Sashe 22
Noor Al Hayat Complete Hausa Novel · about 4 min read
da yake idan tana wanke wanken, yanxu an ma daina sa ta sharan gaba daya tsabar kawai bata iya ba sai dai wanke wanke da jan ruwa wani lkcn a waje idan bbu wuta, tun ranan da ta fita har yau bata sake fita ba sai dai idan an aiketa gun mai kanti ko kuma xata debi ruwa a er karamar bucket da take dauka, har yau bata sake cin abinci mai dadin gidan da taje ba, abincin gidan kawu daga taliya sai tuwo da shinkafa da wake da mai da yaji, gashi duk bata son su hakan yasa take tare da yunwa sosai, Hafsa ta fito ta jefa mata kudi tace "Khadijah wai Mama tace ki je gun mai kanti ki siyo sabulun wanki da Hypo leda biyu, sai ki siyo maggi mai tauraro na hamsin" Khadijah ta turo baki bata ce komai ba, tashi tayi bayan Hafsah ta wuce sanin Hajiya na iya lekowa taga ko ta wuce, ta shiga parlor Hajiya Salaha tace "Aiken fa" ta kalli kayan jikinta tace "Mama xan canxa kaya" dakuwa tayi mata tace fita Ki ban guri, shashasha sshe da gangan kike jike kayan wajen wanke wanke kenan kin san abinda ya kamata" juyawa tayi ta fita, ta sake kallon kayan dake a jike tun daga saman gwiwanta har kasa, gate ta nufa kanta sanye da hula don gaba daya Hijabs dinta yaran gidan sun gaje, tafiya ce me nisa xuwa gun mai kanti, tana tafe tana wasa da d'an karamin iccen hannunta, har ta wuce gidan da taje ta ci abinci idonta na kan gate din gidan amma ba daman shiga, tana isa gun mai kanti cikin aiken da aka mata maggi kawai ta tuna, gida ta koma da sauri ta shiga parlor tana kallon Hafsa kamr xata yi kuka tace "Me da me kika ce ma" Hajiya Salaha tayi wani murmushi ta na kallon kishiyarta tace "Me na fada maki" Hajiya Maimuna tace "Kin ji na maki musu? Ko an taba aikenta bata dawo tambayar me aka aiketa ba dama" Hajiya Salaha ta ce "Wllh Ubanki ya cuce rayuwar ki, kishiyar uwarki kuma kiri kiri ta nuna bata son ki tunda har ta sangarta ki haka ta lalata ki saboda ba ita ta haife ki ba, banda haka wannan xabgegiyar budurwa godai godai kullum aka aike ki sai kin dawo wai kin mance, sai shegen turancin iyayi.... ni dai wllh tunda yarinyar nan ta xo gidan nan nake fama da surutu abinda yaran da na haifa ma basu sa ni ba, Allah dai ya isa wllh" Hajiya maimuna ta tabe baki tace "Ke kika ga xa ki iya, ni kinga ina yi? Ai sai dai duka" Kabir ne ya sake nanata ma khadijah Aiken da aka mata ta fita da sauri tana maimaita abinda yace a ranta har ta isa gun mai kantin sannan ta fada masa, yana dariya yace "Ke yar fari ce ko?" Ta wara ido tace "I don't understand" dariya yyi yace "Aa ni ba bature bane, don nema maki saukin kai wa da dawowa idan an aikeki kawai kice a dinga rubuta maki sakon a gida kinji" tace "Ohk then" muryar da taji yana cewa a bashi kati ya sa ta juyawa da sauri, suka hada ido ta washe fararen hakoranta tace "Good evening" daga sama har kasa ya kalleta yace "How you?" Ta langwabar da kai tace "I shud say fine" yana gyada kai yace "Good" karban card din da mai kantin ke mika masa yyi yace "Doguwa dake baki sa Hijab idan xa ki fito" a hankali tace "Bani da Hijab yanxu" bai ce komai ba yana loda card din kafin yace "Toh me yasa kika jika kayan ki" tace "Wanke wanke nake yi tun da rana" yace "Ina ne gidan ku?" Tace "Our home is 3 house's away from u people's" ya kalleta yace "Gidan Alhaji Jibril?" Ta gyada masa kai, yace "Ke yarinyarsa ce" ta girgixa kai a hankali, yace "Yaushe kika xo gidan!" Ta kalli sama kamar me naxari sannan tace "10 days ago" ya gyada kai bai ce komai ba, ta amshi ledan sakonta da canji tana kallonsa kafin tace komai yace "Ya sunanki?" Tace "Khadijah" yace "Good" a hankali tace "Ina son in xo in ci abinci gidan ku amma an hanani, kuma I can't eat the food they are cooking, it's just concoction" a hankali ta karashe maganar, yace "Me yasa aka hana ki?" Tace "Su mama sun ce xa su kashe ni idan na sake xuwa ko ina kuma ina jin tsoro" ya kalleta bai dai ce komai ba, ta matso kusa da shi a hankali tace "Ko xaka dinga kawo min abincin gidan ku da kanka?" Ya buda ido yace "Ina?" Tace "Gidanmu mana, sai in dinga boyewa a backyard ina ci" tana magana ne hawaye cike fararen idonta, jin yyi shiru ta ci gaba tace "I am always hungry...." Ya sauke idonsa daga kanta bai dai ce komai ba.