← Book details Noor Al Hayat Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 49 OF 168

Sashe 49

Noor Al Hayat Complete Hausa Novel · about 8 min read

kirata, ta taso da sauri tace "Ni?" Yace "Eh xo" karasawa tayi kusa da shi ya jawo ta waje ya kulle kofar parlorn, ya rike duk hannunta biyu yace "Ni sa'an ki ne da sai dai ki kalle ni a gidan nan baxa ki gaishe ni ba" hade rai tayi xata kwace hannunta ya kai mata Rankwashi ya murda kunnenta da karfi, ta bare baki ta fara kuka, hakan ya basa daman tsula mata bulalan hannunsa, ya xaneta ta ko ina a jikinta to his satisfaction, sai ihu take tana kiran Anty khadijah, Saleem ne ya bude kofa da sauri uwarta kuma ta fito kitchen a rude tana tambayar me ya faru, ina iklimar, ko kallon Saleem Aliyu bai yi ba ya kara rankwashinta ya turata ya nufi gate da sauri ya fice daga gidan. Hauka ne kadai Anty khadijah bata yi ba barin da ta ga yanda bulala ya kwanta ta ko ina a jikin yar ta, Da ta tambayeta me tayi masa cikin kuka tace "Wai bana gaishesa" ran Anty khadijah yyi mugun baci, cikin fada tace "Shi gaisheni yake yi a gidan? Ae wllh sai dai idan baxai sake dawowa gidan nan ba, ina nan ina jiransa, sai ya gaya min dalilin haka, jaka ya samu ko tinkiya? Idan yana jin haushina sai aka ce ya sauke kan 'ya ta, yayi facing dina mana, toh wllh xai dawo ya same ni sai ya gaya min ko a kansa kike xaune gidan yau, toh wai ma shi akwai wanda ya kai sa fitsara, yanxu idan nace Allah ya isa ace ban kyauta ba koh, yaushe rabon da yyi min gaisuwar kirki a gidan nan, toh wllh sai ya san ya doke ki" ita dai mumy na tsaye ta kasa cewa komai, Anty khadijah na huci ta ja iklima dake aikin rusa kuka tayi sama da ita, Baby har da rike cike saboda dariya a dakinsu, bayan ta yi mai isarta tace "Yayanmu and sense, that served her right" Aliyu kam yana fita aiki ya tafi abun sa ba tare da ya waiwaiyi motarsa ba. Haka rayuwa ta ci gaba da kasancewa a gidan har su Baby suka fara shirin yin junior waec, sosai Aliyu ya ji dadin tafiyar kyauta don yanxu kam kowa aiki yake a gidan, duk sanda Anty khadijah xata shiga kitchen in da safe ne to karfe takwas da rabi yaran xa su makaranta, idan da rana ne to sai kusan biyar xa a ci abinci gidan, idan kuma da daddare ne sai goma wasu har sun yi bacci, ga girkin ba kan gado yau ya yi half done gobe ruwa yyi yawa, hakan yasa Mumy ta gwammace ta shiga tayi da kanta tare da su siyama su yi ta turo baki, wanke wanken gidan kuma aka raba ma Baby, Khadijah da iklima, duk sanda iklima ce da wanke wanke idan Anty khadijah ta faki idon mumy sai ta sa khadijah tayi tana hantararta da xagi wai ai aikinta ne dama, idan kuma mumy na parlor toh ita da kanta take fita ta taya 'yar tata wanke wanken tana cika tana batsewa kamar irin ba a son iklimar, shara kuma Aneesah da Siyama ke yi da goge goge, sai kowa ya gyara dakinsa ya wanke bayi, har lkcn khadijah ta kasa mance kyauta, kullum sai tayi tunaninta wani lokacin har da hawayenta baby tayi ta lallashinta, ga Anty Khadijah ta sa ta gaba fiye da da a gidan barin idan mumy ta tafi aiki, duk gidan gun Aliyu da Baby kadai take samun sauki sai Mumy, shi kansa saleem ko inda yake bai son ganinta, shi yasa idan yana gidan tayi ta xaman daki kenan tana karatu, sau tari ummanta kan fado mata, ko a ina xata sake ganinta kuma? duk da alamun girma ya fara bayyana sosai jikin Khadijah bbu mai gane hakan saboda yanda ta tsiri sa Hijab a gidan, kamar yanda Aliyu yace ta dinga yi, Mumy ta sha mata fadan sa Hijab da take a ko da yaushe amma ta kasa bari, hakan yasa mumy ta kyaleta kawai da ta lura baxa ta iya barin bane, a hakan suka fara junior waec, ko da yaushe tare xa ka ga Khadijah da baby suna karatu amma iklima daga kallo sai bacci uwarta bata ce mata komai, duk ta wani xama lukuta sai kumatu ko wa ya ganta yasan ba cin wasa take ba, idan mumy tayi maganar rashin karatunta sai Anty Khadijah tace ai tana yi cikin dare idan kowa yayi bacci, kullum suka dawo makaranta fuskar iklima a murtuke xaka gansa alamar dai bbu abun arxiki a exams din ranan, baby ce mai shiga harkarta dama tayi ta tsokanarta tana dariya, ita kam khadijah ba ruwanta. Ranan da suka yi last paper dinsu, Anty khadijah ce taje dauko su