ta da kowa nata?" Aliyu ya rike kansa bai ce komai ba, Mumy tace "Sai ka tashi mu tafi can gidan nasu yanxu" Aliyu ya dago ya kalleta da kyar don wani Sara masa kansa ke masa yace "Mumy wllh ni baxan iya rabuwa da Iman ba, baxan iya rayuwa ba ita ba, my life has being miserable tun da na sa ta bar gidan nan, Don Allah ki rokar min ita ta amince mu yi aure, I don't think xan iya auren wata ya mace a duniya idan ba ita ba, plsss even for the sake of this innocent children ta amince mu yi aure" Mumy tace "yanxu kuma??" Tashi yyi Yace "Wllh Mumy idan tace baxata aure ni ba, I promise to go away with this kids baxa ta sake ganinsu ba har karshen rayuwarta, ai da can ba da su take rayuwa ba" Mumy na masa wani kallo tace "Na ga alamar ka fara xarewa, da yaran xaka mata baraxanar ta aure ka kenan, a hakan xata amince ta aure kake tunani, kasan ko kotu aka je yaran nan ba naka bane Aliyu, ba ta hanyar aure ku ka same su ba don haka ka janye wannan baxan maganar da kake yi, kuma kar ka bata min rai" Wani murmushi yyi bai dai ce komai ba, Jikin mumy yyi sanyi ta bi sa da kallo, tsoronta kar ya tafi da su kamar yanda yace, da kyar tace "Ka tashi mu je gidan na su, nasan even for my sake ma xata amince maka" daga haka ta fita dakin. Sai kusan magrib suka isa address da khadijah ta ba mumy, Aliyu ke driving din, Sai baby a gaba, mumy kuma na xaune back seat da yan biyun, tana rungume da little Sudais da jikinsa yyi xafi sosai duk da allurorin da Aliyu yyi masa, kai kana ganin yaran kasan hankalinsu ya kwanta da mumy, Shureim na kallonta yace "Are we going to visit you again mama?" Tana murmushi ta shafa kansa tace "Sure sweetheart" parking Aliyu yyi kusa da gidan ya juya yana kallon Mumy, Mumy tace "Ina jin nan ne" Shureim yace "Ehh mama nan ne gidanmu" Mumy tace "baby sauka ki kwankwasa gate din" Baby ta sauka tayi yanda Mumy tace, Mumy ta sauko tare da boys din, Aliyu ya fito shi ma ya dau sudais, bayan wani lkci Nanny ta bude gate din, da gudu Shureim ya tafi ya rungumeta, Nanny ta ji dadin ganin su sosai ta dinga yi ma su Mumy sannu da xuwa, Kallo daya tayi ma Aliyu ta gane shi ne uban yan biyun, ta yi masu iso har parlor, Sannan ta shiga daki don Umma na ciki tana sallah, Khadijah ma tasan sallan take yi, Umma ta sa Hijab ta fito bayan Nanny ta sanar mata bakin da suka yi, Har lkcn Sudais na jikin Aliyu, Shureim dake jikin Mumy ya tafi da gudu ya rungume Umma yace "I miss you Mumy na" Umma ta xauna tana murmushi ta ja sa jiki sannan suka shiga gaisawa da su Mumy, jikin mumy yyi sanyi sosai don bata taba xaton xata tarbesu da kyau haka ba, shi dai Aliyu ya kasa daga kai ya kalleta, shi ma bai yi xaton haka ba, Khadijah dake xaune kan darduma lkci daya taji ranta yyi mugun bacci jin yanda Umma ta sake masu, jin muryar yaranta yasa ta lumshe idonta, amma ta ki fitowa parlor ta same su don bata ma son ganin Aliyu, Mumy na kallon Umma tace "Ina Khadijar Hajiya?" Umma ta kalli Nanny dake tsaye tace "kira Khadijah" sosai Khadijah ta dake xuciyarta ta mike ta bi bayan Nanny kan ta a kasa, har ta shigo parlorn bata yarda ta dago kanta ba ta gaida Mumy, Aliyu sai kallonta yake ko kiftawa babu, Shureim ya nufeta ya xauna jikinta yace "Anty mun dawo, I like the house so much..." Khadijah ta ki kallon yaron amma har ranta bata ji dadin abinda yace ba, ita fa in dan ta ita ne yaranta basu da uba, ita dai tasan Allah ne ya bata su, kuma tana gode masa, fuskarta daure ta dago tana satan kallon Aliyu dake ta kallonta suka hada ido ta masa wani harara ta dauke kai, lkci daya ta mike ta ja hannun Shureim suka bar parlorn, tana xaunawa kan gado ta jawo yaron gabanta tana kallonsa da kyau tace "Did that stranger tell you anything?" Shiru yyi da farko kafin yace "But he is not a stranger Anty, this is the 4th time we are meeting with him" ta xaro ido xuciyarta na bugawa tace "Where and where" yace "Anty ranan nan da muka kusa yin accident, that i told you he made sure we where fine...." Gabanta yayi mugun faduwa tace "And where?" Yace "We met again at the airport da xa mu je holiday a UK, shi ma xai je can..." Ta runtse ido xuciyarta na tafarfasa tace "And where????" Yace "Yesterday at the market, because sudais don't like him shine ya
Chapter 113 · 0% Book details