← Book details Noor Al Hayat Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 164 OF 168

Sashe 164

Noor Al Hayat Complete Hausa Novel · about 8 min read

Daren ranan a gidan khadijah ta kwana don Aliyu bai takura ta sai sun koma gida ba shi dai yayi wucewarsa, washegari yayyin mahaifiyar ta maxa duk suka wuce bayan sun cika ta da kyautan kudi mai yawa tunda basu samu sun mata komai na aure ba, Su Safeenah basu yarda sun bi iyayen nasu ba wai sai sun je gidan khadijah, Hajiya Rahamah tace "Gaskiya kam ya kamata ku je sai ku dawo anjima da yamma" Khadijah taji dadi sosai tace "Umma don Allah su kwana mana" Mum dinsu Jawahir tace "A'a su dai dawo da yamma" ta marairaice tace "Toh sai mu dawo tare" Hajiya Rahamah tace "Ki dawo kiyi me khadijah, ina kika taba jin amarya na yawo daga kai ta dakinta, wannan ma ai lalura yasa kika fito..." shiru khadijah tayi bata ce komai ba jikinta yayi sanyi, Driver aka sa ya maida su can gidan nata, Mum din Jawahir tace "Sai ki fara kiran mijin naki ki sanar da shi xuwan ku" a hankali khadijah tace "Toh..." Daga haka ta mike ta tafi daki ta dau wayarta, kiran Aliyu ta shiga yi, yana dagawa yayi sallama yace "Good morning wife" ta turo baki tace "Xa mu dawo gida yanxu da su Safeenah" yace "Ohk, in taho in dauke ku ne?" Tace "A'a driver xai maido mu" yace "Alryt then, Allah ya kawo ku lafiya, am already missing you dear" Bata ce komai ba ta katse wayar ta, Sha biyu saura suka dau hanyar gida tare da Safeenah, Deejah da Maimoon, a waje drivern yayi park duk suka sauka motar suka masa godiya, khadijah ta bude gate din tana gaida mai gadi dake gaisheta shi ma, sauran duk suka gaisa da shi sannan suka bi bayanta, a hankali ta murda kofar parlorn, Babu kowa ciki sai sanyin ac da tv dake a kunne, ta shiga su Safeenah na biye da ita har cikin parlon duk suka xaxxauna, tana murmushi tace "Bari in kawo maku ruwa" Bata jira cewarsu ba ta wuce Kitchen ta dauko tray da cups ta bude fridge ta daura lemo da ruwa a kan tray din ta dawo ta ajiye masu, Safeenah na murmushi tace "Thanks sis" murmushin tayi ita ma ta wuce sama, a hankali ta bude kofar bedroom din Aliyu, xaune ta samesa yana operating laptop, ta hade rai tace "Baxa ka taho ku gaisa da su ba" ajiye laptop din yayi yana murmushi yace "I was waiting for ur instruction ne dama kar in yi laifi" hararansa tayi ta juya ta wuce, yana murmushi ya mike ya bi bayanta, har ya shigo parlorn yana kallon su Safeenah yace "Sannun ku da xuwa" duk suka gaishesa da fara'a, ya xauna saman kujera yana murmushi yace "Lafiya lau, fatan kun baro mutan gida lafiya" duk suka ce "Alhmdllh" yace "Maa sha Allah" sannan ya mike yana kallon khadijah ya koma sama, mikewa tayi tace "Mu je sama ku yi alwala it's almost time for zuhr" tashi suka yi gaba daya suka wuce sama xuwa dakinta, sai bayan da suka idar ta cire hijab dinta tace "Let me cook something for us" mikewa suka yi gaba daya Safeenah tace "We will do that together" dariya kawai khadijah tayi, tuwon shinkafa da lafiyayyen veg soup suka hada gaba daya, aikin yayi sauri saboda yawansu, Safeenah na gama kwashe tuwon a leda tace "Toh ina xa a sa ma mijin ki" khadijah tace "It's not necessary, namu ne kadai, nasan eatry xai je shi" Deejah ta saki baki tana kallonta tace "Eatry kuma Namecy?" Murmushi kawai khadijah tayi, Maimoon tace "Uhmm lallai ma, tun yanxu xa ki fara sakaci haka Khadijah?? Har kina son mijin ki ya tafi wani waje ya ci abinci" Kallonta khadijah tayi bata ce komai ba, Safeenah ta dauko wani kwali mai dauke da cooler mai kyau ta fiddo babba da karami ta tafi sink ta wanke shi tas ta tsane sannan ta sa tuwo ta rufe, Deejah ta dau na miyan ta xuba miya da isasshen nama a ciki ta rufe duk suka daura a tray, ita dai khadijah na tsaye tana kallonsu kamar an dasa ta, Maimoon ta dauko plate mai kyau da spoon da cup ta dauraye ta daura kan tray din, Safeenah ce ta hada xobon dake ajiye tun daxu suna jiran ya huce, xobon ya ji kayan kamshi da abarba da cucumber, ta xuba kananun kankara kan thick xobon, sabon jug ta dauko ta kusa cika jug din ta rufe, tana kallon khadijah tace "Sai ki kai masa daki, ko shi ma waitress din eatry xa su maki??" Khadijah bata san lkcn da tayi dariya ba sai dai bata ce komai ba ta dau tray din abincin da drink ta fita kitchen din ta wuce sama, a hankali ta tura kofar dakinsa, yana xaune yana danna laptop har sannan, ya dago yana kallonta har ta iso inda yake ta durkusa ta ajiye tray din ba tare da ta kallesa ba ta mike ta nufi kofa ya bi ta da kallo har ta fita, yayi murmushi sanin