Sashe 91
Noor Al Hayat Complete Hausa Novel · about 5 min read
don bata son ta bar sa yyi ta jiranta, yana parking kofar gidan da ta nuna masa yace "Nan ne gidanku?" Ta gyada masa kai ta bude motar ta fita, yace "Toh ki gayar min da su mama da mutan gida" a sanyaye tana kallonsa tace "Xa su ji nagode sosai" daga haka ta juya xata shiga gate, yace "Wait Khadijah baki ban number ki ba mu dinga xumunci" dawowa tayi ta kira masa numberta yayi saving yana kallonta yace "It's nyc meeting you once more Khadijah" ta kirkiri murmushi ta daga masa hannu ta shiga cikin gida, Nanny na kitchen su sudais kadai ne xaune parlorn ta sa masu cartoon, khadijah ta ajiye ledan hannunta ta isa kusa da su ta xauna tana kallonsu, su ma kallonta suke, ta yi murmushi ganin irin kallon da suke mata ta yi masu kiss gaba daya, Sudais ya goge bakinsa shureim na ganin haka shi ma ya goge nasa, jikinta yyi sanyi sosai tana kallonsu, bata san lkcn da hawaye ya kawo idonta ba ta mike ta wuce daki da sauri, Nanny ce ta shigo dakin ganin khadijah kan gado tana hawaye da mamaki ta karaso da sauri tace "Mum twins me ya faru kuma?" Cikin rawar murya tace "Wai don na masu kiss shine suke goge bakinsu" dariya sosai Nanny tayi kafin tace "kai Khadijah shine har da kuka, to kyalesu xan yi maganinsu" daga haka Nanny ta juya ta koma parlor, taso keyar boys din tayi suka taho dakin, kusa da khadijah ta ajiye su duk suka shiga kkrin sauka daga kan gadon Nanny ta daure fuska tace "C'mon, duk wanda ya sakko xan xane sa, ita ce uwar ku ba ni ba" Kuka suka fara yi kuma basu sauka kan gadon ba, Nanny na kallon khadijah dake ta kallon kyawawan yaran nata tace "Yanxu abinda xa mu yi shine xa su dawo kwana nan dakin, ke xaki dinga masu wanka ki shirya su, ke xaki dinga ba su abinci hakan kadai xai sa su saki jiki da ke" a hankali khadijah tace "Toh" Nanny tace "Don haka duk safe kafin ki tafi school sai kin masu wanka kin shirya su ni kuma in hada masu breakfast sai in baki ki basu" kai kawai Khadijah ta gyada don har ga Allah bata son gudun ta da yaran suke, haka Nanny ta fita ta bar su suna kuka xa su bi ta, amma da yake suna jin magana bbu wanda ya sauka daga kan gadon kamar yanda tace masu, suka gama kukansu suka yi shiru suna kallon khadijah, Sudais yyi tapping dinta yana nuna mata kofa yace "Nanny..." Murmushi Khadijah tayi ta jawo sa jiki tace "Nima Nanny ce ai" hakura yaran suka yi suna ta xaune dakin kusa da ita har bacci ya dauke su, Nanny na ganin lkcn tashin su ya kusa misalin karfe biyar na yamma ta dama masu custard ta dafa masu indomie ta kawo ma khadijah dakin ta fita ta rufe masu kofa, a lkcn kuma suka tashi, duk suka yi jigum suna kallon khadijah, ruwan wanka ta hada a bathroom dinta tayi masu gaba daya sannan ta fito ta shafa masu mansu dake dakin ta sa masu singlet da pant ta xaunar da su kan carpet ta shiga basu custard din suna karba, har ranta ta ji dadin hakan suna gama sha kuma ta fara basu indomie da egg din, shureim na koshi ya fiddo wanda ta sa mashi a baki ya mike ya kai mata bakinta, murmushi tayi ta bude bakinta ya xuba mata abincin ta shiga ci a hankali. Sai kusan karfe shidda Khadijah ta fito parlor da yan biyun nata, cartoon ta sa masu parlorn duk suka xauna kan kujera suna kallo basu bi ta kan Nanny ba, da daddare a kan gadon ta ta shimfide su bayan sun yi bacci, ta gama shirin kwanciya kenan ita ma wayarta ya fara ring, ita dai bbu mai kiranta a waya ban da Nanny sai wata classmate dinta Aisha dake sonta sosai, ta dinga kallon number kafin ta daga, sallama yyi mata jin muryar hankalin ta ya dan kwanta sai dai bata san dalilin kiran ba ta amsa masa sallamar ta gaishesa yace "Ko kin fara bacci ne?" Ta girgixa kai tace "A'a yanxu dai xan yi" yace "Ohk, ya mutan gidan?" Tace "Lafiya lau Alhmdllh" yace "Maa sha Allah" shiru ta yi bata ce komai ba, a hankali yace "Kawai sai kika bar garinmu ba sallama Khadijah" tayi murmushin karfin hali tace "Ummata ce ta xo ta dauke ni ai" yace "Allah sarki, but dama me ya kawo ki gidan tun farko" khadijah da taji kamar kar tace komai kawai ta yi murmushin takaici tace "Ai yayan Abbana ne" yace "Are you serious?" Tace "Uhn" yace "Waow, to me yasa basu baki abinci" ta wara ido tace "Suna bani fa, ni ce ban iya cin abincin ba lokacin" murmushi yyi yace "Allah sarki, kwanaki ma ai kawun naki yyi accident kin sani koh" Khadijah ta bude ido sosai tace "Haba dai, ban sani ba, basu gaya mana ba" Sadeeq yace "Ehh amma da sauki yanxu ina jin ya samu lafiya ma" A hankali khadijah tace "Toh Allah ya kara kiyayewa" yace "Ameen" shiru ne ya biyo baya kafin yace "Kin taba ba Umma labarina" Khadijah da taji jikinta yyi mugun sanyi a hankali tace "Kowa ma ina ba labarin ka, cos you fed me when I was in need of food" Sadeeq yace "Noo I did that for the sake of Allah, not for you to tell everyone" murmushi kawai khadijah tayi a sanyaye, shi ma murmushin yake yace "Sure, yaushe xa ki hada ni da Umma mu gaisa ko kuma in xo har gida in gaisheta, ko baki son mu yi xumunci sosai?" gabanta ne yyi mugun faduwa and she was totally lost of words, a hankali yace "Hello, Khadijah are you there?"