don Sanusi baya nan, su siyama kuma sai hudu dama xa su dawo gida, Khadijah na ganin Anty khadijah ce ta xo daukansu jikinta yyi sanyi sosai, bayan su baby sun shiga xata shiga Anty khadijah ta jefa mata naira Dari tana mata matsiyacin kallo tace "Wannan kuma baki isa ba, idan xa ki nemi abun hawa ki nema don kaza kazan ki" daga haka ta ja motarta, baby ta bata fuska tana kallon small mum din tata, Iklima kuma sai kallon khadijah take ta glass tana murmushi, a sanyaye Khadijah ta durkusa ta dau kudin hawaye cike idonta, a yanxu ne abinda Anty Khadijah ke mata ke damunta sosai ita kanta bata san me yasa ba unlike before, ni kam nace ko don ta fara sanin ciwon kanta ne? Napep ta samu ya kai ta har kofar gida ta basa darin sannan ta shiga cikin gida tana gaida Usman ya amsa da fara'a yana tambayarta ita kadai ta dawo yau ina sauran, murmushi kawai tayi masa tace suna xuwa, tayi mamakin da ta riga su dawowa gida, ta wuce cikin gidan wanda da alamar dai babu kowa ciki, sama ta wuce don cire uniform, tana cire riga aka bude kofar dakin ta juya da sauri, saleem ne tsaye bakin kofar ta sunkuyar da kai tace "Ina yini ya saleem?" Bai amsa ba instead sai ma shigowa da yayi ya rufe kofar, ta koma baya a hankali tana kallonsa, ya rungume hannayensa yana kallonta yace "Na maki wani abu a gidan nan ne da ba kya shiri da ni?" Kasa kallonsa tayi, da kyar ta tattaro abun cewa "A'a baka min komai ba" ya taho kusa da ita yace "Toh me yasa sai Aliyu kike kulawa" ta koma baya kamar xata yi kuka tace "Kai ma ina kula ka ai" kamo hannunta yyi ta fixge da sauri hawaye cike idonta a hankali tace "Bana son haka.. Am I not just like baby to you" Wani kallo ya mata yace "You are not, baby is my blood" ya sake riko hannunta ta kuma fixgewa, dago kanta yyi yana kallon kwayar idonta dake cike da hawaye yace "You are pretending you don't want me to touch ur hands?" Hawayen idonta ya silalo tace "I am not, I just don't want that" Yyi wani murmushi yace "then you have to, just for today" ta sauke idonta muryarta na rawa tace "Am sorry ni ba yar iska bace" daga haka xata wuce ya fixgota da karfi tayi wani kara yace "Ni ne d'an iska?" Ta fashe da kuka sosai tace " Ya saleem don Allah kayi hakuri ka kyaleni, stop this..." Bai kai ga cewa komai ba aka bude kofar dakin, a tare suka juya da sauri, Aliyu ne tsaye bakin kofar, ya dinga kallon saleem ko kiftawa babu, saketa Saleem yyi ya nufi kofar, Aliyu dake kallonsa a hankali yace "Me kake yi a nan?" A takaice yace "Nothing" xai bi gefensa ya fita ya mayar da shi dakin sannan ya sauke masa mari, dafe kuncinsa yyi yana kallon yayan nasa da mamaki yace "Mari na kayi fa?" Aliyu yace "Toh rama" ya fi second ashirin yana kallon yayan nasa sannan ya fice daga dakin, Khadijah ta durkusa kasan dakin ta hade kanta da gwiwa tana kuka, karasawa yyi cikin dakin yana kallonta a hankali yace "Me yasa kika dawo gida ke kadai?" Cikin kuka tace "Anty Khadijah ce tace baxan shiga motar ba, shine ta bani kudin mota" bai sake cewa komai ba, bayan kusan minti daya ya durkusa gabanta, a hankali yace "Forgive him Iman, kiyi hakuri" hawaye na sakkowa idonta tace "I have done that" bai sake cewa komai ba, a hankali ta mike ta dau Hijab dinta ta sa ya bi ta da ido, mikewa yyi yana kallonta yace "Plss kar ki gaya ma Mumy komai Iman, she will be disturbed" ta kallesa a hankali tace "I won't" daga haka ya nufi kofa, dakin saleem ya shiga ya samesa xaune gefen gado, strictly yace "Saleem this shud be ur 1st and last attempt idan ba haka ba, I will make u start imagining if I am ur blood or not" daga haka ya fice masa a dakin. Anty khadijah ce xaune dakinta tana ta kallon Saleem da wani expression tace "Ya mare ka fa kace?" Saleem dai ya hade rai bai ce mata komai ba, a fusace tace "Toh don me baka rama ba?" Ya kalleta yace "In rama Anty?" Tace "Ehh mana, tun da bai rike girmansa ba, fuska ya fi fuska ne? Sannan uban me ma ya dawo da shi, da na bar gidan fa baya nan...." Saleem ya tabe baki bai ce komai ba, kwafa ta yi ta cije yatsa, can tayi wani murmushi tace "Ohk, ai idan ya san wata bai san wata ba, kuma shine da jin kunya, kunya babba kuwa, sai ya gwammace ina ma ba shi bane"
Chapter 49 · 0% Book details