← Book details Noor Al Hayat Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 168

Sashe 8

Noor Al Hayat Complete Hausa Novel · about 6 min read

"Sir ga mu Airport din..." Dago kai Aliyu yyi da sauri daga danne dannen wayar da yake yi, ya kada kai yace "Alryt Bilyamin thank you" daga haka ya bude motar ya fita yana rike da karamin travelling bag dinsa, in 2 hrs and a halve har sun shigo Abj daga kd, ko don yayi gudu ne, "Amin nagode" amsar da ya ba Bilyamin kenan dake masa Allah ya kiyaye hanya ya bar gun ya nufi hanyar shiga cikin airport din, yana jin wayarsa na ring a aljihunsa amma sanin warce ke kiransa yaki fiddo wayar. Aliyu na kokarin ajiye karamar jakarsa sama bayan an shiga jirgi ya ji an taba sa, juyowa yyi da sauri, lkci daya ya wara dara daran idonsa ya durkusa yana kallon Little Shuraim dake masa murmushi yace "Waow handsome we met again" Shuraim yace "Sure!" Aliyu ya juya ko xai ga any of his parent ganin babu yace "So how you?" washe hakora shuraim yyi yace "Am fyn Uncle, and you?" Aliyu ya shafa kansa yana murmushi yace "Same sweetheart... Where is ur twin" nuna masa Sudais dake kusa da Nanny tana bude masa cake dinsa a leda yyi, Aliyu ya dinga kallon matar kafin yace "Is.... that your mum?" Shuraim ya girgixa kai yace "Noo she's our Nanny, we left mum at home, we r going to meet aunt in UK in sha Allah" Aliyu ya gyada kai yana mamakin sharpness din yaron don da ganin sa baxai wuce shekara biyar ba, ya kamo hannunsa yace "That's nyc my boy, am also heading there, What's ur name?" "I am Shuraim Muhd" Cewar Sudais yana wara masa ido, Aliyu yace "Waow, ur twin name?" Shuraim yace "Sudais Muhd" Aliyu yyi patting shoulder dinsa yace "That's my boy" mikewa yyi ji da yyi ana announcing ayi fastening din seat belt, Tuni Nanny ta taho tafiya da Shuraim, kafin Aliyu yace komai yaron ya daga masa hannu yace "C ya uncle, well' meet later, may be in UK...." daga haka ya bi Nannynsa Aliyu ya bi sa da kallo yana murmushi, xaunawa yyi seat dinsa, Baturiyar dake wajen tana murmushi tace "You've got a lovely son" Aliyu ya kalleta da sauri,
Sannan ya kalli Shuraim sai kuma yace "Ohhh thanks very much" har jirgi ya tashi Aliyu bai daina juyawa yana kallon cute twins din ba har ya lura sun yi bacci few hours later. Da yamma suka sauka Uk, Aliyu ya mike ganin Twins din duk bacci suke ya nufi Nannynsu da ke kokarin tada su gaba daya, yace "Bari in taimaka maki da guda daya Madam" bai jira cewarta ba ya dau Sudais don ya fi kusa da shi, ya rungumesa yana rike da jakarsa ya nufi kofar fita jirgi, Nanny ta bi bayansa da sauri tana rike da Shuraim da har ya tashi, sai da ya jira suka dau luggage dinsu sannan ya samar masu taxi... tuni Sudais ya bude ido yana kallon Aliyu ya wani tsuke fuska, Aliyu ya sakar masa murmushi yana kallonsa a hankali yace "How you Prince?" Sudais bai amsa ba sai ma kokarin sauka da ya fara yi daga jikinsa, hakan yasa Aliyu ya sauke sa yana kallonsa murmushin dake fuskarsa yyi fading a hankali, Shuraim dake rike da Nanny da ke kkrin saka jakar kayansu cikin booth din taxi yace "Uncle are we going the same way?" Aliyu ya kallesa sannan ya girgixa masa kai yana murmushi yace "No love" godiya Nanny tayi ma Aliyu ta shiga taxin Sudais ma ya shiga da sauri, Shuraim kam sai da ya daga ma Aliyu hannu yace "See u some other time" Aliyu ya gyada masa kai har lkcn bai daina kallonsa ba, Shuraim na shiga ya rufe kofar motar, Aliyu ya daga masa hannu shi ma ya daga masa yana washe set of teeth dinsa, har taxi din ya bar gun Sudais kin daga nasa hannun yyi sai ma dauke kai da yayi, Aliyu ya kasa dauke idonsa a kan yaron. A hanxarce khadijah ta gama daukan duk abinda tasan boys din suna so sanin sun kusa sauka ko sun ma sauka, ta nufi counter ta biya kudi ta bar Mall din, taxi ta samu ya kawo ta kofar gida ta fito ta basa kudinsa sannan ta shiga ciki, ko kadan bata ji dadin tafiyar Vanessa daxu ba, tana kkrin bude kofa taji tsayuwar taxi ta juya da sauri tana kallon gate, bayan minti biyu ta hango twins, ai bata san lkcn da ta ajiye ledar hannunta ba ta nufe su kamar yanda su ma suka nufo ta da gudu, durkusawa tayi ta rungumesu gaba daya suka kankameta barin sudais ita ma duk ta fi maida hankali kansa, kisses ya dinga mata a fuska, shuraim kuma ya dinga kyalkyala dariya yana kallon su, ganin ba saketa xae yi ba ta janye sa ta mike tana dariya ganin yanda Nanny ta tsaya kallonsu, Nanny tace "Toh ba mu kudi mu ba mai cab, ba currency din nan tare da ni" Tashi tsaye tayi da sauri ta bude jakarta ta ciro kudin kasar ta mika ma Nanny, kamar ance ta waiga taga Khaleel tsaye bakin kofar sa, tayi saurin dauke kai, Shuraim ya wara ido yace "Aunt you knw what" hannunsa ta kama da na d'an uwansa ta fara tafiya tace "No Darling" yace "We still met with that uncle I told you about...." Tace "Which?" Maimakon ya bata amsa sai ta ga ya tsaya yana gaida Khaleel dake kallonsu har lkcn, Khaleel yyi murmushi ya karaso wajen yana kallon yaron a hankali yace "How are you handsome?" Shuraim ya wara ido yana nuna masa wandonsa da yyi sagging yace "Am fyn, but...." tuni Khadijah ta ja Sudais da shi dama bai ma da niyyar gaida khaleel suka shiga cikin parlor a ranta tana cewa ita kam ta shiga uku da Shuraim, sai a sannan tace "Which uncle was ur brother talking about" Sudais ya yamutsa fuska yace "I don't think I like him..." Ta d'an bude ido tace "Who?" Yace "The uncle he is talking about," Ta langwabar da kai tace "Why" Sudais ya bude hannu alamar bai sani ba, tace "Where did you guys meet him" Sudais yace "Shuraim will make u understand Anty" dai dai nan Shuraim ya shigo tare da Nanny, ya taho da gudu ya hau kanta, yace "I missed you Anty" ta daura lips dinta a forehead dinsa tace "but I've warned you to stop talking to strangers times without number.. I mean that man u were greeting outside" Ya xaro ido yace "I never knew he was a stranger, sorry Anty" tayi murmushi tana shafa kansa tace "But you don't knw him, so he is a stranger"

*Haske writers association*💡

✨ *Noor-Al-Hayat*✨

_By Khaleesat Haiydar_📚✍🏻

8......
Chapter 8 · 0% Book details