Sashe 28
Noor Al Hayat Complete Hausa Novel · about 4 min read
sauri jin ihu da kukan yarta, tana kallonta a gigice tace "Walida ya aka yi, me ya faru" cikin kuka walidar tace "Xan shiga inyi wanka shine Anti ta fiddo min ruwana ta fito da ni ta saka yarinyar da ta kawo cikin bayin" Hasana da tayi mitsi mitsi da ido tace "Toh Allah ya isan ki, kuma mu xuba da su a gidan nan xan ga ko agolarta xata samu gun xama, ita ma da take a dosane ta ji da kanta mana, tsabar munafurci da neman kugun xama taje ta jajibo yar kishiyar da kilan ma ita ta kasheta ta kashe ubanta, shege ya fasa mu da ita a gidan nan" Umma bata ko kalleta ba ta shiga share kofar parlorn ta, Shafa ta fito tace "Ya aka yi ke kuma da sassafe, ke da wa?" A fusace Hasana tace "Ki rabu da yar kaxa kaza, wai Walida ce xata shiga wanka shine ta fiddo mata da ruwan ta ta saka na shegiyar da ta kawo mana mai kama da aljanu" Shafah ta rike ha6a tace "Ikon Allah Walida da xata makaranta? Ita kuma agolar da take gida, Mutum dai bashi da aiki sai neman fitina, banda jakanci ma ina aka taba dauko agola ace xa a takura ma masu gida dominta" Hasana tace "Ke fa kika san jakanta, amma ni nasan maganinsu wllh, kuma xa mu sa kafar wando guda da su" daga haka ta kalli yar ta tace "In ta fito ki kwara ruwa bayin ka fin ki shiga, Allah dai ya tsine duk mai son takura ku gidan ubanku ehe" daki ta shiga tana ci gaba da kumfar baki, Shafa ta bi bayan ta tana cewa "Amin dai, Allah kuma ya kawo mana karshen bala'in nan, muna xaman xamanmu dai" Khadijah bata fito ba duk da ta gama wankan, sai leken tsakar gidan ta kofar bayin take taga ko sun tafi, ganin Walida ce kadai xaune tsakar gida ta fito tana gyara daurin da tayi ma Xanin jikinta ta ta nufi dakin Umma da sauri, taji Walida tace "Shegiya kawai" kallonta khadijah tayi tace "Back to sender" sannan tayi saurin shigewa dakin ummanta. Kafin karfe bakwai da rabi duk yaran gidan an shirya wucewa makaranta, jin muryar Abban fadila a waje, Umma ta kalli khadijah tace "Go outside and greet him. Come back immediately after that" khadijah ta fita waje ta gansa tsaye ya shirya alamar xai fita kasuwa yana sauraren yaransa mata biyu da suke requesting kudin wani littafi da xa su siya a boko ga iyayensu tsaye bakin kofa, Khadijah ta karasa kusa da shi ta durkusa a hankali tace "Good morning sir" ya kalleta yace "Morning yar turawa, how was ur nyt?" Ta washe hakora tace "It was splendid" yace "Good, ina mamar taki?" Ta kalli kofa tace "Tana ciki" yace "Kira min ita" Shafa da Hasana da lkci daya mood dinsu ya canxa suka kalli juna, juyawa khadijah tayi taje kiran Umma suka fito a tare, Yace "Naga baki shigo gaisheni ba" Umma tace "Bayan nayi sallah I just slept off" yace "Ohk, anjima sai ki je ki mata registern islamiyya ko xuwa next week sai a samu boko a sata" Umma tace "Toh nagode, Allah ya kai mu" Naira Dari ya Ciro ya mika ma khadijah yace "Gashi ki siya biscuit" xaro ido tayi ta kalli Umma, Umma tace "Amsa" ta karba da hannu biyu tana murmushi tace "Nagode uncle" daga haka Umma ta ja ta suka shiga ciki ba tare da ta yarda ta kalli inda kishiyoyinta dake cika suna batsewa suke ba, Shafa tace "Toh Abban Fadila kudin kitso da na tambaye ka tun jiya fa?" Hasana tace "Ni tun shekaranjiya nake ta bi ya sa min kati amma kinga wani gwaninta a nan" Tuni ya isa kofa bayan ya sallami yaransa mata dake turo baki kudin bai ishesu ba, sai da ya fita gidan, Hasana tace "Toh wllh abinda baxai yiwu ba kenan, ya gama ji da nasa yaran mana, har xa a kara daura masa nauyi bayan wanda ke kansa, ko ita yarinyar bata da dangin uba ko uwa ne sai karere??" Shafah tace "Ke fa kika San karere, ita nan gwaninta take a idon duniya ko, toh kuwa xata sha kunya in har bata mayar da yarinyar nan gun dangin ubanta ba, sai yarinyar nan ta ja mata masifa da bala'i sai kuma ta dauko mata abun kunya muna nan dake, sai dai idan ba ni ce nan Shafa'atu yar gidan Sanusi jikar Yakubu na bude baki na yi magana ba" Hasana tayi shewa tace "In sha Allahu kuwa" Umma dake ta jin su ta girgixa kai tana murmushi a ranta tana masu addu'ar samun sauki, sai bayan da duk suka gaji suka shiga ciki ta dauko kibiya da comb xata tsefe ma khadijah gashinta, Tuni khadijah ta fara matsar kwalla tun kan ta kama kan din right from Beginning idan ana son tashin hankali toh a taba gashinta, sosai ta ba Umma wahala ta dinga rusa kuka tana ihu, har dai aka gama tsefewa ta bata Hijab ta sa suka fito don xuwa saloon a wanke mata gashin, da ido su Hasana suka bi su har suka fita.