Sashe 120
Noor Al Hayat Complete Hausa Novel · about 6 min read
clinic duk yana kallonsu ya lumshe ido to prevent more tears, he still can't believe that cute boy, his blood is gone forever, kiran Abbansa ne ya shigo wayarsa, ya san mumy ta kira sa ta fada masa kenan, don tun bayan da Mumy ta gaya masa abinda ya shiga tsakaninsa da khadijah da batun yan biyun ya dauke masa wuta duk da a ranan ma ya bar kasar, a hankali ya mike ya daga kiran Abban nasa. Har suka isa gida khaleel bai ce ma khadijah komai ba, sai dai ya lura duk a sanyaye take, yaji wani mugun tausayinta na dawainiya da shi, jiki ba kwari ta fita daga motar bayan yyi parking ta wuce ciki tana tsoron yanda xata je ta samu Umma, Xaune umma take har lokacin a daki tayi kukan har taji ba dadi, nanny ma duk ta fita hayyacinta da ta tuna sudais ya mutu sai ya rushe da kuka don tun suna jarirai take tare da su. suna ganin khadijah duk suka shanye kukan Khadijah ta karasa da sauri ta xube gaban umma gabanta na mugun faduwa tace "Ummata mai ya faru, why are you crying plss" rungume ta umma tayi ta sake fashewa da wani kukan, Khadijah duk ta rikice ita ma ta fashe da kuka tace "Umma don Allah ki gaya min me ya faru, waye ya mutu?" Nanny ta mike ta bar dakin wani sabon kukan ya xo mata. A sanyaye khaleel yyi reverse ya koma clinic din, dai dai lkcn da Sudais ya fito daga emergency ward, Dr Mukhtar kuma ya sakko kasa rike da shureim, shureim na ganin Khaleel ya nufe sa da sauri, Aliyu ya bi yaron da kallo a sanyaye, khaleel ya duka yana kallonsa murmushin karfin hali dauke fuskarsa yace "How are you feeling now?" A hankali yaron yace "Uncle I want to see my brother plss" Khaleel ya dinga kallonsa ko kiftawa babu, can ya kirkiri wani murmushin yace "He is sleeping now" ya fashe da kuka yace "Nooo, I want to sleep with him too" daga haka ya juya xai tafi inda dan uwansa yake, khaleel ya jawo sa da sauri yace "He is sick, baka son ya samu lafiya, idan kana damunsa baxai samu lafiya ba ai" cikin rawar murya yaron yace "Toh uncle kar ya tafi ya bar ni" Khaleel dake kallonsa ko kiftawa babu a hankali yace "Ina xai je?" Shureim yace "Gida" tashi Khaleel yyi ya kama hannunsa ya fita duk jikinsa a sanyaye. Aliyu dake xaune ya dinga kallon colleagues dinsa dake tambayarsa inda xa a kai gawar sudais ko a nan xai kwana, mikewa yyi da kyar yace "Xan tafi da gawar gida yanxu" a kunnen Barrister sudais da sai lkcn ya fito daga dakin da gawar sudais yake, ya karaso inda Aliyu yake fuska daure yana masa wani kallo yace "Gidan mahaifiyar sa xa a kai gawar yanxu...." kallonsa kawai Aliyu ke yi, Sudais yace "You will be the one to go break the news to her" Aliyu ya d'an bude ido yace "Why me?" Sudais bai sake saurarensa ba ya koma ya dauko gawar ya fita xuwa gun motarsa Aliyu ya bi sa da wani irin kallo. Kusan a tare duk su ukun suka isa gidan, khaleel ya fara fitowa sannan ya sakko da Shureim yana kallon Sudais da ya fito shi ma amma gawar na motarsa, dauke kai khaleel yyi ya shiga ciki yana rike da shureim, Aliyu ya fito daga tasa motar da Doctors biyu suka bi bayan Khaleel, Sudais ya kasa shiga ciki ya jingina da motarsa yana tunanin yanda Khadijah xata dau xan cen rasuwar d'an ta, lumshe ido yyi wasu hawayen na sakko masa, Nanny ce ta bude masu kofa khaleel yasa ta shimfida tabarma a nan balcony, duk gabansa faduwa yake damuwar sa