Sashe 137
Noor Al Hayat Complete Hausa Novel · about 8 min read
Khadijah na kwance bedroom dinta waya kare kunnenta tana sauraren Umma dake mata magana, bayan wani lkci ta turo baki a hankali tace "Umma ni ce masa nayi ko wanne, I don't have choice..." daga daya bangaren Umma tayi murmushi tace "You know ur problem Khadijah?" Khadijah ta girgixa kai a hankali kamar tana ganinta, Umma tace "Kin ki kwantar da hankalin ki to know what's best for you, sure ni na san kina son khaleel but he is married kin sani, me yasa har yanxu xuciyar ki ke yaudarar ki?" da mamaki Khadijah ta dinga sauraren Umma, can dai tace "Umma how did u knw he is married?" Umma tace "Ya xo gida ranan Saturday, he told me about his wedding" Khadijah taji hawaye ya taho mata ta kasa cewa komai, Umma tace "Ke da bakin ki kika ce masa barrister... to don me kuma baxa ki kwantar da hankalin ki da Barristern ba, it's not as if Khaleel isn't good, but I think barrister Aliyu is the best for you, Kuma khaleel daga aure ai baxai fara xancen auren ki ba kuma, Khadijah as a mother nake gaya maki ki kwantar da hankalinki ki ba barrister chance you won't regret it, idan kuma kinga khaleel din ke xuciyar ki to sai ki tanadi kalaman da xaki gaya ma barrister but count me out kar ma ki nuna masa na san komai" Hawaye na sakko mata cikin sanyin tace "Ni ai ban ce ban yarda da barrister ba Umma, his wife is my greatest fear Umma lkcn a clinic da Sudais bai da lafiya I didn't tell you she called and warned me to stay away from her husband" Sake baki Umma tayi tace "Ehh lallai Khadijah da alamar rako mata kika yi, ita kishiyar xaki fara tsoro tun baki shiga gidan ba, ita kishiyar Khadijah?" Turo baki tayi tace "Umma ni ba tsoronta nake ba kawai dai tashin hankali ne bana so, I don't want anything that will make me sad" Umma tace "Toh ai ba gida daya xa ku xauna ba" Khadijah tayi shiru bata ce komai ba, cikin kwantar da hankali Umma tace "Kiyi ta addu'a daughter, Allah ya maki xabi mafi alkhairi" a hankali Khadijah tace "Ameen" Umma tace "And one more thing Khadijah in har ke a tunanin ki saboda kawai Barrister Aliyu ya taimake ki a rayuwa kike son aurensa to pay him back toh gaskiya you are making a mistake kuma kin cucesa kin cuce kan ki indai sabida haka kika amince da aurensa" Hawaye Khadijah ya dinga yi sosai duk jikinta yayi sanyi, cike da karfin hali tace "Umma ba haka bane" Umma tace "Are you sure Khadijah" tana gyada kai da kyar tace "Ehh" Umma tace "Toh am happy to here that, ke dai kiyi ta addu'a kawai, and make sure yanxu ki kirasa ki ce masa ga wanda kika fi so a akwatunan" Khadijah na share idonta tayi kasa da murya tace "Wanda kika ce ya fi koh?" Umma tace "Ehh" A hankali tace "To bari in kirasa yanxu nagode Ummata" Umma tace "Welcm dear, Shureim yayi bacci koh?" Kai ta gyada tace "Ehh yayi but kamar yana son yin mura fa Umma, his voice is even cracky" Umma tace "Wannan kuma ke kika sani, least I forget nasan halin ki Khadijah tsakanin ki da matar khaleel mutunci kada kiyi amfani da cewa kina son mijinta ki dinga daure mata nasan ba hankali ya ishe ki ba" turo baki Khadijah tayi tace "Umma ni da ma mun kusa hutu in taho gida abuna ina ruwana da su" Umma tace "Khaleel dai ba abun walakanci bane a gun ki, though baku dade da sanin juna ba but he is always there for you, kuma duk da yasan ke wacece ya nuna yana son ki yana yaran ki, am reminding of all this ne don naga kamar kina da saurin mance alkhairi, dubi fa mahaifiyar Aliyu ba don nayi da gaske da ke ba ita ma ba raga mata xaki yi ba" jikin Khadijah yayi sanyi sosai, Umma tace "Sai da safe" daga haka ta katse wayarta, Khadijah tayi lamo kan gado, can ta bude idonta a hankali ta shiga kiran barrister a sanyaye, bayan sun gaisa a hankali tace "Barrister ka fara bacci ne?" yace "Noo ina wani aiki ne, how r you?" Tace "Lafiya lau, I now have a choice my barrister" Ya d'an buda ido yace "Really?" Tana murmushi tace "Sure" yace "Then which is ur choice?" Ta langwabar da kai tace "Ka hau Whatsapp in nuna maka yanxu" yace "Ohk then" daga haka ta katse wayar, bayan ta nuna masa akwatin da take so tayi masa text din sai da safe, daga haka ta kwanta nan da nan bacci ya dauketa. washegari da safe Khadijah na sa ma Shureim shoes dinsa na makaranta aka danna bell, ta kalli kofar kafin ta mike ta dau jakarsa ta goya masa a baya ta dau lunchbox dinsa tana rike da shi ta nufi kofar ta bude, khaleel ne tsaye bakin kofar, bai yarda ya kalleta ba