Sashe 43
Noor Al Hayat Complete Hausa Novel · about 4 min read
da ya bar motarsa. Karfe hudu saura driver ya ajiye su a gida, sai da su siyama dake ta kumburi cikin motar suka fita sannan khadijah ta fito rike da ledan uniforms dinta da takardu, Baby ma ta fito rike da sauran takardun khadijah, Duk sai da kyauta ta bi ta yi ma uniforms din tsirara daga ledansu tana washe baki tace "Yarinya ta xama yar boko, toh me suka koya maku yau a makarantar" Khadijah tayi dariya tana cire kayan jikinta tace "anty mai girki yanxu xan yi wanka ne, idan na fito xan koya maki" daga haka ta shiga bathroom da sauri, har daki kyauta ta kawo mata abinci bayan ta xuba ma su siyama nasu a dinning, khadijah dake ta kallon pepper soups kala kusan uku da ta xubo mata tace "anty mai girki, kinyi girki da yawa kenan yau?" Kyauta tace "Ke Alhaji da kanin Aliyu xa su dawo anjima, yanxu haka suna can cikin jirgi a sararin samaniya, ai girkin da nayi ya fi kala shidda yau tun safe nake kitchen, na kuma ji Hajiya nacewa kila baxawara ma ta dawo yau" Khadijah ta tallabi cin dinta tace "Waye Alhaji anty mai girki?" Kyauta ta hade rai tace "Babansu Aliyu mana" Khadijah ta xaro ido da mamaki tace "Dama yana da baba, ai na xata shine baban gidan" Kyauta tayi tsaki tace "Dadina dake shegen shirme, toh an ce maki shi ya haifi kansa, ubansa nace maki xai dawo anjima tare da kanin sa saleem" Khadijah ta turo baki tana d'and'ana naman ragon gabanta tace "Toh naji" Baby ce ta shigo dakin bayan Khadijah ta gama cin abinci kyauta ta fita da plates din, baby tace "Mumyna tace in kira ki" Mikewa Khadijah tayi ta bi bayanta suka wuce sama, tun bayan da Anty khadijah ta koreta sai ranan ta sake hawa saman gidan, baby ta bude kofar dakin mumy ta shiga, khadijah ta tsaya daga bakin kofa tana lekan dakin, Mumy da ta hangota tace "Shigo khadijah" khadijah ta shiga ta xauna kasa tace "Ina yini Anty" mumy tace "Lafiya lau, ya school din" Khadijah tayi murmushi tace "I like it Anty" Mumy tace "Sun baki uniform?" Khadijah ta gyada mata kai, Baby tace "Mumy same class fa muke da ita" Mumy tace "That's good, ina books din da suka baki" mikewa Khadijah tayi da sauri ta ce "Xan dauko" daga haka ta koma kasa ta dauko books din ta ajiye ma Mumy, Mumy na kallon book din ganin Iman a jiki tace "Iman? Is that ur name?" Khadijah tayi murmushi ta gyada mata kai a hankali, mumy tace "Maa sha Allah" wani sabon jaka da bakin cover shoe da socks uku mumy ta dauko ta mika ma khadijah tace "Gashi sai ki xuba books din ciki" khadijah ta wara ido tace "Anty nagode, thank you" Mumy tace "Welcm, tashi ki tafi" mikewa khadijah tayi cike da murna ta fita, baby dake kallon mumynta tace "Mumy ni yaushe xa ki siya min sabon jaka?" Mumy tace "Soon" har kitchen Khadijah ta kai ma kyauta abinda mumy ta bata, kyauta ta amshe tana washe hakora tace "Allahu Akbar barin baxawara gidan nan ya maki rana dije, Allah ya makaleta a duk inda take har Hajiya ta gama dake ta dawo kai na nima" Shigowar Aneesah kitchen din yasa Kyauta tayi shiru sum sum ta fita don kai kayan daki Khadijah na biye da ita a baya. Suna shiga dakin ko minti biyar ba ayi ba aka kwankwasa kofa kyauta ta tashi da sauri ta bude, Aliyu ne tsaye rike da wani jakar mai kyau ya mika ma kyauta yace "Gashi ki bata" kyauta ta risina ta karba tace "Toh ta gode, Allah saka da alkhairi" bai ce komai ba ya juya ya bar wajen, kyauta ta bude jakar jin da nauyi ta ga takalma har biyu da safa uku a ciki sai water bottle irin nasu baby, kyauta ta rike haba tace "Ni dai ce ba a so a gidan nan wllh" Khadijah dake jera books dinta a jakar da mumy ta bata ta taso da sauri tace "Anty mai girki menene" Kyauta ta dungura mata tace "Duk kin fi ni goshi wllh" Khadijah ta kyalkyale da dariya ta karbi jakar da a gabansa aka rubuta *Iman* ta wara ido tace "Waowww"