daya khadijah, xuwa yanxu dai umma ta daina kuka bayan ta ce ma khadijah rasuwa aka mata, Khadijah sai kallonta take a sanyaye bayan ta gama kukan ita ma don bata san waye ya rasu ba kuma umma bata gaya mata ba, Umma ta sa Hijab ta fito a sanyaye ba tare da tace ma khadijah komai ba, khaleel ya dinga kallon umma da wasu hawayen ke xubo mata ganin su, Aliyu ya kasa kallonta a sanyaye yace "Allah ya yi masa rahama, ya sa mai ceto ne" Khadijah ta fito daga daki da sauri jin muryar Aliyu, kallonsu ta dinga yi daga inda take tsaye can ta karaso da sauri tana kallon khaleel gabanta na faduwa tace "Dr ina sudais din?" Khaleel ya kasa kallonta kuma ya rasa abinda xai ce, dai dai nan Barrister sudais ya shigo parlorn shi ma bayan ya ajiye gawar sudais kan tabarmar da ya gani balcony baya son ya shiga ciki da shi tukun, suna hada ido da khadijah yyi saurin sunkuyar da kansa, A hankali khadijah ta juya tana kallon umma dake share sabbin hawayen dake xubo mata, ta juya ya kalli Nanny da ta jingina da bango tana hawayen ita ma, a rikice ta nufi Aliyu ta durkusa gabansa cikin rudewa tace "Aliyu ka gaya min wani abu ya sami sudais dina ne, don girman Allah ka gaya min" kasa ce mata komai yayi ya kasa kallonta, lkci daya hawaye ya cika idonsa, mikewa khaleel yyi ya nufi kofa xai fita cos he can't stand it any more, ta mike kamar mahaukaciya ta bi bayansa da sauri, tsaye khaleel yyi balcony ganin gawar yaron a wajen don bai san Barrister ya shigo da shi ba, ya juya a hankali yana kallon khadijah dake kallon gawar kan tabarma an rufe, lkci daya jikinta ya dau rawa ta kamo hannun khaleel cikin rawar murya tace "Dr meye wannan, what is it...." Jawota khaleel yayi jikinsa ya rungume ta gam, cikin sanyin murya hawaye na taruwa idonsa yace "Don't forget Khadijah, Allahn da ya baki shi ya fi ki son sa.... Ba wayon ki ba ba dubarar ki ba ya sa ya baki, to yanxu ya amshe kayan sa, sudais addu'arki kawai yake bukata gare sa yanxu, pray to meet with ur son once again in Jannah...." Jin Khadijah tayi shiru ya dago kanta a hankali yana kallonta, a hankali yaji tana neman sulalewa hannunsa yaki saketa, a haka ta suma yana rike da ita. A hankali khadijah ta bude idanuwanta bayan lokaci me tsawo, kwance take kan gado ta dinga bin mutanen dake xaune dakin da kallo, Wata kawar Umma ta taso ta dawo kusa da ita ganin tashi take son yi ta taimaka mata ta xauna, da kyar tace "Anty me ya ke faruwa?" Umma tayi karfin halin xuwa kusa da ita ta xauna tace "Ya jikin khadijah" shiru khadijah tayi tana ta kallon umma, lkci daya ta fasa ihu ta mike ta fice daga dakin da gudu suka bi ta, Aliyu ne ya fara mikewa a compound din ganin ta fito, ga maxa ko ina, Khaleel dake rungume da Shureim dake bacci jikinsa ya dinga kallonta amma ya kasa tashi, haka barrister sudais, tana ganin Aliyu ta taho gun sa ta rike hannunsa cikin matsanancin kuka sosai tace "Aliyu don Allah kar ka ce min sudais ya mutu, you assured me he will be fyn, kar ka ce min ya mutu don girman Allah" kasa cewa komai Aliyu yyi yana kallonta, ta rungume sa tana kuka kamar ranta xai fita tace "Ka ce min bai mutu ba Aliyu, wllh ina son sa, kar ya tafi ya bar ni" Aliyu ya ja ta suka bar wajen xuwa inda babu mutane ya xaunar xa ita ya durkusa yana kallonta, a hankali yace "Iman kin san Allah xai baki shi?" Ta girgixa masa kai hawaye na xuba idonta tace "A'a"