← Book details Noor Al Hayat Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 69 OF 168

Sashe 69

Noor Al Hayat Complete Hausa Novel · about 6 min read

ya dau spare key dinta da ya cire ya fita dakin ya nufi nata, saka makullin yyi ciki yana addu'ar Allah yasa ta cire makulli jikin kofar, yana murdawa ya bude ya tura kofar dakin, xaune ya ganta ta jinginar da kanta jikin gado, ya karasa da sauri ya durkusa gabanta yace "Kin samu kin ci abincin kuwa Amira?" Shiru yyi yana kallonta ganin yanda idonta ya kumbura, ya sauke idonsa kan ledan abincin da ya ajiye mata jiya da daddare, bude ledan yyi yaga bata taba abincin ba, ya wani hade rai yace "What's wrong with you, tun dare kike kuka har yanxu?" Ta girgixa masa kai da sauri muryarta na rawa ta nuna masa kirjinta tace "Yana min ciwo" sauke ajiyar xuciya yyi murya can kasa yace "Kin yi wankan?" Ta girgixa masa kai, yace "Sallah fah?" Nan ma girgixa masa kai tayi, mikewa yyi ya shiga bathroom da ke dakin ya hada mata ruwan wanka ya fito yace "Tashi ki je ki yi wanka, you will feel more better" a hankali ta tashi ta wuce bathroom din, yana ta xaune har ta fito da kayan ta da Hijab ta kwanta kan gado ta dukunkune waje daya, ya mike ya rufa mata bargo, ba a dau lkci ba ya ga alamar bacci ya dauketa, tashi yyi ya kashe wutan dakin ya nufi kofa ya fita ya rufe. Da asuba bayan sudais ya idar da sllh ya koma dakinta yaga har lkcn bacci take ya koma dakinsa shi ma ya kwanta. Da safe ya fita hotel din don nema mata kunu, wani almajiri da ya gani kan hanya ya ba kudin ya tafi gun masu siyar da kosai ya siyo masa kunu, yana ta jiransa gaban wani store har yaron ya dawo da kunun a cikin leda, karba yyi yyi masa godiya ya bar masa canjin dari takwas din don na Dari biyu yaron ya siya, ya mike ya amshi ruwa bakin store din da yake ya dawo kan bench ya xauna ya bude bottle water din ya sha kadan ya xubda sauran sannan ya juye kunun ledan a ciki ya mike ya koma hotel din, tashinta yyi daga baccin da take ganin tun jiya bbu abinda ta ci, ta tafi bayi ta kuskure bakinta kamar yanda ya ce mata, da alwala ta fito yana ta xaune yana jiran ta gama sallah, duk ta galabaita kafin ta idar, ya dawo kusa da ita ya mika mata bottle din kunun bayan ya bude yace "Gashi ki sha ko ba yawa kin ji" kai ta gyada masa ta karba ta kai baki a hankali har wani rawa hannunta yake, kusan rabi ta sha kunun ta ajiye ta jinginar da kanta da gado, yace "Ki daure ki kara kadan" ta girgixa kai da sauri tace "A'a xan yi amai idan na sha kuma" rufewa yyi yace "Toh ki kwanta kafin in yi wanka xa mu je can gidan step mum dinki" shiru ta yi ta bi sa da kallo har ya fita dakin, da yake ba ya rabo da spare clothes a motarsa can ya tafi ya dauko kayansa yana gama wanka ya canxa. Ko da ya dawo dakin idon Khadijah a lumshe yake duk da ba bacci take ba, tausayin kanta kawai take don bata san wani irin rayuwa xata fara yanxu ba kuma, ita da ba kowa gareta ba a duniyar, muryarsa da taji ya sa ta bude ido da sauri don bata ji shigowar sa ba, ta mike xaune yace "Let go, it's almost nine yanxu" tashi tayi ta sauka daga kan gadon, ya dau ledan abincin jiya da bata ci ba ya fita tana biye da shi a baya, nan reception ya bada makullan dakin ya nufi wajen hotel din xuwa Parking lot, ya bude mata front seat ta shiga sannan ya xaga ya shiga maxaunin driver, sai da ya hau kan titi yace "Ina ne gidan step mum din naki yake?" Kamar xata yi kuka tace "Wllh tsoro nake ji kuma tace kar in kashe mata aure, I don't want to be the cause of that" yana kallon titin gabansa yace "Kar ki damu you will remain inside the car, while we talk" kai ta gyada masa a hankali hawayen dake makale idonta ya sakko, yace "Clean those tears now" da sauri ta goge idonta, tana ta nuna masa hanyar gidan bayan sun shigo anguwar, ganin sun kusa a hankali tace "Plss ka tsaya da motar a nan kaga gidan can" ya tsayar da motar ya na kallon gidan da take nuna masa, kashe motar yyi yace "Ya sunan step mum din ki?" Tace "Hajiya Amina" bude side dinsa yayi ya fita, ta bi sa da kallo ganin yanda yake tafiya har ya isa kofar gidan ya tsaya, wani yaro ne ya fito gidan dake kusa da gidan ya kirasa, yaron ya taho sudais ya duka yana kallon yaron yace "Big boy... shiga gidan nan kace ana sallama da Hajiya Amina" yaron yace "Toh" sannan ya shige gidan da sauri, ba a dau lkci ba sai ga Shafah da Hasana sun fito ko wacce daga mai riga a kai a matsayin mayafi sai mai wando, Sudais ya dinga kallonsu daga sama har Kasa, Shafa dake ta kallon sudais tace "Sannu da xuwa bawan Allah" yace "Ina kwanan ku" a tare suka amsa masa, ya shafa lallausan gashin kansa da ke kara masa kyau yace "Dama Hajiya Amina nake son gani" a tare suka hade rai Hasana tace "Yar uwar ka ce?" Ya girgixa kai tace "Halan kudi xaka karba gunta? Toh Allah sa dai ba yawa, don kuwa Amina xamanta ya xo karshe gidan nan tun shekaranjiya don kuwa Alhaji ya saketa, yanxu haka ko tsinkenta babu a gidan" Kallonsu Sudais yake a sanyaye, Hasana tace "Atoh, ban da mugunta ki tura yar mutane karuwanci don ba ke kika haifeta ba yarinya marainiya bata da kowa duniyar nan banda Allah, dama an ce idan mutum xai gina ramin mugunta yyi ta yar karama.... To ita kam da xurfi tayi sa gashi ta afka ciki" Sudais da ko kadan bai san ma abinda suke cewa ba yyi karfin halin cewa "Toh don Allah kun san garinsu?" Shafah tace "Halan kudin da yawa, matar da har gorin cin bashi take mana ashe a boye take nata" Hasana tace "Mun dai ji kishin kishin a gari ta siyar da duk kayan dakin nata wai xata koma kasarsu, ka san 6are ce ba yar Nigeria ba" Sudais yace "Ina ne kasar ta su?" Shafah tace "Wai ko Ethiopia ko morocco ko Sudan oho dai... amma nan Africa ne, mu dai Allah ya raba mijinmu da alakakai" juyawa sudais yyi ransa a dagule ya nufi motarsa yana shiga ya hade kai da steering yana tunanin ta ina xai fara, ya xai yi da yarinyar nan da kowa ke kira da marainiya, khadijah da ke ta kuka tun bayan fitarsa cikin rawar murya tace "Ummata na fushi da ni har yanxu koh?" Dago kansa yyi yana kallonta da idanuwansa da suka sauya kala.
Chapter 69 · 0% Book details