← Book details Noor Al Hayat Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 149 OF 168

Sashe 149

Noor Al Hayat Complete Hausa Novel · about 5 min read

Sannu...." Baby na masu wani kallo ta nuna Khadijah tace "You are mistaken, ga amaryar can xaune" daga haka ta dauke kai ta ci gaba da shafa powder dinta don ko kadan ji tayi gaba daya jiddah da kawayen nata basu mata ba, Khadijah dai sai kallonsu take ko kiftawa babu, Jiddah ta iso kusa da ita tace "Ke ce Khadijah, Amira, Kuma Ummu Shureim koh?" Khadijah taji gabanta yayi mugun faduwa bata dai ce komai ba tana ta kallonta, Jiddah tayi wani dariya tana kallonta da kyau tace "Ke ce ke Shirin shigowa gidan Barrister a matsayin matarsa ta biyu Koh?" Khadijah ta hadiya abu da kyar still ta kasa ce mata komai, xuwa lkcn kam ta fara dago wacece ke tsaye gabanta ko tantama babu matar Barrister ce, Baby ta mike tace "Ke malama ance maki gidan radio ne nan wannan tambayoyin da kike jefo mata?" Jiddah ta mata wani matsiyacin kallo ta daga mata hannu tace "Dakata Hajiya ban yi da ke ba, ki xama yar kallo a nan, ja gefe ki tsaya kawai" daga haka ta mayar da dubanta kan Khadijah tana mata mugun kallo tace "Wato tsaurin idon ki yakai har ki rasa wanda xaki makale ma wa ya aure ki sai mijina Barrister Aliyu Sudais?" Tuni hawaye ya kawo idon Khadijah duk jikinta yayi sanyi, Jiddah ta fashe da dariya ta juya tana kallon kawayenta tana nuna Khadijah tace "Don Allah wacece xaune nan?" Kamar hadin baki suka ce "karuwa" Jiddah tace "Da ta yi me?" A tare suka kara cewa "Cikin shege...." Tuni duk mutanen dake parlor suka yo daki da sauri jin hayaniya a daki, Jiddah na kallon Khadijah da kyau tace "Toh don kaza kazan ki in har kin haifi cikin uwar ki da ubanki ki yi kuskuren shigowa gidan Aliyu yau, ke don fitsara ki gama yawan karuwancin a gidan aiki ki haifi tagwaye sannan daga mijina ya taimake ki sai ki makale masa, daga taimako???? Har yana ikirarin tausayin ki da yake kadai yasa xai aure ki ba wani abu ba, kin xata badan uban tausayin da Allah ya xuba masa ba xai ce xai aure ki bayan yasan ke wacece? Toh bari ki ji, babu komai naki da ban sani ba, duk sirrin ki na tafin hannuna, babu abinda Aliyu ya boye min game da ke, tunda mijina ne shi din baya komai sai yayi shawara da ni, da farko na xata abun arxiki ne bayan ya bani labarin ki na amince ya aure ki don ya rufa ma ke da shegun ki asiri amma kawai daga baya tun baki shigo gidan ba na fara ganin canji, wato kin fara shanye min miji sai yanda kika yi da shi daga na amince masa ya aure ki ya rufa maki asiri koh? To wllh kinyi kadan, yau xan ga ta yanda xa ayi auren nan da kaxa kaxan ki sai dai ki koma ki ci gaba da karuwancin...." Baby bata san lkcn da ta mike ta cakumota ba ta makure ta..... Kan kace me fada ya kauraye tsakanin jiddah, baby, da kawayen jiddah, frnds din baby su ma suka shiga, da kyar mutanen da suka yi mutuwar tsaye parlorn suka raba fadan, Khadijah ta hade kai da gwiwa jin numfashinta na sama, ko kwakkwaran motsi ta kasa daga gun da take xaune, Jiddah ba irin xagi, cin mutunci da gorin da bata mata ba kawayenta na taya ta, har Umma sai da suka xaga, Baby ma bakinta bai mutu ba, da kyar aka fidda su dakin ana Allah wadaran Jiddah, sai a sannan hawaye ya dinga xubo ma baby taji tausayin Khadijah sosai duk jikinta yayi sanyi, Umma kam xaunawa tayi ita ma hawayen na sakko mata ta kasa cewa komai, Mumy kanta tsaye tayi ta rasa abin cewa duk jikinta yayi sanyi, Wata kawar Umma ta durkusa ta dago kan Khadijah a hankali cike da tausayinta, hawaye ne ke xuba idonta kamar an bude pampo, Baby ta durkusa kusa da ita ita ma hawayen na xubo mata ta rasa abinda xata ce mata, Khadijah ta kamo hannunta cikin rawar murya tace "is it my fault that I was raped baby? Is it my fault that I am an orphan, is it my fault that I had kids out of wedlock? Dama maraici...." kasa ci gaba tayi ta fashe da kuka sosai tana girgixa kai a raunane tace "Alhamdulillah for my fate... irin tawa kaddarar kenan kuma na amsa hannu bibbiyu, Amma me yasa mutane baxa su yi considering dina ba, ni ban so ma kai na haka ba, Allah ne ya kaddara min, but ya xan yi baby, dole in gode masa, ban taba karuwanci ba amma sun ce min karuwa, ban san Sudais baxai iya rike min sirrina ba he betrayed...." Mikewa Baby tayi ta dau wayar Khadijah ta fice daga dakin, Ta kunna ta shiga neman layin Sudais, Bata yi wahalan ganin number ba don Barrister tayi masa save as, tana dialing ba a dau lkci ba ya dauka cike da damuwa yace "Why did you switch off ur phone Amira..." Baby ta katse sa a xuciyarta na tafarfasa tace "Malam dama ka san baka iya rike sirri ba ka nace sai ka auri Khadijah??? dama kai din mijin ta ce ne sai yanda mahaukaciyar jahilar matar ka tayi da kai?" Kasa cewa komai Sudais yyi da farko don gaba daya he was lost, can cike da karfin hali yace "Wacece wannan?" A mugun fusace tace "Ba Lallai ka ji wacece ba, wllh ka ci amanar Khadijah, ka xalunce ta, and am advicing you ka janye batun auren ta kaje jahilar matar ka ta ishe ka, Kuma sai Allah ya saka mata" tana kai wa nan ta fashe da kuka sosai taci gaba "Naga ba ita ta ta xabar ma kanta wannan kaddarar ba har xaka xaunar da warce xa su xauna a matsayin kishiyoyi ka tsara mata komai na rayuwarta daga farko har karshe ta xo har gidan biki ta mata tonan silili ta gaya mata son ranta, tayi mata cin mutunci da cin fuska, tayi mata gori" katse wayar Sudais yyi kansa na juya masa ya mike daga xaunen da yake ya fito parlor, ya kusa minti sha biyar tsaye sai ga jiddah da kawayenta sun shigo parlorn, ya taka har gabanta ya sauke mata tagwayen mari, yana kallonta da jajayen idanuwansa yace "Na sake ki saki daya jiddah"
Chapter 149 · 0% Book details