yana kallon Shureim da murmushin sa mai kyau yace "How are you son?" Shureim yace "Good morning uncle" khaleel ya duka ya kamo hannunsa yace "The morning isn't good son, cold everywhere..." dariya Shureim yayi da ya bayyana white set of teeth dinsa, Khaleel yyi murmushi yana kallon kyakkyawan yaron ya fito da shi ya mike, gyara rigar sanyi sa yyi still bai yarda ya kalli Khadijah da ta hade rai ba yace "Plss do u use salt?" Khadijah na kallonsa tace "Meye shi?" Sai a sannan ya kalleta yace "Gishiri" sauke idonsa yyi daga kallonta, ta tabe baki kamar baxa ta ce komai ba sai kuma can tace "I don't know, let me check" daga haka ta juya a hankali ta koma ciki, Shureim yace "Uncle Aunt din nan tana nan" khaleel ya shafa kansa yana kallonsa yace "Tana nan" Shureim yace "Ae yau tace xata bani puzzle irin na su fadil..." khaleel yace "Tana bacci yanxu, ka bari sai ka dawo school xata ba ka" Shureim yace "Ohk can I tell her good morning now so as she will remember my puzzle?" khaleel ya duka yana kallonsa a hankali yace "No she is sleeping son, idan ta tashi I will remind her for you" Shureim yace "Ohk tnx" Khadijah ta dawo rike da container din Gishiri ta mika masa, ya karba yace "Thanks I will bring back the remaining now" Kamar jira take tace "Noo na ba ku" kallonta yayi da sauri yace "Noo ni xan yi amfani da shi ai" Wani kallo Khadijah tayi masa tace "Did you hear me mention name?" Khaleel ya sauke idonsa daga kallonta, a hankali ya juya xai koma ciki sai kuma ya juyo da sauri yace "I am coming inyi dropping dinsa a schl" Khadijah tace "Xan kai sa yanxu, you don't worry" yana kallonta da kyau yace "I insist Khadijah" daga haka ya juya ya wuce ciki, Khadijah tafi minti biyar tsaye a wajen can ta juya ta koma parlor ta xauna shureim ya biyo bayanta, tashi tayi daga parlorn gaba daya mood dinta ya canxa ta kalli Shureim tace "Ka jira sa a nan" daga haka ta wuce bedroom ta kwanta, ta rasa dalilin da yasa ta ji tana son yin kuka, ta kife kanta da pillow trying hard not to cry, ta fi minti goma a haka aka bude kofar dakin, Shureim ya shigo yace "Anty uncle yace in kira ki" A hankali ta mike xaune ta runtse ido jin xuciyarta na mata xafi, ta kalli agogo taga takwas saura, da kyar ta tashi ta bi bayan Shureim, tsaye ta tadda khaleel parlorn har ta karaso cikin parlorn bai yarda ya kalli inda take ba, ta tsaya tana kallonsa, kama hannun Shureim yayi yace "Plss Khadijah I need hot water, or rather lipton kafin in dawo" daga haka ya fita tare da Shureim dake daga mata hannu ya rufe kofar, juyawa tayi ta koma daki tayi kwanciyar ta. Bayan kusan minti ashirin aka danna bell, kin tashi tayi daga kwancen da take, Jin an sake dannawa ta daure ta dake, cike da karfin hali ta tashi ta fita, bude kofar tayi tana kallonsa, ledan hannunsa ya mika mata yace "Drugs din Shureim naga he is having cold" karba tayi ba tare da ta kallesa ba tace "Thanks" daga haka ta juya xata wuce yace "Khadijah ruwan lipton din fa?" K'in juyowa tayi tace "Ni bani da ruwan Lipton" daga haka ta rufe kofar ta, daki ta wuce ta fada kan hado tayi kukanta mai isarta Kamar warce aka aiko ma da sakon mutuwa, ita kanta bata san me yasa take kukan ba, ta fi minti talatin kwance, ta mike a hankali jiki ba kwari daga karshe ta fito parlor, kitchen ta shiga ta kunna gas ta daura ruwa ta xuba Lipton da kayan kamshi ta dawo parlor ta xauna, tana ta xaune parlorn har taji alamar ruwan ya tafasa ta mike a hankali ta shiga kitchen din, cikin flask ta juye ruwan Lipton din gaba daya ta sa hijab ta fita, danna bell dinsa tayi, tana ta tsaye bayan wani lkci ya bude kofar, Mika masa flask din tayi ba tare da ta kallesa ba tace "Yanxu na dafa" Ya karba a hankali yace "Thanks Khadijah" Bata ce komai ba ta juya ta koma apartment dinta, sai kusan sha biyu ta fita gidan duk da karfe goma take da lectures, da wuri ta fito schl don daukar Shureim ta samu har khaleel ya xo ya dauke sa, har ta fito wanka tayi sllh tana ta jiran ganin shigowar Shureim amma bai shigo ba, throughout ranan babu wani abin kirki da ta ci kuma gaba daya taji bata jin yunwa, a hankali ta dau wayarta don kiran Barrister taji ko ya isa gida lafiya, har ya katse bai dauka ba ta sake kiransa, nan ko yana xaune parlorn sa Little Meerah na jikinsa tana ta masa surutu da pure English dinta, Jiddah kuma na durkushe gabansa tana xuba masa dafadukan taliya da ta dafa sanin ranan xai dawo, kallon taliyar kawai yake don he is not a fan of it kuma sarai tasan