Sashe 101
Noor Al Hayat Complete Hausa Novel · about 6 min read
amma tayi kyau ne ba kadan ba, ta glass khaleel ke ta kallonta ganin jingina tayi da motar bata bude ba ya sa ya bude ya fito ya xagayo ta inda take, ba tare da ta kallesa ba tace "Ina yini?" A hankali yace "Cool, ya boys dina" tace "They are inside, mu je sai ka gaisa da Umma" daga haka ta nufi cikin gidan ya bi ta da kallo da farko kafin ya bi bayanta, Sosai Umma ta tarbi khaleel da yaki kallonta kansa a kasa, xaman ma bakin kujera ya xauna kana ganinsa kasan duk a takure yake, Umma ta tambayesa mutanen gida yace duk suna lafiya, dariya ya ba Khadijah don bata tana xaton yana da kunya haka ba don ko da wasa ya ki dago kansa, Umma da ta lura da haka ita ma ta bar masu parlorn, sai a sannan khaleel ya dago kamar munafuki, khadijah dake ta murmushi tana xuba masa lemo a cup tace "Kamar gaske" mikewa yayi ya mata wani kallo murya can kasa yace "Karya ce dama, am outside" da sauri ta kallesa tace "Me xa kayi a waje" yace "I can't stay here" ta bata fuska tace "Abinci fa xan xuba maka" yace "Ni bana jin yunwa, kawai ki turo min twins" daga haka ya nufi kofa kamar ana hankada sa, Khadijah ta bi sa da harara har ya fita, tsaki ta yi ta xauna kujera tana turo baki, Ba a dau lkci ba ya fara kiranta a waya har ya katse bata dauka ba, ya sake kira ta ki dauka, text ya turo mata yace "Plss Khadijah, ina mota fa ni baxan iya xaman parlorn ba, idan baxa ki fito ba ki turo min su sudais kawai" tashi tayi ta wuce dakin Umma don suna can suna kallo basu ma san ya xo ba, Umma na ganinta tace "Barin sa ki ka yi shi kadai a parlor?" Khadijah ta tabe baki tace "ya fita yana waje" Umma tace "Saboda me?" Tace "Wai baxai iya xama a parlorn ba" Murmushi Umma tayi tace "Shi kuma haka yake da kunya, Khadijah ina kika samo balarabe?" Xaro ido Khadijah tayi lkci daya ta fashe da dariya tace "Ba balarabe bane fa shi" hararata Umma tayi tace "Ya xa ki ce min ba balarabe bane" Murmushi Khadijah tayi tace "Toh ni dai haka yace min" Umma tace "Ya dai ce maki hakan ne, to ki fita ki samesa tunda baxai xauna parlor ba" Tare da su Sudais ta fita, khaleel ya fito daga motar yana kallonta bayan yyi pecking yaran da suka yi murnan ganinsa yace "Har da walakanci koh?" Tace "Nima ae shi ka min" shiru yyi yana kallonta, can yyi murmushi yace "Baki san ina da kunya sosai ba ko" Khadijah bata san lkcn da tayi dariya ba ya dinga kallonta don bai taba ganin dariyarta haka ba, har da rike ciki, ganin yanda yake kallonta ta hadiye dariyar tana murmushi tace "Amma a nan Nigeria kake ajiye kunyar idan xa ka UK koh?" Xaro ido yayi ba don yaranta dake gun ba da babu abinda xai hanasa jawota jikinsa tayi bayanin abinda take nufi, dariya kawai khadijah take tana kallonsa, khaleel ya kasa cewa komai, kawai ya 6uge da shafa lallausan bak'in gashin kansa, ta sata kallonsa ta sake kyalkyalewa da dariya, yyi murmushi ya cire glass din idonsa murya can kasa yace "Xa ki yi bayani ai xa mu koma UK din" ta hade rai tace "So?" Yana murmushi yace "Nothing, ki gaya ma Umma xa mu je shopping da su sudais plss har da ke" khadijah da bata sake kallon fuskarsa ba tace "Noo ban da ni" yace "Plss" tace "Ni baxan je ba da gaske, su dai ka tafi da su" da kyar da kyar khaleel ya lallabata bayan ta sa ya rufe idanuwansa da glass din da ya cire sannan ta yarda xata bi su, amma bayan ta gaya ma Umma idan xata yarda, ganin tare da su sudais ne Umma ta yarda suka tafi bayan tace kar su dade, front seat ya bude ma su Shureim suka shiga, ganin haka ta bude back seat ta shiga, sai da suka yi nisa khaleel yace "Mu je ki gaida mum dita nima, it's just malali here ba nisa...." Da sauri khadijah tace "Noo plss, sai in je a wa?" Yana kallonta murya can kasa yace "A surkarta to be" shiru khadijah tayi ta na kallonsa da mamaki, ya mayar da dubansa kan titi yana driving, da sauri tace "Noo, sae dai a matsayin friend dinka, and am not ready for that Dr don ban ce ma umma xan je ko ina ba daga inda kace xaka kai mu" a hankali yace "Ohk then, amma xa mu biya gidansu jawaheer mu dauketa, I think she wants to shop also" kallonsa Khadijah ta tsaya yi ta ma rasa abinda xata ce masa, ai ko suka isa anguwarsu jawaheer din yyi parking ya dau waya ya kirata yace yana waje, khadijah tayi karfin halin cewa "Toh su sudais su dawo baya" Khaleel yace "Noo xata xauna baya ita ma, no probs" Ba a dau lkci ba jawaheer ta fito, she is a real definition of black beauty, kyakkaywa ce ita din ta karshe, ta bude front seat tace "Sweetheart ashe da gaske xaka xo din" ganin su sudais da Shureim ta wara ido tace "Waoww cuties, ina ka samo su swthrt? They are so cute" gaisheta yan biyun suka yi, duk ta yi masu kiss a goshi, Khaleel dake kallonta yace "Yarana ne" dariya ta yi tace "Kai dear, don Allah waye su, sun min kyau wllh" ya kalli khadijah ta madubi yace "Ga Aunt dinsu a baya nan" sai a sannan jawaheer ta kalli baya da sauri tace "Ohh ban lura ba, hello" Khadijah tace "Hi" jawahir na murmushi tace "You've got sweet siblings" murmushi khadijah ta kirkira, kamar baxa ta ce komai ba sai kuma murya can kasa kamar ana tilastata tace "Thanks" jawahir ta bude bayan motar ta shiga ta rufe khaleel ya ja motar suka bar wajen, ta madubi yake ta kallon khadijah da ta kauda kai tana kallon waje, ita kuma jawahir na ta basa labari da siririyar muryarta da ya cika motar. Farouq dake ta kallon Aliyu da d'an mamaki yace "Ko meye dalilin da yasa kake son sanin sa Dr?" Aliyu ya hade rai yace "Idan xaka gaya min ka gaya min" Farouq yace "He is my good friend, tare muka yi karatu a England degree and masters, his mum from Saudi Arabia, the most simplest woman I have ever known, his dad a Nigerian from kano, shi kadai ne namiji gidansu with 4 siblings duk mata, Dr Ayman ba shi da matsala, he is free with everyone sai dai he don't make friends easily, he is a genuine... He was among those that graduated with d best result during our time, yanxu haka PhD dinsa yake a Uk..." Katse sa Aliyu yayi yace "Am not asking you about his life history or how intelligent he is, ina gidansu yake?" Farouq ya dinga kallonsa da tuhuma kafin yace "I don't think i wil tel you that Aliyu" murmushi Aliyu yyi yana shafa beard dinsa.