this might not be her thinking, infact it's not even her thinking... Khadijah ce xata kawo masa abinci haka kawai, shafa kai yyi yana murmushi. Kafin ta koma kitchen din duk sun wanke duk abubuwan da suka bata, Maimoon ta fito masu da abincin nan tsakiyar parlor, Xaunawa suka yi gaba daya suka ci a tare, Deejah ta gyara wajen ta tafi da komai kitchen, suna ta xaune parlor suna hira khadijah ta dinga jin kamar kar su ce xasu tafi, ta dinga addu'ar Allah sa su manta kawai su kwana, suna nan a haka har aka kira la'asar suka wuce sama xuwa dakinta duk suka yi sallah, sai a sannan suka fara shirin komawa gida, duk jikin khadijah yayi sanyi ta xauna can karshen gado tana kallonsu a sanyaye, Dariya Deejah ta dinga mata, Safeenah na gama gyara fuskarta ta dawo kusa da ita tace "Kar ki damu sis xa mu dinga haduwa frequently in sha Allah kin ji, Kuma ga waya xa mu dinga communicating" hawaye ne ya cika idon khadijah, Safeenah tayi dariya tace "Tabb, to mu fa gobe da safe xa mu koma Abuja, Deejah kadai ce a nan, kema nasan soon xa ki koma uk saboda karatun ki" Ita dai khadijah bata ce komai ba, bayan duk sun gama Safeenah tace "I notice something khadijah, it seems har yanxu baki kwantar da hankalin ki da mijin ki ba, are you still thinking of the past koh? I will advice you to just erase that of ur mind idan ba haka ba baxa ki taba samun kwanciyar hankali gidan ki ba, nobody is above mistake khadijah, barin ma irin wannan mistake din da aka yi ba da gangan ba, wllh idan baki maida hankali kin rungumi mijin ki ba kina ji kina gani wata a waje xata yi hakan ga mijin ki very handsome gentleman, Wallahi Kar ki kuskura wata ta hango maki shi a waje, don rashin samun kulawa gun ki xai sa ya ba ta waje dama, Haba sai kace ba wayayya ba Khadijah..." turo baki khadijah tayi, Safeenah ta dawo kusa da ita ta kamo hannunta tace "that's just it, kiyi hakuri ki xauna xuciya daya da mijin ki, forget the past, ni na tabbatar mijin ki yana son ki kema kuma kina son sa sosai" Khadijah ta sauke idonta a hankali, Maganganu sosai Safeenah ta yi mata da yasa duk jikinta yayi sanyi, daga karshe ta mike tace "Toh mu xa mu tafi khadijah sai mun yi waya" khadijah ta mike a hankali tace "Bari in gaya masa" daga haka ta fita ta shiga dakin Aliyu suka kusa cin karo don fitowa xai yi shi ma daga dakin, jawota yayi jikinsa ya rufe kofar yana kallon eye balls dinta, ta sauke idonta tace "Sake ni" ba musu ya saketa yana murmushi, tace "Xa su wuce" yace "I was thinking kwana xa su yi" ta girgixa kai tace "Gobe da safe xa su wuce Abuja" yace "Ohk ba nan suke ba dama?" Tace "Deejah ce kadai a nan" yace "Alryt am coming now" juyawa tayi ta fita, turarruka da kayan kwalliya na lefenta ta debar masu mai yawa suka sauka downstairs tana jin kewansu, ba a dau lkci ba Aliyu ya sauko, dubu talatin ya ba su gaba daya, suka ki amsa, khadijah ta hade rai ta karbi kudin hannunsa ta bude jakar Deejah tace "Ae ba ku kuka ce ya baku ba toh" Murmushi kawai Aliyu yake yana kallonta, suka masa godiya yace "No thanks sisters, or shud I drop you?" Safeenah tace "A'a mun gode xa mu tadda driver bakin titi" yace "Alryt then, Allah ya kiyaye hanya" duk suka amsa masa da Amin, har bakin gate khadijah ta rakasu, Maimoon tace "Kin ga ki koma haka mun gode sosai Khadijah, Allah bar xumunci" sai a sannan hawaye ya cika idonta cikin sanyin murya tace "I am going to miss you all" rungume juna suka yi gaba daya, tana ji tana gani suka wuce ta juyo ta koma ciki tana goge hawayen dake xuba mata, Aliyu dake parlor ya dinga kallonta har ta wuce sama. Ko minti talatin su Safeenah basu yi da barin gidan ba Barrister ya xo, Aliyu ya bude masa kofa suka gaisa, Barrister ya xauna kan kujera yace "Ya gidan" Aliyu na shafa kai ya xauna shi ma yace "Alhmdllh, ya aiki" Barrister yace "Mun gode Allah, ya mum shureim" Mikewa Aliyu yayi yace "She's upstairs" daga haka ya wuce sama, bude kofar dakinta yayi ya ganta kwance ta rufe fuskarta da pillow, ya isa kan gadon ya xauna kusa da ita ya dagota a hankali yace "Ummu Shureim" Bude ido tayi tana kallonsa, ya sakar mata lallausan murmushi yace "Mu je ku gaisa da Barrister" tace "Ya xo?" Yace "Sure" shi ya taimaka mata ta sauko saman gadon bayan ta sauko ta kwace hannunta shi dai bai ce komai ba ta sa hijab dinta suka fita dakin, gaisawa suka yi da Sudais ya mika ma Aliyu takardan hannunsa yace "Bata ta gani, I don't want to do anything without her knowledge" Aliyu ya amsa ya mika mata, karban takardan tayi ta bude tana kallon content din,
Chapter 164 · 0% Book details